Monday, 2 January 2017

JALALUDEEN 32

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 3⃣2⃣

  Ammar ne ya fito daga toilet, a bakin kofar toilet d'in ta ganshi yana fitowa ta d'aneshi, tace "yaya godiya sosai, thanks to you munshirya da Deen."

  Ammar ya had'iye wani bakin cikin sai dai ya kakaro murmushi yace " are you that happy?" Kai ta d'aga sannan ta d'ago ta kalli Ammar tace " yaya inasan Deen sosai, kasan me?"

Kallanta yai zuciyarshi kamae ta fashe duk yanda yaso ya b'oye bakin cikin dake ransa ya kasa, Seemah tai murmushi tace " amma kasan wani secret yaya? Na kasa tantance wayafi matsayi tsakaninka da shi a guna."

  Ammar ya kalleta jiyai zuciyarsa bazata juri ganin ta ba, shi zata had'a da wani bare da ko wata da had'uwa basuyi ba? Juyawa yai ya fara tafiya batare da ya tankamata ba, da sauri tasha gabansa ta rangwad'ar da kai tace " Ohhhh my bro ba dai haushi kaji ba?" Idanunsa ya runtse   saboda bazai iya fad'a mata magana mara dad'i ba, gashi bai san ya mata magana, cewa yai" Seemah matsa mu wuce, Dad nake san gani."

Ya matsa kad'an daga kusa da ita, hannunsa ta kamo tace " wasa nake yaya." Juyowa yai ya kalleta tai murmushi tace " yaya inasan Deen sosai amma yama za'ai in had'ashi da kai? Ko kamanta ne? In na kwanta zazzab'i saboda shakuwarmu kaima sai ka kwanta?"

Tai murmushi sannan ta cigaba" tsokanarka kawai nakeyi, Deen soyayyar macen dake bala'in san saurayinta nake mai kai kuma soyayya ce ta jini yama za'ai ka had'a?"

  Murmushi ya saki sosai ta had'a yanayenta biyu ta tafamai tace " yauwa my dear bros yanzu kafimin kama da yayana."

  Ajiyar zuciya yai, yace " Seemah nima bansan meyasa naji haushin ba d'an kin had'ani da wani, na sani sarai soyayyar jini dake tsakaninmu."

  Ta furzo iska ta sa hannu a goshinta tace " oh God my bros sai yaushe zamu dauka ne?"

  Dariya yai, ta kalleshi tace " ji kafar yaya kamar wanda bata aiki?" Yace ni d'in? Gwalo tamai ta ruga da gudu, binta yai da gudu shima, suna gudu suna dariya.

     Jalal kam jin yanayin jikinsa ba daidai ga magrib takawo kai yasa ya wuce d'akinsu ya bud'e, abin haushi 'yan d'akin suna zaune sun kure radio, jiyai kansa na juyawa haushi yasa shi ya fita tare da zama a waje, sanyin dake ratsashi yasa ya tabbatar zazzab'i keneman rufeshi, waya ya d'aga abin haushi ya rasa wama zai k'ira? Sagir ne ya fad'omai hakan yasa yai dialing number,  ringing 2 Sagir ya d'aga tare da cewa " Jalal kaga Chairman d'in?"

  Yace " Eh amma sagir please kana ina?" Sagir yace ina gida ya akai zaka zo ne?

  Jalal yai shiru, Sagir yace " please kazo tun yaushe nake rokanka? Har cewa nai ka dawo gidanmu mu d'inga zama a d'akina ka k'i bansan meyasa kake haka ba.

  Jalal kam sai nishi yake jiyake kansa na wani irin sarawa, ka karar disco duk ta isheshi, a hankali ya firta Sagir please kazo ka d'auken a wajen d'akinmu kaina...........

  Jiyai kansa yayi kinkirikim, hakan yasa ya sauke hannunsa, Sagir ya saki kiran sunanshi, jin shiru yasa ya zari makulli da sauri ya fita.

  Da gudu ya zuro motarsa, yana zuwa yaga Jalal a waje ya jingina da jikin bishiya, da sauri ya karasa kusa dashi, yanasa hannu ajikinsa yaji kamar wuta, da sauri ya d'auke hannunsa yace " Jalal meke damunka haka? Ya za'ai kanajin zazzabi haka bazaka gun likita ba, Jalal ya d'ago ya d'an saki murmushi yace " Sagir ka iso? Nagode fa."

  Sagir ya kalleshi cikin tausayi, yace Jalal tashi muje asibiti, kai ya girgiza mai yace " muje chemist kawai, ina sha magani zai tafi."

  Sagir ya amince da shawararsa, nan ya nemi taimaka mai Jalal yai murmushi yace " me kad'auken Sagir? Zan iya tafiya da kaina, is not a big deal."

   Sunje chemist nurse d'in ya kalli Jalal yace " ya kamata kaje asibiti gaskiya, jikinka na burning dayawa."

  Jalal yace bani magani kawai, nan ya bashi magani yana mamakin taurin kai irin na Jalal, Sagir ya kallu nurse d'in yace " haka yake indai Jalal ne."

  Sun fito suka shiga mota Jalal sai kallan wayarsa yakeyi, da alama k'ira yake jira ko kuma yakesan yi.

  Sagir ya kalleshi yace " ka tabbatar ba matsala?"

  Jalal ya d'aga kai, Sagir yace " amma maganar me kukai da Chairman d'an da alama ba maganar aiki bane."

  Jalal yai d'an karamin tsaki yace " banasan ma tunawa amma Sagir wani irin mutum ne Chairman?"

  Sagir yai murmushi yace " mutum ne mai mutuncin gaske sai dai yanda na ga alama yana tsananin san family d'insa, yana girmama mahaifinsa sannan yanasan kanwar nan tasa."

  Jalal yad'an tab'e baki, Sagir yace "amma maganar me kukai?"

  Jalal ya maida kanshi jikin window baice komai ba.

 

  Dad yana zaune a wajen gidansa, motar Habib ta shigo, mamaki yasa ya kalli motar har Habib ya karaso ciki, yai parking,  Dad ya kalleshi kallo d'aya zakamai kasan akwai abubuwa dayawa a zuciyarsa.

  Yana karasowa ya gaida Dad, Dad ya amsa tare da cewa " na d'auka Ammar ne zaizo."

  Habib yace " anan zai kwana yace, nasan anjima zaizo suna tare da Seemah ne."

 
  Dad ya d'aga kai tare da murmushi yasani ai, da za'abar Ammar da a gidan Habib zai kwana.

  Habib ne ya katseshi da cewa " Dad ina da tambaya?"

Kallansa yai yace tame fa?
Habib yace " Ummi mahaifiyar mu, ita ta haifi Seemah?"

  Gaban Dad ne ya fad'i ya kalli Habib cikin tsananin mamaki, yawo ya had'iya sannan yai saurin kauda kai, yace " wani irin shirme kake fad'a? Bansha sanar daku sanda Maryam zata rasu ba tana haihuwar Seemah ta rasu? Ko so kake inyi ta tisa maganganu na?"

  Habib ya dawo ta gaban Dad ya kalleshi, yace " a'a Dad akwai wani abun bayan abinda muka sani, akwai abinda kake b'oyewa bayanan."

   Dad ya had'a rai kamar me, yace " karka kara tunanin ba mahaifiyarku d'aya da Seemah ba, inba sokake ranka ya b'aci ba."

  Yana kai nan yai saurin yin haryar ciki, sai dayai nisa ya juyo yace ka gaidata in ka koma, sannan kace mata nayi missing d'inta.

  Yana kai nan ya karasa ciki.
  Daga yanda Habib yake kallan Dad zakasan bai aminta da kalaman da Dad ya fad'a ba, dole dole akwai wani abun da ake b'oyewa kod'an yanda dad yake saurin katse maganar in an fara.









©  *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

No comments:

Post a Comment