Thursday, 26 January 2017

JALALUDEEN 52

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 5⃣2⃣

   A goggon dake d'aure a hannunsa ya kalla, sannan ya jawo wayarsa dake gefensa, number Seemah ya kurama ido, ya bude gun da nufin aika mata da sako, sai dai sam ya rasa mai ma zai ce mata, a goggon wayar ya kalla karfe 1 na dare, ya runtse ido da nufin yai bacci sai dai inaa, sam ya kasa sai ma wani irin ciwo dakan ke yi masa, zama yai, yaji zaman ba dad'i ya mik'e tsaye can kuma ya kwanta, tunawa yai ashefa daren jiya baccin awa d'aya da rabi ya samu.

  Shawara d'aya ya yanke, a yanda yakejin San Seemah a ransa yana tunanin zai iya sadaukar da farincikinsa ita ta samu, indai har auren shi kad'ai ne mafitar da zaisa Seemah ta san mahaifinta ta kuma yi farinciki da ganinsa, to ba shakka zai iyayin abinda ya fi wannan, sannan shi yasani bai isa ya take hukuncin mahaifinsa ba, sai dai a da yaso gwadawa ya rok'eshi akan ya hakura da auran sai dai bukatar Seemah yasa bazai iya tambayar hakan ba.

  Ya rik'e kansa dake rad'ad'i tare da rufe ido, ya dad'e yana tunani kala kala kafin Allah ya taimakeshi bacci yai gaba dashi.

    Washegari.........

  Ranar Alhamis kenan ya kama kwana d'aya da rasuwar Hajiya sannan a d'aya b'angaren kuma yau ne ake shagalin kamun Zainab, sai dai itama Zainab ba wani farin ciki take sosai ba ga kawayenta sai tsokanarta suke, wai basuga tana waya da angon ba bare ma har yazo ganinta, murmushi kawai takeyi a ranta tace " inafa zanganshi bayan ba nice a ransa ba?"

  Jalal kam da bacci ya d'aukeshi sai karfe 10 ya tashi, shi kansa yayi mamakin ganin karfe 10, da sauri ya mik'e Alhamdulila yaji ciwon kan ya tafi, ya fad'a toilet yai wanka sannan ya zura kaya ya fito, yayi mamki daya shiga cikin gida ya taddasu suna ta hidimar su ta biki, wasu kuma suna shirin wai tafiya gidansu Amarya, Jalal ya had'e rai sannan karasa ya gaidasu Goggo ta kalleshi tace " Ango anya ma kuwa kaje ganin Amarya?"
Ya d'ago ya kalleta yace " Goggo sai kace ban santa ba? Ganinta kuma name?"
  Goggo ta shiga tafa hannu tace "lalai wannan shine bagidajen, kai an fad'ama ko a kauye ana haka ne?tsaya ma anya kuna d'an tab'a wayar nan kaji matsalarta?"

  Jalal ya kalleta yace "Goggo kenan, wace matsala zata samu yarinyar dake gidan iyayenta?"
  Goggo ta shiga salati sannan tace " oh ni yau me nake ji haka? Ni ko d'akin da aka gyara muku ma banga kaje ka gani ba."

  Jalal ya kalleta zaiyi magana karar wayarshi ta katseshi, Manager d'insu ne hakan yasa ya mik'e tare da cema Goggo yana zuwa, yana fita ya d'aga wayar, Manager yacemai "Jakal ya? Ka tura takardar kuwa?"
Jalal yace " oh God wallahi na manta amma bari na musu sending yanzu."
Ran Manager ya b'aci yace " Jalal wai me ke damunka ne? Sam ka daina maida hankali akan aikin ka sannan yanzu kayi tafiya ba rubuto takarda nakasa fahimtar ka yanzu."
  Jalal yai kasa dakai baice komai ba, ganin haka yasa Manager ya katse wayar.
  Komawa yai kan dakalin kofar gidan ya zauna, Umma ta aiko yazo yaci abinci, ya kalli d'an aiken tare da cewa " banajin yunwa sai dai anjima."
  Daga bayama mik'ewa yai ya tafi can bayan gari ya zauna shi kad'ai.

    Rana bata karya, a yau ne ranar asabar uku ga mutuwar Hajiya haka kuma a wannan lokacin ne aka gama d'aurama Jalal aure a massalaci, kana ganinsa zakaga ya rame sosai, sannan sam ya canza Umma kam harta gaji da fad'an rashin cin abincinsa, ana gama d'aurin aure ya wuce gida ya shiga d'akinsa, abokai 'yan uwa da iyaye sai cigiyarsa sukeyi a d'au hoto sai dai an nemishi an rasa, shikam yana kwance cikinsa na mai wani irin ciwo, agoggonsa kawai yasa a gaba yana kallo.

  'Yan d'aurin aure sun watse, Abba ya taho gida shikanshi farincikinsa ragaggene d'an yana tsoron abinda zai faru a yau tsakaninsa da Jalal.
  Yana isa kofar gida kuwa yaga Jalal a tsaye, kallan mamaki yamai yace " Jalal meye hakan? Kasan dole ne a nemeka amma shine kayi tahowarka gida ko?"
  Yai kasa da kai yace " Yahkuri Abba banajin dad'i ne."
  Abba yamai kallan tausayi duk ya canza,  Jalal yace " Abba jiranka nakeyi, akan alk'awarin dakamin."

  Abba ya d'ago a tsorace yace "Jalal!!!."
Jalal yace " Abba d'an Allah na rok'eka daka cika alk'awarinka na fad'amin d'in dakace zakai."

  Abba yai shiru sannan yace " muje d'akinka."
  Nan suka juya suka shiga soro inda d'akin Jalal yake.

  A b'angaren Seemah kuwa tunda ta tashi da asuba, taketa maimaita wannan ranar a ranta, lungun gado ta samu ta rakub'e duk yanda Zahra tai da ita inaa abin yaci tura ga maza duk suna gun karb'ar gaisuwa, agoggon hannunta ta cire tare da rungumeshi a kirjinta, idanunta sun kad'a sunyi jaa.
Kalma d'aya ke yawo a ranta " *Deen an d'auramai aure da wata.*"
  Daga karshe Zahra da Aisha sai zuba mata ido kawai sukai.

 

  Jalal zaune a kasa, Abba nakan katifarsa dayake kwanciya, Jin kwankwasa kofar yasa Abba yace " Shigo."
Jalal yabi kofar da kallo, Umma ce ta shigo rik"e da tire, da samiru d'aure a kai, ta ajiye a gaban Jalal, Abba yace " Jalal bismilla."
  Kallansa Jalal yai yace "Abba amma ni......"
Abba ya katseshi yace " in har kanaso kaji sai kaci abinci, bansan inkaci wannan abincin kuma sanda zaka karacin wani ba."

  Jalal ya kalleshi da mamaki, Umma ta zauna a gefen Abba tare da bud'emai kwannon shinkafa da miyar da akai, nan Jalal ya fara cin abinci sai daya cinye tass sannan Abba yace " Habiba kema ki zauna ."
  Nan Umma ta zauna Abba ya kalli Jalal cikin tausayawa sannan yafara bashi labari tun daga farko........................
Har sai da yazo kan ranar da Fatima tazo shagonsa, Jalal hawaye kawai yakeyi na tausayawa Fatima.
  Abba yai ajiyar zuciya yace " Nafita kiran Isma'il ne a lokacin dana bar d'ana a shagona shida Fatima akan su jira ni, na fito naga maza guda 5 sun nufo shagon, karasawa nai kusa dasu tare da cewa  d'an Allah ina sauri ne amma in kunje akwai d'ana a shagon sai ku bashi kud'in.
   Sai a lokacin na kuka da kamaf abu suke sha, jin warin abin ma yasa na gane wiwi ce, na d'an ja baya sannan nace " hmm kuyi hakuri nad'auka shagona zaku.
  Ogan cikinsu dana kula shi bayashan komai ya matso kusa dani yace " Amadu Tambaya, Fatima wai na shagonka?"
Na kalleshi sai a lokacin na gane Chairman d'in garin mune wanda ake tunanin nad'awa a satin, kuma yaron gidan da Fatima ke aiki, kuma mijin da zata aura nan da kwana biyu. na kalleshi nace " Chairman nemanta kake?"
Yace " Eh yanzu abokaina sukace tun d'azu suka ganta a shagonka." sam har kasan zuciyata na d'auka ko k'iranta ake ko kuma shi ke san ganinta ko saboda wani abu, na kalleshi nace " Chairman kayi hakuri yanzun nan zata koma gida......."
Kafin na karasa maganata naji an kifamin mari, da sauri na kalli wanda ya naren d'aya daga cikin abokan Abdul d'in ne nace " Kai meye hakan kuma?"
  Wanda ya maren d'in yace " Wai Abdul kai wani irin mutum ne? Ya za'ai kana Matsayin Chairman ace wani banza mai shago har zai kalleka yad'inga ma tambayar banza? Banace ka barni nai handling d'in komai ba? Kobakasan ka d'ana ne?"
   Abdul ya kalleshi ga mamakina kamar me  tsoransa naga yaja baya, daidai nan cikin rashin sa'a ashe d'ana na kallanmu d'an muna kusa da shagon, ganinsa mukai yazo tare da kallan wanda ya maren d'in yace " Malam me Babana ya maka?"
  Wata muguwar dariya ya saki sannan yace " Good haka nake so."

Ban kawo komai a raina ba kawai sai gani nai an cafke min d'ana, an kuma samai wuka a wuya, nan fa ya shiga kuka.
   Na rikice sosai, kuka yakeyi sosai nima na shiga rokonsu,dariya suka samin na d'azun da ko sunanshi ban sani ba ya cilla ma wani d'an nawa tare da matsowa kusa dani yace " karkuma kai tunanin wannan ne kad'ai matarka tana hannunmu, ahh abin tausayi ko?"
    Sannan ya kalli Abdul d'in yace " kayi tafiyarka ko itama tafi karfin ka?"

Abdul ya girgiza kai yace " ai ko d'aureta ne sai nayi, ina gani ya nufi shagona ina ihu akan karyayi.......

  Kallansa nai duk na gana rikicewa nace d'an Allah kuyi hakuri, karku lalata mata rayuwa. Naga tashin hankali a lokacin kuma abin da yaban mamaki ba wanda yazo wucewa, gashi kamar sun tambaya, ba wutar nefa gashi dama a lokacin ba gen ake kunnawa ba.
    Dariya suka samin dashi sannan aka kwad'ama d'ana k'otar wuka a goshi wani ihu yasa kawai sai ga jini kankace mai......

Kuka nake sosak, suka cemin matarka da alama bata ma da lafiya ko? Na d'ago da mamaki d'an ko ni ban sani ba, suka kwashe min da dariya sukace dataji azaba cemana tai wai muyi hakuri karmu bari abin cikinta ya zube.

  Nan na matso tare da rik'e kafafunsu, tashin hankali ne ya karune a sanda suka fito da bindiga, suka nunani sannan suka nuna d'ana sannan sukace " kaje ka k'ira ma Fatima wanda take jira kayi sauri kafin Abdul ya mata ila."
  Na d'auka tausaya mata sukai hakan yasa da sauri na wuce na tadda ana fitowa daga masallaci nan na gyara fuskata na shiga cikin masu fitowar, Isma'il na gani na d'aure na sanar dashi Fatima na nemansa na gaggawa.
  
  Mun taho gabana sai faduwa yake, muna zuwa zan shiga sai naga sun min alamar inzo, hakan yasa Isma'il ya shiga shi kad'ai ni kuma na je gunsu, sukamin tafi sukace yauwa ka kyauta.
  Na kallesu nace d'ana fa? Mugun ya tab'e min baki sannan ya kalli Abdul da nima sai a lokacin na kalleshi yanasa wando, zaro ido nai nace " meke faruwa?"

    Hoton D'ana aka nunomin an saitashi da wuka sannan matata ansaita ta da bindinga, sukace abu d'aya zakai ka cecesu.
Kuka nake sosai ina rok'onsu, ban farga ba kawak naji karar mutanen gari, sukace cewa kawai zakai Abokinka Isma'il shiya mata fyad'e.

  Girgiza kai na shigayi ina kuka, mugun yace " to shikenan ka taimaki abokimka in yaso matarka da d'anka, da wanda ba'a haifa ba kwa had'u a lahira.

   Abba na zuwa nan yai share hawayensa, Umma ma haka, Jalal kam kukan ya kafe kaf kawai Abba yake kallo wani irin kallo daban fahimceshi ba ni kaina.
  Jinai cikin wata irin murya Jalal yace" Saboda tsoron kar ama matarka da d'anka ila yasa ka ce Amininka ne ya mata fyad'e?"
   Abba ya kalli Jalal sannan ya kara goge kwalla yace " Akan d'ana ba abinda bazan iyayi ba, ina ganin ansama d'ana wuka za'a yankashi mezai sa inkasa fad'ar kalma d'aya?"

  Jalal ya mik'e ya shiga jijiga kai sannan ya kalli Abba sai a lokacin wasu zafaffen hawaye suka fara zubo mai, Abba ya matsu tare da kokarin rik'e hannunsa Jalal yayi baya.




  © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM.*

  *Gaisuwa ga duk Masoyan littafin nan ....I Luv u Ol*❤����

7 comments: