����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣4⃣
A daren ranar Jalal da Habib idanunsu basuga bacci ba.
Washegari ya kama litinin, Habib zaune a d'akin da Hajiya take kallan Abba da Dad kawai yake yana tsananin mamakin yanda suka iya b'oye wannan sirrin batare da sun sanar ba, bayan ya gaidasu ya koma gun Hajiya ya zauna ya kalli Dad yace " Dad bari naje gida in dawo sai kuma kuje."
Abba yace to in kaje daga nan ka biya tagurin Mamie ka amso min sak'ona, Habib yace "to" sannan ya mik'e ya fita.
Agoggon Hannunsa ya duba karfe 7 na safe kenan, gida ya wuce yai wanka ya sa kaya sannan ya fito, gidan su Zaid ya wuce.
Bayan ya isa a bakin gate yaga Ammar, nan suka gaisa sannan Ammar ya tambayeshi jikin Hajiya, Habib yace " Da sauki, sai dai inasan magana da kai."
Ammar ya kalleshi da mamaki yace " akan me fa?"
Habib ya dafa kafad'ar sa yace " inaso ne kazo kuje gurin Mamie ina tunanin a wannan lokacin ita kad'ai ce zata warware mana abinda ke faruwa."
Ammar ya jinjina kai yace " ni kaina ban fahimci kalaman da Dad da Hajiya sukai jiya ba kuma da alama mu 2 ne kawai bamu san me suke nufi ba a d'akin."
Habib yai shiru can yace " Nagano maganar akan Seemah ne duk da bansan gaskiyar abinda ke faruwa ba."
Gaban Ammar ne ya fad'i ya kalli Habib yace " amma yaya........"
Habib ya katseshi yace karka damu mud'ai je ciki tukunna.
Nan suka shiga cikin gida, Zahra suka gani tana goge goge tana ganin Ammar ta mik'e tare da gaidasu, Habib yace " Zahra ina Mamie?"
Ta amsa da "tana d'aki."
Basu kara mata magana ba sukai hanyar d'akin mamie, sun isa suka kwankwasa, daga ciki Mamie tace su shigo, nan Habib ya murd'a kofar tare dayin sallama, Mamie ta amsa tare da mik'ewa ta rufe littafin Husnul Muslim d'in dake hannunta.
Ta kallesu tace " Habib kai ne?"
Habib ya shiga tare da zama a kasa kusa da inda take, Ammar ma ya zauna nan suka gaidata ta amsa fuska a sake tare da tambayar jikin Hajiya.
Sunyi shiru kafin can Habib yace " Mamie jiya da daddare sam idanuna sun kasa runtsawa tunani kala-kala sai daga karshe zuciyata tabani amsar tambayoyina."
Yai shiru bayan yazo daidai nan a kalamansa, Mamie ta kalleshi tace " ina jinka Habibu, mecece amsar?"
Habib yai ajiyar zuciya ya d'ago ya kalli Mami.
Daga d'aki kuwa Seemah ce ta fito daga toilet, tai saurin sa kaya ta fito a falo taga Zahra tace" Zahra ina ya Ammar? "
Zahra tace " yanzu sukai d'akin Mamie shida Ya Habib."
Murmushin farin ciki tayi tai hanyar d'akin da sauri fuskarta d'auke da murmushi tazo daidai zata kwankwasa kofar taji muryar Habib yace " Mamie da farko dai na gano abubuwa guda 2, na farko Seemah ba 'yar Dad bace, sannan abu na biyu babu alak'ar jini tsakanin Mu da Seemah wannan dalilin ne yasa Dad yake san had'ata aure da Ammar."
Tunda Habib yafara magana Ammar yake kallansa idanunsa cike da tsananin mamaki, kallan Habib yai yace " Ya Habib meye hakan kake fad'a? Kasan me bakinka ke furtawa kuwa?"
Habib ya d'ago ya kalli Ammar sannan ya maida dubansa ga Mamie data runtse ido ta sani tun jiya a asibiti dole ne zargin kalaman da Dad da Hajiya sukai ya bayyana.
Habib ya kalli Ammar yace " Mamie dan Allah ki sanar damu abinda ke faruwa, wannan ne kad'ai hanyar dazai sa mu taimaki kanwarmu sannan shirin auren da Dad yake sai munsan dalili tukunna abin zaiyiwu d'an ni tun sanda Dad yace Ammar ba d'ansa bane sam zuciyata bata aminta ba."
Seemah kam ta kame a tsaye silalewa tai ta zube akasa kamar abinda ba ya motsi haka ta koma.
Mamie tai ajiyar zuciya ta kalli Habib tace "Habibu?"
Habib ya kalleta yace " Mamie d'an Allah karku k'ara kokarin b'oye mana wani abu, d'an gaba d'aya na kasa fahimtar inda kuka dosa."
Mamie tai shiru can tace " Ni kaina banasan wannan b'oye-boyen, sai dai ina tsoron yanda zaku d'au al'amarin."
Ammar kam shi kansa ya kasa magana, kawai jinsu yake, Habib yace " Mamie babu wani yanda zamu d'auki al'amarin gaskiya kawai muke san ji."
Mamie ta runtse ido sannan tai gyaran murya.......
♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢
Jalal kam har ya isa office ya zauna sai dai sam hankalinsa ya kasa nutauwa akan aikinsa mik'ewa yai da hanzari ya fito daga office d'in, asibitin da aka kwantar da Hajiya, inda suka had'u da Ammar ya tsaya jiya nan Jalal ya tsaya yana tunanin a ina zaiga Dad, cikin ikon Allah sai ga Dad da Abba sun fito daga wani d'aki da likita a kusa da su.
Da hanzari Jalal ya karasa gun, likita na tafiya Jalal yace " Dad ina kwana?"
Juyowa Dad da Abba sukai suka kalli Jalal, da mamaki Dad yace " Jalal kai kuma lafiya?"
Jalal ya karasa kusa dasu tare da kara gaidasu, Dad da Abba suka amsa Dad ya kara cewa " Jalal lafiya?"
Jalal ya d'ago ya kalli Dad yace " Dad kayi hakuri, sai dai hankalina ya kasa kwanciya, so nake naji mai mahaifina ya maka ka shak'e mai wuya? Naso in bar abin sai dai sam hankalina ya kasa kwanciya menene dalilin da zaisa kama mahaifina haka? Saboda inasan 'yarka ne ko me?"
Dad ya kalleshi da mamakin Kallamansa yace " Banace kaje ka tambayi mahaifinka ba?"
Jalal yace " haka ne haka kacemin sai dai a tunanina kai da ka mai hakan kai ya kamata in tambaya d'an zai iya yiwuwa shi baisan me ya maka ba."
Ran Abba ya fara b'aci yanzu ya gano wannan shine d'an gidan Amadun cikin b'acin rai yace " kai bakaji kunyar zuwa ka tsaremu ka fara mana tambayar banza ba? Ko rashin kunya ce?"
Jalal ya kalli Abba yad'anyi murmushi kad'an yace " ta ya za'ayi tambaya ta zama rashin kunya? Kamar yanda Mahaifina yake a guna haka Dad yake a gun Seemah, taya zan mai tambayar banza?"
Yai ajiyar zuciya sannan yace " sai dai duk inda d'a na gari yake dolene yaji haushi in har aka cima mahaifinsa mutunci ko da kuwa mahaifin nasa d'an fashi ne."
Dad ya kalleshi sam baya jin tsanar yaran zaiyi magana Abba yace " ka koma gun mahaifinka ga sako zan baka, kace masa yaci darajar Isma'il ne yaje gunsa ba ni bane da nine da wlh sai ya kwana a prison, ka kuma fad'ama mahaifinka sharrin dayama Kanina in ma laifin nasa ne ya rufe ko kuma akwai wani abu daya sashi yimai sharri, ko kuma so yake yaga kanina ya tozarta, to ka koma kasanar dashi matsayin Isma'il a wannan lokacin ka kuma sanar dashi a company d'in d'ansa kake aiki."
Abba na kainan ya ja hannun Dad suka shiga d'akin suka rufo sukabar Jalal a daskare a tsaye, sai da yai ta maimaita kalaman da Abba ya fad'a a ransa kafin cikin tsananin b'acin rai ya juya ya fita.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
Enter your comment...tnx ayusha kina kokari buk enki yayi dadi amma na matsu naji tushen labarin
ReplyDeleteMun yi biyu kenan, za muyi strike fah...
ReplyDeleteRangyan rangyan gyan
A ba mu littafi fah...
Rangyan rangyan gyan