����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_For you Maman Shaheed, I sincerely dedicated this page to you��thanks alot, Allah ya raya mana su Shaheed amin_
No. 4⃣5⃣
Mamie ta ja numfashi tace " Habib bazan iya baku labarin abinda ya faru ba saboda ni kaina ban san kanun labaren gaba d'aya ba sai dai zan iya sanar daku abu guda biyu zuwa uku.
Da farko dai kamar yanda ka fad'a tabbas Isma'il ba shine mahaifin Seemah ba.
Sannan Mahaifiyarta wato Fatima fyad'e aka mata sai dai mu kanmu bamusan waye ba sai dai bayan an mata fyad'en mai shagon da akai fyad'en yace Dad ne ya mata.
Wannan kalma d'aya daya furta yasa komai ya ruguje saboda alokacin saura kwana 2 a mata aure, alokacin wanda zai aureta ya fasa, Isma'il kuma 'yan gari suka tsaneshi har wuta aka sa a gidan Hajiya da kuma shagon da akai abin."
Habib yace " mene?"
Ammar kam hawaye ne kawai ke zuba daga idanunsa, me yake ji haka?
Mamie ta kallesu tace " abinda na sani kenan, bayan abin nan ya faru Fatima ta fiskanci wulakanci ta kowani b'angare har cikinta ya kawo haihuwa tana haihuwa tace ga garinku nan."
Habib ya mik'e tare da rik'e kansa, da sauri yai hanyar kofa ya bud'e yana bud'ewa yaji mutum ya biyo kofar, da sauri ya kalli kofar Seemah ya gani ta fad'i rim, jin karar fad'uwa yasa Ammar da mamie suka juya suma.
Habib da sauri ya tsugunna, Ammar ya taso da gudu yazo kusa da ita ya shiga jijigata yana k'iran sunanta sai dai inaaa Seemah kam ta suma.
Ammar ya kalli Habib idanunsa na hawaye yace " yaya kodai taji komai?" Kallan kallo sukai da Mamie, Mamie ta d'aure tace " akaita d'akin su Zahra."
Nan Ammar ya d'agata cak yai d'akinsu Zahra da ita, ya kwantar da ita, Ammar ya tsugunna a kusa da ita a rik'o hannunta idanunsa na zubar da kwalla, fita Habib yai daga d'akin d'an duk da yanajin tausayin Seemah a ransa amma yanajin haushin abinda akama mahaifinsa akan ta ta mahaifiyar.
Seemah kam ruwa Ammar ya shafa mata a fuska, hakan yasa ta bud'e idanunta tare da jan wani dogon numfashi, Ammar ya kalleta yace " Seemah!" a cikin wani irin yanayi mai ban tausayi ta kurawa Ammar ido, alokacin abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata.
Da sauri ta fizge hannunta tana girgiza kai cikin kuka mai ban tausayi kawai Dad take k'ira, Ammar ganin haka yasa tausayinta yak'ara kamashi ya mik'e tare da fita falo, Dad ya k'ira.
Daga can b'angaren Dad ya d'aga tare da cewa " Ammar ya akai?"
Ammar yace " Dad kazo da matsala fa."
" Matsalar me fa?"
"Dad kazo gidan Abba d'an Seemah na wani hali."
Cikin rud'ewa Dad yace " meya sami Seemar? Waya b'ata mata rai?"
Shiru Ammar yai kafin can yace " Dad bansan me zance ba."
Jin karar alamar sa makulli yasa ya juya da sauri ya kalli d'akin, da sauri yace " Dad kazo yanzu da matsala."
Yana kainan ya kashe wayar tare da saurin karasawa kofar d'akin ya shiga jijigawa, jiyai ansa sakata.
Hannu bibiyu yasa ya shiga bubuga kofar yana k'iran sunan Seemah.
Mamie, Zahra da Zaid da sauri suka zo jin ana bubuga kofa, nan suma suka shiga k'iranta.
Ganin ba alamar bud'ewa yasa suka tsaya jugum jugum Mamie tace " gashi babu wani makullin."
Ammar kam haryanzu bai gaji da bubuga kofar ba, yana k'iran sunanta cikin wani irin murya.
Sun dade agun kafin Dad ya iso da sauri yana zuwa ya kallesu yace " menene?" Shiru sukai Mamie tace "nice na fad'i abinda bai kamata ba kuma ina tunanin ta ji."
Gaban Dad ne ya fad'i ya sa hannu zai buga kenan yaji muryar Habib yace " Zaid d'an Allah kaida Zahra kud'an bamu guri."
Zaid ya kalli Habib cikin b'acin rai gani yake kamar rainin hankali ne hakan, a zuciye yai waje.
Habib ya maida dubansa kan Dad yace " Dad da alama Seemah tasan komai a kanta, menene dalilin dayasa zaku b'oye wannan babban sirri ga kowa? Sannan taya za'ayi a maka sharri saboda mahaifiyarta amma ka rik'e yarinyar da ba kaine mahaifinta ba."
Dad ya kalli Habib cikin takaicin kalamansa, kafin yai magana yaji Ammar yace " lalai ya Habib, wato kai abinda ya dameka kenan? Yarinya tana cikin d'aki Allah ne kad'ai yasan meke faruwa da ita a ciki anma kai abinda kake tunani kenan?"
Dad ya kalli Ammar kallon jin dad'i ga kalamansa, Dad yai baya sannan ya taho da gudu ya big'e kofar, sai dai bata bud'e ba, haka sukai tayi shida Ammar har sukai sa'a kofar ta bud'e, da sauri suka shiga ciki sai dai ba kowa a d'akin, ga mamakinsu kuma karar zubar ruwa sukeji daga b'an d'aki.
Ammar ya karasa da sauri tare da bubuga kofar toilet d'in.
Seemah kam tana cikin bathroom ta tsugunna a cikin ta saki shaya, ga bata cire kayan jikinta ba, ga ruwan sanyi ta sakar ma kanta, hakan yasa ruwa duk ya jikata jakaf, sai dai ko damuwa batai da jikinta ba kawai kuka takeyi, gani take wannan itace hanyar da ya dace da ita, ita kad'aice hanyar dazatasa takasa gane yawan hawayen datake zubarwa.
Kuka sosai takeyi sai dai ruwan dake zuba jikinta yasa baza'a gane ba.
Dad ya matsa jikin kofar ya shiga k'iran sunanta, tana jin muryarsa ta mik'e jikinta na rawar sanyi, sai dai bata bud'e ba, Dad ya shiga lalashinta, can cikin lallashi yace " fito Seemah inhar kika fito zan fad'a miki duk abinda ya faru a baya, na miki wannan alk'awarin."
Jin wannan kalaman yasa ta bud'e kofar a hankali, kofar tana bud'uwa Dad da Ammar sukai saurin shiga ciki, kallanta Ammar yai hawaye na zubo mai, kanta ya kalla sannan ya kalli yanda jikinta ke d'iga da ruwa, dukansu har Habib sai da sukaji tausayinta ya kamasu sosai.
A hankali sukaji tace " Dad kafad'amin abinda naji ba gaskiya bane, ka fad'amin kaine mahaifina, ka fad'amin gaskiya d'an Allah."
Dad ya share hawayensa ya matso ya rungumeta yana hawaye sosai, yace " Seemah ki kwantar da hankalinki."
Kai ta girgiza tace " Na fahimta dagaske ba kaine mahaifina ba kenan, mahaifiyata karuwa ce, tsintata akai?"
Kallanta Habib yai cikin tausayi da alama bataji komai ba kenan, Dad ya d'ago tare da share nata hawaye yace ki canza kaya Seemah zan fad'amiki komai, amma ko kusa Fatima ba karuwa bace, ba kuma tsintarki nai ba."
Kallansa tai ta kasa yin komai, sai hawaye da suke tsere a idanunta, Mamie ta kwallama Zahra ido, tana zuwa tace " taimaka mata ta canza kaya."
Dad ya kalleta yace " ki shirya ki fito fallo zan sanar dake komai."
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
��♀
Tnx Allah ya kara basira.
ReplyDeletecyberghost vpn crack
ReplyDeleteSoftware
Download