Wednesday, 24 May 2017

ZUCIYA....kowa da irin tasa 31

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

  *Gaisuwa gareku 'yan sauyi, 'yar gaya, sankach, nagudu, sharubutu, Aisha Idris, Sub, Zee Sa'id and many more, tunda yanzu kun daina neman Aisha sai Zuciya to ga sakon Zuciya nan tana muku fatan alkairi....lol*

{ *31*}

   Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu.

   A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bikin nan."

  Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba."

  Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata.
Little ta d'au waya ta kira Ashraf,  sai da ta kusa katsewa  sannan ya d'aga tace " Yaya."

  Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? "

   Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar Ashraf,  Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy."

   D'agowa Nafi tai ta kalli Little,  jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye."

  Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?"

  A zuciye yace " da wani karambanin ne ma yasa ku d'auko yarinya tana makaranta? Sai kuje ku sami wanda ya saku ku tambayeshi."

  Little zatai magana taji ya katse, jiki a sanyaye ta kalli Nafi wacce ke wasa da hannunta a zahirin gaskiya kalaman Ashraf sun mata zafi sai dai tasan koma meye ai laifin ta ne.

Ta kalli Little tace taimakamin dan Allah in kwanta."

   Little ta kalli kafarta tace " Nafi ko muje Chemist? "

  Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a tace "bafa wani serious bane. " a zahiri kuwa tanajin zafin gun sai dai bataso a cire handkerchief d'in Ashraf daga kafarta.

  Little ta mike sannan ta shiga taimaka mata ta kwanta, idanu ta rufe kamar mai bacci, hakan yasa Little ta fito daga d'akin.

   Tana fita Nafi ta fara zubar da hawayen dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa."

  Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso.

  Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa.

  Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba.

   Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta.

   A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi.

   A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse.

   Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai.

Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters.

  Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu.
  Nafi ta dage sosai......

   Shekararta d'aya kenan a makaranta,  duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa.

   A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi.

  Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta.

  Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai.

  A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata.

   Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?"

  Ferry tai d'an tsaki tace " Ai   Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci."

  Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna."

  Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai."

  Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni."

  Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?"

  Nafi ta juya kai tace " Secret."

  Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?"

  Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai."

  Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?"

  Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana."

  Suka sakeyin dariya.
Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?"
  Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan."

  Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi."

  Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri."

  Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata."

  Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry."

  Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba."

   Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki."

  Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana."

  Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza."

  Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun."

  Dariya sukai harda tafawa.

  Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi.

  Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little.

    Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?"

  Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota."

  Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na."

  Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little.

   Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen.

  Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai."

  Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina."

  Little ta harareta tace " ba wani nan kedai kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi."

  Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window.

Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa."

  Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita."

  Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini."

  Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?"

  Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba."

  Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai."

  Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci."

  Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru."

  Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba."
  "Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci."

  Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa."

    kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan."

Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side."

    Nace Uhmmmm zaki iya????.

   *THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment