Thursday, 5 January 2017

JALALUDEEN 35

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 3⃣5⃣


  Habib yana isa gidan da sauri ya bud'e mota ya fita ko kofar bai rufe ba, yai cikin gidan da sauri, bayan ya shiga da Sallama suka amsa mai yasamu guri ya zauna, Ammar na kasa kusa da Dad yana daddana waya, Habib shima ya karasa bangaren dake kallan Ammar ya zauna.

  Ammar ya kalleshi tare da cewa "Yaya ka iso?" Habib ya d'aga nasa kai alamar eh yamaida kallansa kan Dad dayai shiru, a zuciyarsa kam addu'arsa d'aya ce Allah ya taimakeshi akan abinda yake shirinyi.

  Habib ganin Dad yayi shiru yasa yace " Dad kayi shiru?"

Ya sauke idanunsa akan Habib sannan yamaida kallansa kan Ammar yai gyaran murya tare da cewa " inaso ku bani aran hankalinku nan."

  Gaba d'ayansu suka maida kallansu kanshi, Dad ya had'iyi wani abu sannan yace " abinda nake shirin sanar daku shine......."

Duk sun zak'u gashi maganar Dad ta katse bai karasa ba, jin shirun dayai yasa Ammar yace " Dad yaka tsaya?"
  Dad yai shiru sannan ya sauko tsakiyansu ya zauna tare da dafa Ammar idanunsa taf da kwalla yace " Ammar kasani inasanka ko?" Murmushi Ammar yai yace " haba Dad harsai ka fad'i haka?"

  Dad ya kakaro murmushi sannan ya mik'e tare da takawa gaba dasu kad'an ya hard'e hannayensa ta baya, ya juya musu baya ya cigaba " lokaci yayi daya kamata in sanar daku wani sirri da baku tab'a sani ba, Ammar banaso ka sa wani mugun abu a ranka dalilin dayasa na yanke shawarar sanar daku shine Ammar nakeso ya auri Seemah."

  Ba Ammar ba hatta Habib mik'ewa yai a zabure, Dad kam idanu ya runtse, Ammar da Habib a tare suka had'a baki suka ce *What?* Ammar ya cigaba da magana " ban fahimci me kake nufi ba Dad, ni in auri kanwata? Me kakesan fad'ane Dad?"

  Habib ya amshe maganar da cewa " Dad me kake nufi da kalamanka? Wani irin zance kakeyi haka? Kana nufin akwai aure a tsakanin Ammar da Seemah ko me?"

  Dad ya d'aure tare da share hawayen da suka kwaranyo ta gefen idanunsa, ya juyo tare da cewa " haka ne Habib akwai aure a tsakaninsu domin kuwa Ammar ba d'ana bane."

  A tare suka kara cewa *what?* gaban Ammar ya fad'i zubewa yai kasa tare da kallan Dad cikin wani irin rud'ani, Habib ma ya kalli Ammar sannan ya kalli Dad yace " ban fahimceka ba Dad kanasan kacemin Ammar kanina ba kaine mahaifinsa ba?"

  Dad ya d'aga kai tare da cewa " nasanar dakune saboda inasan had'shi aure da Seemah shiyasa na aika yazo kasar nan."

Girgiza kai Ammar ya shigayi da sauri ya mik'e yai waje da gudu, Dad ya runtae ido shikad'ai yasan meyakeji, Habib ya matso kusa da Dad, ga mamakin Dad gani yai Habib ya saki murmushi yace " Dad do u expect me to believe that? Mene? Ammar ba d'anka bane? Banda tsananin kama da kukeyi? Da muma mukeyi dashi? Me kakesan cewa dad?"

  Dad yai saurin juya baya tare da cewa " kanina da nake tsananin kama dashi shine mahaifin Ammar yana haifarsa sunyi tafiya sukai hatsari shida matarsa wannan dalilin ne yasa na anso Ammar tare da alkawarin kula dashi kamar d'ana."

  Habib yai shiru tare da jinjina kai yace " ayya meyasa baka tab'a fad'amin ba Dad?" Ganin Habib ya yarda da kalamansa ne yasa Dad ya juyo yace ba wannan bane da muwar da ya kamata muyi yanzu, Seemah kana tunanin zata rabu da waccen banzan yaron? Habib yai shiru sai can yace " Dad Allah ne kawai ya sani, amma yarinyar nan sai anyi da gaske wajen rabasu, har kud'i na bashi d'azu akan ya bar aikin dayake a company d'ina ya bar garin nan amma yak'i, Dad yaron nan yanada taurin kai."

  Dad yai tsaki tare da cewa duk taurin kansa ai baifi karfin iyayensa ba, su kuma iyayen nasa nasan basufi karfin kud'i ba,ka bincikomin garinsu zanje har gidansu in basu kud'i su sa d'ansu yabar aiki a company d'inmu.

  Habib ya jinjina kai yace " wannan ma is a good idea."

Dad yace " naso in d'auketa mubar kasar amma kuma sai nai wani tunani, inaso kafin mu koma ai baikonsu da Ammar inyaso daga baya sai ai auren."

  Habib yai shiru bai amsa ba, shidai tana mamakin wannan al'amarin.

  Nan yai sallama akan gobe zai turo address d'in gidansu Jalal.


  Jalal kam da kyar ya lallab'a Jalal suka wuce gidansu, sunje shiga gate d'in gidan Yaga k'iran Abba, da sauri ya d'auka tare da saisaita murya ya gaida shi, Abba ya amsa tare da cewa " Ashe ka koma?"
Jalal yace " wlh k'ira na akai na gaggawa."
  Abba yace " ba wani abu dama na k'iraka ne na sanar dakai na yanke hukunci ranar Juma'a rana ita jiya kenan, za'a d'aura maka aure da Zainab, ka kuma tabbatar ka iso da sassafe."

  Cikim razana Jalal ya bud'e murfin mota ya fita tare da cewa " Abba ban fahimci me kake nufi ba, bangane Aure ba?"

  Abba ya had'e rai yace " na yanke hukunci kuma baka isa ka bijirema hukuncina ba kafi kowa sanin hali na, sannan bazan yarda da wani shirmenka ba."

  Jalal yace " Amma Abba......."

Cikin fad'a Abba ya katseshi da cewa karka kuskura Jalal kace zaka d'inga musu dani, kai ko kumya bakaji ba? Yarinyarnan tun tana karama take taimakon mahaifiyarka da kanwarka, kai kana tunanin dabadan Allah yasa tana nan ba wani abun ai mahaifiyarka bazata iya jura ba."

  Jalal zai kara magana Abba ya kara katseshi da cewa " ka kuma tabbatar ka zo ranar juma'a da wuri d'an intanine gobe ma za'a d'aura auran sa'a kaci mahaifiyarka ta nemi izini zuwa juma'a." ABBA nakainan ya katse layin.

  Bin wayar Jalal yai da kallo meke faruwa? Dasauri ya danna number Umma sai dai lokacin tana zaune kusa da Abba hakan yasa tak'i d'aukan wayar d'an umarnin Abba ne kar kowa ya d'auki k'iran Jalal.

  Ganin taki d'auka yasa ya k'ira Zainab tana zaune akan sallayar datai salla tana lazimi, ganin k'iran Jalal yasa tai murmushi sai dai data tuna me ya mata da kuma umarnin Abba yasa ta canza fuska ta koma kalar tausayi, sai dai inaaaaa bazata iya ganin wayar Jalal ta katse ba tana zaune, saura kiris ta katse ta d'aga tare da sallama, Jalal ya amsa tare da cewa " Zainab meke faruwa? Ban gane aure wani satin kai tsaye ba?"

  Zainab tai kasa da kai a hankali tace " Yaya bansan nima meya faruba gaskiya kawai tun sanda Abba ya fita d'in nan, inaji gidan mu yaje, d'an bai dawoba sai daf da magrib, bansan meya faruba kawai yacemin inyi hakuri lefe da wani sha'anin biki ayi daga baya in inaso amma wani satin za'a d'aura mana aure amma anan zan zana kafin ka samu gida."

  Jalal yaja dogon ajiyar zuciya tare da cewa " it can't happen." Yana fadar haka ya katse wayar tare da neman number Seemah, sai dai duk yanda yake k'ira layin a kashe yake matar take sanar dashi.

  Hannu yasa ya shafi kansa sannan ya furzar da wata isa tare da naushin jikin bango da hannunsa, yaji zafi kwarai sai dai baikai zafin da yakeji a zuciyarsa ba.

 

  Sagir ne ya matso ya dafashi, baice mai komai ba.


Seemah kam taci kuka harta gaji, Aisha sai dariya takeyi, d'an karma tai lallashi yasa taki shiga d'akin, gani take gwara a saita mara kunya da sakalci.

  Farida kam shigarta  uku tana bata hakuri amma inaaaaa seemah taki hakura sai kuka takeyi itadai a bata wayarta.





© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*


��‍♀

No comments:

Post a Comment