Sunday, 21 May 2017

ZUCIYA.... Kowa da irin tasa 30

ZUCIYA
       ĸowa da ιrιn тaѕa

© na Ayυѕнer Mυнd
    ayushermohd.blogspot.com

Wattpad As_AyusherMohd

Gaisuwa gareku Aminan Arziki Mom Hamra,  Mom Farhan,  Agra,  Mom Farouk and Fresh LUSM

{ *30*}

   Gaba d'aya Nafi ta kasa d'auke ido daga kanshi,  har ya gama d'ebo ruwa ya wanke mata duk da rad'ad'in da takeji sai leb'e kawai da take ciza, sannan ya kalli inda ta yanke,  sosai gun ya shiga ciki da alama karfe ne ko kwalba ya mata wannan aikin,  hannu yasa a aljihunsa ya ciro handkerchief sannan ya d'aure mata gun dashi.

  Mik'ewa yai tsaye sannan ya kalleta yace " zaki iya tashi? "

  Kai ta d'aga mai idanunta subyi tsuru tsuru,  ta d'aga zata mike taji wani zugi a kafarta wanda sai da tayi 'yar kara saboda azaba,  baya tai kamar zata koma kan kujera da sauri yasa hannu ya taro ta,  idanunsu ne suka had'u da juna,  Ashraf ya kalleta sannan yace " bakya gani ne? "

  Kallansa tai batare da ta amsa ba,  ya girgiza kai sannan yace " taya zaki bari har kiji irin wannan ciwon? "

  Kasa tai da idanunta,  saukar da ita yai ta koma ta zauna kan kujerar da ta mike.
  Harararta yai yace " yanzu ya kike so muyi? "
  Tai kasa da kai sannan tace " kaje kai ai jeranka ake ni zan karaso da kaina."

Ta d'auka bazai tafi ba ganin ba yanda za'ai ta iya tafiya,  amma ga mamakin ta gani tai yayi gaba,  kallansa tai idanunta suka ciciko,  ta sukunyar da kanta cikin rashin jin dadi.

  Batai auni ba taji kawai an sungumeta, a tsorace ta bud'e idanunta cikin rud'ewa tace " Yaya saukeni dan Allah. "
Ya murtuke fuska yace " kina tunanin bazan iya ba? "

  Kai ta girgiza alamar a'a, sannan tace " tsoro nake kar wani ya ganmu a haka."

  Wani murmushin rainin hankali ya mata yace " ke dai kina tsoro kar Aneesa ta miki duka."

  Nafi tai kasa dakai sannan tace " Allah dagaske nake ka ajiyeni please."

  Bai kulata ba ya cigaba da tafiya,  sun kusa isa filin gun sai ga Little da Habib sun taho ta gun suna Neman Ashraf.

   Daga d'an nesa kad'an Little taga alamun kamar sune hakan yasa ta karaso gun da sauri.

  Kallan mamaki ta musu,  Habib ne ya karaso gun shima cikin mamaki yace " Ashraf meye hakan? "

  Batare da ya kalleshi ba yace " name fa? "

  Habib ya kalli Nafi wacce tai tsuru tsuru da ita yace " event d'in auranka fa akeyi? "

  Yace " ehen sai me?  Abun haramun nai ko me? "

  Habib ya kara kallansu, sai dai amsar Ashraf yasa ma ya kasa magana,  Little ta daure tace" yaya yanzu in mutane suka ganku a haka me kake tunani? "

  Zaiyi magana kenan sukaji ana zabga salati daga bayansu.

  Ashraf ya kallesu Umma ce da 'yan uwanta ga Aneesa a tsaye cikin tsananin mamaki.

  Ashraf wuce su Little yai ba tare da damuwa ba ya gifta su Umma sannan ya ajiye ta a kan kujera daga baya,  sannan ya kalli Umma yace" Umma me kuke anan?? "

   "Kan jakar uba,  abinda za ka tambayemu kenan? "
Ashraf ya kalli Aneesa wacce ta fara hawayen bakin ciki sannan yace" naga kamar abun yara ne ban d'auka manya ma zasu zo ba. "

   A zuciye Umma ta matso tace " me kake aikatawa anan kai da waccan munafukar yarinyar a ranar shagalin bikinka? "

  Ya kalli Nafi cikin salon rainin hankali yace " wacce?  Waccan yarinyar? "

  Umma ta kumbura kam,  yai murmushi sannan yace" karamin accident ne ya sameta shine na taimaka mata."

  Umma ta kalli Nafi cikin kuluwa sannan ta kalli Ashraf tace " accident? Shi accident d'in bai tashi ba sai a ranar bikinka?  Ko dai tsabar kinibibi da muafurci ne hakan? "
  Ashraf bai tanka ba ya kalli Aneesa  da take kuka,  matsowa yai kad'an sannan yace " muje ko mutane na jira. "

  Hawayenta ta share sannan cikin b'acin rai tace " Duk wayar danake ma baka d'auka ba dan kana tare da waccan ne ko me? "
  Kallanta yai cikin rashin kulawa yace " zakije ko kuwa in tafi?  Dan naga kamar lokaci na kawai ake b'atawa anan."

Wata 'yar uwar Umma ta kalli Nafi wacce tai kasa da kanta hawaye kawai takeyi,  tace " waccan munafukar ai d'azu muna jere itace ta shiga d'akinsa ba kunya ta dade aciki kafin ta fito,  kun tabbatar ba wani abu na masha'a tsakaninsu? "

   Umma ta kalli Ashraf sai dai gani tai kamar ma baisan me suke cewa ba waya kawai yake danna wa,  zatai magana taga kamar tafiya ma zaiyi.

  Da sauri Habib ya rike hannunsa yace " Ashraf ka jiraya mana. "

  Hannunsa ya fizge sannan yace " zamanta nake?  Ita har takai in mata magana taki tahowa? "

  Aneesa ta matso inda yake jiki a sanyaye tace " Yaya amma.... "

  Cikin fada yace " amma me?  Ba ki yadda dani ba ko me? "

  Kai ta girgiza sannan tace " ba haka nake nufi ba. "

  Ya kalli su Umma sannan yace " to me kike nufi?"

Tace " ba komai kawai dai dama. "

  Tsaki yai sannan yace " inzaki wuce muje to,  in kuma bazaki ba ni inada gun zuwa. "

  Nan ya fara tafiya,  Umma ta maka mata harara alamar kar taje, da sauri Aneesa ta d'auke idanta akan Umma tabi bayan Ashraf da sauri.

  Ran Umma ya b'aci sosai lalai ta kosa Aneesa ta auri yarannan insun samu kan dukiyarsa su salwantar dashi dan kuwa bazata iya jurar bakin cikin yaron nan ba.

  Kan Nafi suka dawo a zuciye,  gashi Habib ya tafi,  duk yanda Little ke ba umma hakuri amma inaa idanta ya rufe duka ta shiga yima Nafi ba ji ba gani, itakam Nafi hawaye kawai takeyi.

Gaba d'ayawannan ranar mutane dayawa da bakin ciki suka taso daga gun nan.

  Su Nafi suna sauka a mota, Little ta sakala hannunta ta kafa'adarta suka nufi ciki,sai dai me?

  Suna shiga sukaga cincirindon mutane a tsakiyar farfajiya banda masifa ba abinda akeyi,  Little ta kalli Nafi tace"ko me aka sake yi oho. "

  Ji sukai da karfi wata tace " dan kut...... Uban yarinyar ai karyata zakuyi ba barinta zakuyi ba. "

  Nafi kam ta rasa me yasa takejin gabanta na fad'uwa haka,   jisukai ance " wai yarinyar ma daga ina take?  Akan ke zaku yadda ta zauna a nan gidan? "
Little ce ta kalli Nafi yanzu kam sun gane inda maganar a dosa,  Little ta kalleta tace " mu wuce ciki. "

  Suna shiga ciki Little ta ajiye Nafi sannan ta fito tai gun Mumy.

  A zaune taga Mumy tayi tagumi ga 'yan uwanta suma sunata magana, Little ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Mumy wlh ciwo taji a dalilin neman yaya,  ganin bazata iya takawa ba yasa ya d'auketa. "

  Mumy tai ajiyar zuciya tace" Little ki fadama Nafi gobe ta shirya da safe a maidata makaranta saboda tsoron abinda mutane zasu mata dan nasan 'yan uwan maman Aneesa sarai bazasu tab'a barin maganar nan ba. "

  Little tai shiru jikinta yai sanyi sosai,  sai dai tana ganin hakan ne yafi sauki.



¤¤¤¤¤¤¤¤

  A kachako kuwa d'an litti ya zake sosai yana aikin kasuwancin sa na babur, yana kuma jin dadin yanda uban gidan sa yake sanshi,  fatanshi d'aya yai sauri ya kammala kud'insa ya taho kano neman Ashaf........


*THE INNOCENT TEAM*

1 comment:

  1. Allah shikara basira en nadubaki a watt pad banga bookz naki ba ko daya

    ReplyDelete