*JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣4⃣
Jalal ya d'ago ya kalli Abba yace " Shugaban kasa ne shi ko me?"
Abba ya kalleshi yace "Jalal Sanate ne yanzu wanda kuma ake ji dashi haka kuma mutane na sanshi, ina tsorace maka abinda zai biyo baya."
Wata muguwar dariya Jalal yai wacce sai da abin ya tsorata Abba, sannan ya tsagaita yace " mene? Sanate? Wasu mahaukatan ne suka zab'eshi? Kuma shi ko kunya mutumin dabai san darajar d'an Adam ba harya iya cigaba da siyasa?"
Abba yai ajiyar zuciya yace " nidai yanzu kabar komai kaga gobe za'a kawo Zainab."
Jalal ya kalli Abba shi harya manta da wani auren Zainab, ya juya kai batare dayace komai ba.
Ganin haka yasa hankalin Abba yad'an kwanta, mutane mak'ota ne suka fara zuwa halan yasa Jalal ya koma ciki, shiru yai yana tunani can ya d'auko wayarsa yafara duba senate na kasa, kan wani yazo *ABDULLAHI UMAR*
Ya kalli hoton mutumin dakyau gabansa ne ya fad'i ba shakka wannan shine mahaifin Seemah bawai kama sukai sosai ba sai dai in har ka kalleshi ka kalli Seemah zakasan akwai alak'a ta jini sannan ga tarihinsa daya karanta, ransa yakai k'oluluwar b'aci sanda yaga yanda ake ji dashi da kuma yanda mutane ke masifar sanshi wasu har so suke ya tsaya a matsayin shugaban kasa na zab'e ma gaba.
Haushi ya ishi Jalal ya cilar da wayarsa kan gado sannan ya mik'e cikin zafin rai kawai wayarsa ya d'auka ya fita.
Tasha ya nufa kawai ya shiga motar abuja, sam idanunsa sun rufe.
Dad da Abba da kuma kawo ne zaune a d'aki, Abba ya kalli kawu yace "Wani hukunci ka yanke?"
Dad yai saurin cewa " Kawu nidai dan Allah kadawo nan da zama me zakayi a suleja yanzu? Dama can ba garin mu bane."
Kawu yai shiru cam yace " naji amma dai kai Isma'il kaima ina fatan kadawo nan da zama kenan?"
Dad ya d'ago ya kalli Kawo sannam ya kalli Abba jikinsa yai sanyi, Abba yace " gaskiya kam ya kamata kaima ka dawo kazauna anan."
Dad a hankali ya furta "karatun Seemah fa? Ina tunanin yimusu baiko itada Ammar sai in koma can inyaso in ta gama karatun sai mu dawo gaba d'aya."
Abba yai shiru can kawu yace " naji bayananka sai dai nima na yanke nawa hukunci na."
Ya kallesu sannan yace " In akai bakwai d'in marigayiya nakeso wahsegari ai baikon Junaid da Ammar, in yaso sai ka d'auki matarka ku koma England har zuwa sanda zata gama karatu, da zarar ta dawo za'a had'a ayi auren."
Dad ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan can ya kalli Abba sannan ya kalli Kawu yace " Amma junaid yanada budurwa ne?"
Nan Abba ma ya kalli kawu da mamaki, Kawu yai murmushi yace " ba wani taro za'ai ba saboda rasuwar da akai mana kawai dai za'asa rana ne a kuma bada kud'in gaisuwa."
Abba ya kalli Kawu yace " amma kawu......"
Kawu yai murmushi yace "Mahaifiyarku babban burinta bai wuce tayi had'in aure a tsakanin 'ya'yan ku ba, tunda shi Ammar yanada Seemah shiyasa nake tunanin had'a auren Junaid da Zahra."
Kallan juna Dad da Abba sukai, Kawu yace " na amince da auran Ammar da Seemah sai dai kamar yanda mahaifiyarku tace dole ne kafin ranar auren asan mahaifinta."
Dad yai murmushi tare da cewa gaskiya ne naji dad'in had'in nan, Abba ma yai murmushi.
Jalal sai bayan magrib ya iso Abuja, wayar Umma ce ta shigo sai alokacin ma yai tunanin ashe bai fad'a musu ba, da sauri ya d'aga wayar yace " Umma?" Tace " Jalal kana inane? Tun d'azu ana nemanka."
Jalal ya kalli cikin garin Abuja yace " Umma kiyi hakuri d'an Allah wani uzuri ne ya tasomin ina Abuja yanzu."
Tace " Abuja kuma?gobe fa za'a kawo Amarya."
Jalal ya runtse ido jin an anbaci Amarya yace " kiyi hakuri Umma."
Tace " naji amma ka tabbatar gobe ka dawo da wuri banasan mutane su fara zargin wani abun."
Yace "insha Allah." Nan suka kasje wayar.
Yana sauka yai sallah sannan ya nemi d'an machine yace " kasan gidan Sanate Abdullahi?"
D'an machine d'in ya kalli Jalal daga sama har kasa sannan yai dariya yace " kasan me kake cewa kuwa?"
Jalal ya had'e rai yace " mahaukaci ne ni dabazan san me nake cewa ba ko me?"
D'an machine yace " A'a muje inkaika." Aransa yace ko mai aiki ne a gidan?
Sun isa wata had'ad'iyar unguwa manyan gidajen dake gun da kuma tsarinsu zai tabbatar maka da guri ne manyan mutane.
A kofar wani had'ad'an dank'araren gida yai parking, Unguwar shiru kamar ba mutane, d'an machine ya juya yatafi bayan ya cemai nan ne gidan.
Jalal yabi gidan da harara yace " Dama irinkune masu hana kasar mu cigaba, kun tara zunubai a kanku kuma kunzo d'an yaudarar mutane."
Kofar Gate d'in ya karasa tare da tunanin ta inda zai fara, wani security ne ya fito tare da kallansa yace " me kake anan?"
Jalal ya kalleshi yace " Gidan Sanate Abdullahi ne?"
Mutumin ya kara had'e rai yace " eh amma kai waye?"
Jalal ya d'an daure tare da sa hannu a aljihu yace " nemansa nakeyi."
Security d'in ya jara kallansa yace "baka da hankali ne? "
Jalal yace " what?"
Nunashi da bindiga yai irin doguwar nan yace " waye kai?"
Nan fa idanun Jalal sukai tsuru tsuru, husur security d'in ya hura nan da nan wasu securities d'in suka fito, ya kalli Jalal yace " a dubashi da kyau ban yarda da shiba."
Jalal haka suka ririk'eshi suka shiga lalubamai jiki kamar yai ihu d'an bakin ciki, suna gamawa suka sakeshi tare da cewa " nothing suspicious Sir."
Ya kalli Jalal yace " tashi ka kara mai karkuma insake ganinka anan."
Jalal ya dake zuciyarsa yace " ganina kuwa dolene d'an bazan tafi ba harsai naga mutumin gidan nan inkuwa kuka hanani to sai dai ku fita da gawata."
Mutumin ya kalli Jalal yai murmushi yace " I wish kayi karatun Soja da anyi jarumi."
Jalal ya juya kai, mutumin ya cigaba sai dai inhar baka tafi ba zakuwa a fita da gawarka.
Jalal ya kara dakewa tare da jingina da katangar gun, ran mutumin ya b'aci ya d'aga kasan bindiga zai bugama Jalal, sai sukaji karar horn, da sauri suka jeru aka bud'e gate, motoci uku ne suka shigo Jalal ya kalli motocin har sukai parking sannan wata yarinya ta fito daga motar sanye da riga da wando sun matseta, tana tafe tana jijiga kai alamar rawa, Jalal yaja karamin tsaki yace "Allah ya shirya."
Juyowa tai d'an taji alamun kamar ana kallanta caraf suka had'a ido da sauri Jalal ya d'auke idanunsa, d'an takaici aransa yace "yanzu wannan kanwar Seemah ce fa ko?"
Baisan tazo kusa dashi ba sai jiya tace " waye wannan?"
Securitin ya kalli Jalal yace " Sorry madam."
Yanda take magana ma ya tabbatar ma Jalal ba'a hayyacinta take ba, ta nuna Jalal tace " Kai."
Jalal ya kalleta tare da girgiza kai yarinya karama dabata wuce shekara 18 ba amma.......
Zata sake magana taji daga saman beni ance "Me kikeyi anan?"
Da sauri Jalal ya d'aga kai, baban mutum ne da dukda baikai su Abba ba amma kasan baba ne, Jalal ya kara cusa ido ya kalleshi tabas mutumin da yake nema ne.
Dabara ce ta fad'o mai,
Yarinyar zatai magana Jalal da karfi yace " Sannu Dad dama cewa tai inzo gunka akan maganar soyayyarmu."
Securities suka kalleshi da mamaki itama ta juyo duk da a bige take ta nuna shi sannan ta nuna kanta, murmushin rainin hankali ya mata yace " Ko Sweety?"
Kai ta d'aga sannan ta kalli Mahaifinta wanda ransa yai mugun b'aci yace ku shigo ciki.
Jalal yai wani murmushin rainin hankali sannam ya kalli Securities d'in yace " Sorry bansanar daku da wuri ba."
THE SEEMAH'S LOVE TEAM