����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣1⃣
Seemah zaune take kawai, a rakub'e a jikin gado, sai kallan y'an uwa take suna zuwa gaisuwa, sam ko magana batayi bare cin abinci, duk ta rame ta canza a kwana d'aya.
Tana zaune tana jan carbi taji sallama, jin muryar yasa ta d'ago da sauri, Junaid ya kalleta tare da sakar mata murmushi, kuramai ido tai a hankali hawaye suka zubo mata ya matso kusa da ita tare da cewa " Kanwata ai saura kiris in kasa gane ki, wace irin jinya kikai haka?"
Kallansa tai kawai ga mamakinsa sai yaga ta fashe da kuka, kallanta yai da namaki, sai kuma can yace " Seemah mutuwa fa ba'a san a d'inga mata irin wannan kukan, bare Hajiya da batasan kuka addu'a kawai zamu mata."
Seemah ta d'ago a hankali tanasan mai magana, yace " anma wani irin cinwo kikai haka?"
Zahra ce ta shigo ganin Mutum yasa tai kasa dakai tare da gaisheshi, Junaid ya d'ago ya kalleta yace" Badai badai ba?"
D'agowa tai tare da nuna shi tace " yayana?"
Kallanta yai yad'an kanne ido yace " badai badai ba?"
Tace " badai yaya bane wannan?"
Dariya yai yace " na d'auka kin manta inkiyar tamu."
Tai murmushi tare da matsowa tace " yayana yaushe a gari?"
Yace "d'azu na shigo ya hakurin mu?"
Tace " Alhamdulila"
Kallan Seemah yai yace " Kanwata mey........"
Da sauri Zahra ta katseshi tace " tashi yaya muje ka gaida Mamie."
Ya mik'e tare da kallan Seemah, nan sukai waje, Seemah ta share kwalla Allah sarki rayuwa, a da tad'auka 'yan uwanta ne na jini yanzu kuwa ta gane ashe bata da alaka da dukansu, itafa? Inane cibiyarta? Suwaye 'yan uwanta?.
Jalal yayi sa'a a kofar gida yaga Abba, da sauri ya karasa gunsa, Abba ya kalleshi yace " Jalal kai nake jira ai, na shiga ciki aka sanar dani ka iso."
Jalal ya kalli Abba tare da cewa " Ina Kwana?"
Abba ya amsa tare da rik'o hannun Jalal yace " Nagode Jalal da baka bani kunya ba kazo tun kafin ranar bikin, nagode kwarai, Zainab ta koma gidansu acan zasuyi taron su."
Jalal kallan Abba kawai yakeyi, can yace " Abba inada magana mai mahimmanci dakai."
Kallansa Abba yai yace " Jalal wace magana ce haka da bazaka bari sai bayan biki ba?"
Jalal ya girgiza kai yace " Abba banajin zan iya runtsawa sai naji abinda ke faruwa."
Gaban Abba ne ya fad'i ya kalleshi cikin tsoro yace "Jalal me kakesan ji?"
Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace " Abba meye tsakaninka da Dad d'in Seemah?"
Da sauri Abba ya juya baya gabansa ya cigaba da fad'uwa, Jalal ya kalleshi sannan ya matso ta gabansa, yace " Abba bai kamata ka cigaba da b'oyemin wani abu ba, me ka musu suka tsaneka haka? Meye tsakanin ka dasu dahar suke tunanin kafisu sannin abinda si basu sani ba?"
Abba ya had'iyi yawu sannan cikin tsoro yace " Jalal banasan maganan nan na kuma hanek da karamin."
Ga mamakin Abba kawai gani yai Jalal ya tsugunna a gabanshi, yace " Abba d'an Allah ka fad'amin bakasan yanda nakeji a zuciya ta bane a wannan lokacin."
Abba yai ajiyar zuciya yace "naji zan sanar dakai abinda yafaru amma da sharad'i sai ka min alkawari."
Zuciyar Jalal ta matsu taji komai yace " na ma Abba koma akan menene."
Abba ya kalleshi idanunsa sunyi ja, yace " tun ranar da Isma'il yazu gidan nan nasan sirrin nan dole ne ya bud'u, in har kuma kanasan insanar dakai sai kamin alkawari tsakaninka da Allah cewar ko menene tsakanin mu bazai hanaka auren Zainab ranar Asabar ba."
Jalal ya d'ago da sauri ya kalli Abba yace "Abba me kake nufi?"
Abba yace" bazan sanar dakai ba har sai ranar da aka d'aura muku aure da Zainab."
Jalal ya mik'e a zabure yace " Abba d'an Allah......"
Abba ya katseshi da cewa " In har kanasan kaji to sai ka jira ranar auranka, alkawari na maka kaima kamin, haka ya kamata mu barshi."
Abba na kainan ya wuce cikin gida, Jalal bai kula bane amma hannun Abba rawa yakeyi.
Jalal ya naushi bango da hannunsa yana huci ya rasa mai zaiyi.
Wayar Sagir ce ta katseshi, ya d'aga da sauri tare da cewa " Sagir ya Seeman?"
Sagir yai shiru, Jalal yace Sagir ya kai shiru?
Sagir yace " Jalal kakarta ta rasu."
Jalal yafara " *Inna lilahi wa ina ilaihi Raji'un*"
Nan ya kashe wayar tare da silalewa ya zauna a dandaryar kasa, hannu biyu yasa ya rufe fuskarsa zuciyarsa na k'una, wani hali Seemah take ciki? Ance in tambayi Abba mahaifinta shikuna yace sai na auri Zainab, idanu ya runste sai ga hawaye sun zubo, Seemah ya zanyi?
Mutane sai wucewa suke suna kallansa.
Ya dad'e a gun kafin ya mik'e ya fara tafiya, wayar Ammar ya d'aure ya k'ira, daga gun Ammar dake zaune gun amsar gaisuwa ganin k'iran Jalal yasa ya mik'e yai gefe tare da d'agawa, Jalal yai sallama Ammar ya amsa, Jalal yace " Ammar ya hakuri? Ya kuma jikin Seemah? Tanacin abinci kuwa?"
Ammar yai shiru can yace" Jalal baka fahimci abinda muke nufi bane? Ko kuwa idanunka ne suka rufe?"
Jalal yai shiru, Ammar ya cigaba " abu d'aya muke buk'ata agunka ka tambayar mana mahaifinka waye mahaifin Seemah shikad'ai mukesan ji daga gareka."yana kai nan ya katse wayar, tare da kasheta gaba d'aya.
Jalal ya samu wani dakali ya zauna kamar maraya, kalaman Ammar kawai yake tunawa........
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
��♀
Tnx
ReplyDeleteSannu da kokari,amma ki dan rinka yin post din yana yawa cos wannan is too short.
Waiting for d nxt chapie
Allah ya kara basira kuma ya amfanar....
ReplyDelete