Tuesday, 24 January 2017

JALALUDEEN 50

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 5⃣0⃣

 
       Jalal ganin Seemah a sume ya rasa inda zaisa kansa kuka kawai yake, yarasa meke faruwa shikem, addu'a kuwa duk wacce tazo mai yi yakeyi, kallanta yakeyi zuciyarshi sai kuna takeyi, Ammar ne yashigo da likita da sauri, nan likitan ya shiga duba Seemah, ya samu ta dawo daidai ya kalli Ammar da Jalal yace " ba nace kar a tada mata hankali ba? A barta ta samu nutsuwa ba? Ina tsorace muku abinda zai faru inbaku kiyaye dokukin nan ba."

  Yana kai nan yai waje, Jalal ya kalli Ammar da idanunsa da suka sha zubar da kwalla, yace " Ammar am.........."
Ammar ya katseshi da cewa " Jalal please get out."
  Jalal ya kalleshi cike da tausayi yace " amma......"
   Ammar ya d'aga mai hannu tare idanunsa taf da kwalla yace " Jalal kake kawai please. "
  A hankali Jalal ya karasa kusa da Seemah ya kalleta cikin tsananin tausayi da bege sannan ya juya harya kai kofa yaji muryar Ammar yace " idan kaje katambayi Mahaifinka waye mahaifin Seemah, shikad'ai ne abinda muke bukata yanzu daga gareka."

  Juyowa Jalal yai cikin tsantsar mamaki bai fahimci inda kalaman suka dosa ba, me suke ba Dad bane mahaifin Seemah ko me?"

   Dad ya gani a bakin kofa, wani irin kallo Dad yamai, Jalal yai kasa dakai tare da cewa " Yahkuri na sab'ama umarnink......"
  Hanya Dad ya nuna mai alamar yai waje, hakan yasa Jalal ya taka a hankali yai waje, yana fita yazauna akan dakalin gun, tare da rik'e kansa dake wainawa, agogon hannunsa ya kalla karfe 2 na dare ya buga, mik'ewa yai a hankali bayaji zama ya kamaceshi dole gobe da sassafe ya dira a birnin/gwari d'an jin me mahaifinsa ya sani dangane da abinda ke faruwa, kofar d'akin Seemah ya kalla tausayinta ya kara ratsashi, da alama yau tasan ba Dad bane mahaifinta sannan me ake nufi da Abbansa ya sani?
   Da alama Abba ne kad'ai yasan amsar tambayoyin nan.

    Seemah kam sai karfe hudu ta bud'e ido a hankali, Ammar ta kalla dake zaune akan kujera yana bacci, ta mik'e a hankali tare da yaye bargon da aka rufa mata, tai bakin kofa, a hankali ta bud'e kofar gudun karta tasheshi.
   D'akin Hajiya ta shiga, Dad na zaune shima yana bacci, ta karasa kusa da Hajiya tare da rik'e hannunta da hannuwanta biyu, Hajiya ta bud'e idanunta ta kalleta, Seemah hawaye suka zubo mata tai kasa da ido tace " Hajiya kiyi hakuri nasani dolene ki tsaneni, ko nice akama d'ana haka dolene in tsani duk masu hannu a harkar, sai dai nasani a kasan ranki baki tsaneni ba."
    Kallanta Hajiya tai da alamar tambaya, Seemah ta matse kwalla tare da kakaro murmushi tace " da kin tsaneni nasan da kin tilastama Dad ya rabu dani, da bazaki bari har ya rainani izuwa yanzu ba."

   Ta zare hannun hagunta ta share hawayen dake mata gudu tace " Nagode Hajiya da taimakonki, nagode sosai Allah ya saka da alkairi."

  Hawaye ke zuba a idanun Hajiya a hankali tasa d'ayan hannunta akan Seemah sai dai abinda takeji a kirjinta mai nauyi yasa ta kasa magana, Seemah ta girgiza mata kai tace " A'a hajiya basai kince komai."

  Tai ajiyar zuciya sannan tace " Hajiya na rok'eki ki yafema mahaifiyata da ni, d'an Allab ba dan mu ba."

  Seemah na kawo nan taji kuka na neman kufce mata, Seemah tasa kanta a jikin gadon ta shiga kuka mai tab'a zuciyar mai sauraro.

    Dad kam tunda ta shigo yanajinsu, kawai dai yayi shiru ne, Hajiya tasa hannu ta d'ago fuskar Seemah tare da share mata hawaye.

   Sun dad'e a haka kafin Ammar ya shigo da sauri, a firgice yake da alama yad'auka ko Seemah ta gudu me ko wani abun, ganinta kusa da hajiya yasa ya saki nannauyan ajiyar zuciya, Seemah ta kalleshi tare da mik'ewa.

   Bayan Sallah asuba su Dad sun tafi massalaci, suna dawowa suka ba kamar yanda suka barta ba, da sauri Dad ya karasa tare da tab'ata sai dai inaaaa.... Allah ya d'auki ran abarsa.

  _Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin_

  Ba karamin tab'asu tai ba wannan rasuwa, abu goma da ashirin.
  Sun dawo dukansu gidan Abba anan aka mata wanka, Seemah ma ta matsa dole itama ta dawo gida.

   Jalal kam yana sallar asuba ya wuce tasha, a mota a zaune kawai yake zuciyarsa taf take da tunani kala kala.
  Sun isa birnin gwari ya hau mashin ya karasa gida, yana sauka ya tsaya a kofar gidan tare da kwankwasawa, ba'ai minti 2 ba akazo aka bud'e, ga mamakinsa kanwar mamansa ce, tana ganinsa ta saki guda ya shiga tare da cewa " Goggo yaushe kika zo?"

  Ai ba gama rufe baki ba yaga 'yan uwan Abba da Umma suna ta fitowa ya kallesu da mamaki yace " toh! Taran me ake haka?"

  Goggo ta harareshi tace " Lalai wannan Angon ba kunya, watoma da alama bakasan a taru ayi zumunci a bikinka."

   Jalal ya maimaita kalmar Ango?
Umma ce ta fito fuska d'auke da fara'a tace " Jalal me kake a tsaye bazaka shigo ka kwashe gaisuwa ga 'yan uwa ba?"

  Ya d'anyi murmushi kad'an sannan ya shiga ya zauna sannan ya fara gaishesu, kowa sai tsokanarsa suke, ya mik'e tare da tambayar Umma ina Abba?, tace " ya fita d'azu zaije siyo kayan abinci." sai alokacin ya kuka da har fenti anyi a gida, badai da gaske suke ba?
  Yace "Zaheeda fa?"
Tace " tana d'aki." Nan ya wuce ransa duk a dagule, kusa da Zaheeda ya zauna, ta kalleshi tare damai murmushi yace " Kanwata da alama kina cikin farinciki, ko duk ganin 'yan uwa ne?"

Muryar Umma yaji tace " Dad'i takeji zaka auri 'yar uwarta Zainab."

  Jalal ya juyo ya kalli Umma yace " Wai Umma meyasa kuke min haka? Nifa ban d'auka abinnan da gaske kuke yi ba."
  Umma ta had'e rai tace " baka sani ba mai ya kawoka to? "
  Jalal yad'an furzar da iskar bakinsa yace " Zuwa nai muyi magana da Abba, ni banajin ma zan iya jiranshi ya dawo, Umma kawai fad'amin inda yake."

   Umma ta kalleshi tace " Ba dai cewa zakai ya janye auren ba?"

Jalal yad'an juya kai yace " ni auran nan ba'a gabana yakeba Umma, abun da ke damuna yafi karfin wannan auran."

  Umma ta kalleshi da mamaki tace " Badai......"
Jalal yai saurin cewa " Umma d'an Allah ina Abba?"
Tace" Yana lambun Basiru."
Jalal ya mik' e tare da kallan Zaheeda sannan ya juya, Umma ta matso kusa dashi tace " Jalal yanaga kamar ka fad'a? Sannan da alama akwai abinda ke damunka naga gaba d'aya fuskarka ta canza."

Kallanta yai sannan ya runtse ido yace " Umma banaso 'yan uwa susan abinda ke damuna shiyasa nake kok'arin b'oyewa kibari inje gun Abba tukun."
  Tai ajiyar zuciya tace " to sai ka dawo."


  Jalal ya fito, sai tsokanarshi ake, shikam sai yake kawai yake musu, yana fita Goggo ta shigo gun Umma tace " Yaya Habiba nikam kamar Jalal baya farin ciki."
   Umma ta kalleta tace " meyasa kikace haka?"
Goggo ta d'an rik'e hab'a tace " gaskiya bama haka Jalal yake ba sam, naga kamar ya canza, halayarsa ma kamar ta canza, Allah dai yasa ba wani abun bane."

  Umma ta kalleta sai dai ta kasa bata amsa, Addu'arta d'aya Allah yasa ba zancen nan Jalal zaina Abbansa ba.

   Jalal kam kai tsaye Lambun Basiru makocinsu ya isa, yanazuwa Basirun yace " yanzu kuwa yabar nan, ya koma gida."

Jalal ya juya yai hanyar gida, wayarsa ya rik'e wazai k'ira ya tambaya jikin Seemah?
  Da sauri ya k'ira Sagir bayan sun gaisa yace "Sagir d'an Allah ka dubomin halinda Seemah ke ciki."
Sagir yace " to, nan sukai sallama."


  © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

1 comment: