Saturday, 7 January 2017

JALALUDEEN 37

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 3⃣7⃣




    Seemah ta shiga knocking d'in toilet d'in Ammar na tsaye jikin kofar tunaninsa d'aya ya ya zai kalli Seemah yanzu? A matsayin me? Ganin yaki bud'ewa yasa Seemah ta zame ta tsugunna a jikin kofar tare da cewa a hankali " Yaya nice fa? Nad'auka tsakanina dakai babu 'yar haka, ko me ya faru ya kamata in sani indai har abin ya shafeka."

  Ammar shima ya tsugunna a jikin kofar ta ciki yana sauraranta, Seemah tai ajiyar zuciya tare da cewa " yaya please ka bud'e muyi magana? Please? "

  Ammar ya motsa baki har zaiyi magana kuma ya fasa, Seemah ganin yayi shiru yasa tace " yaya kasan me? Ni yanzu na daina san Yaya Habib d'an haka mu koma kawai gidan Dad ni dakai muzauna."

  Nan ma shiru yai sai dai yanda na kalleshi naga fuskarsa tad'an saki, Seemah tai murmushi sannan ta cigaba " yaya amma in muka koma wazai d'inga mana abinci? Kasan ban iya girki ba."

  A hankali murmushi ya bayyana a fuskar Ammar, Tab'e baki tai ta cigaba " yaya nasan dai kaima ba wani abinci ka iya ba, to ya zamuyi?"

  Murmushi sosai Ammar yai, jiyai zuciyarshi tayi haske, Seemah kam ganin yak'i kulata yasa ta mik'e tare da cewa " yaya nasan kanaji na amma tunda kak'i kulani, shikenan bari nai tafiyata."

  Jin alamun ta mik'e yasa Ammar ya fito daga toilet da sauri, yana zuwa ya rungumeta ta baya,  a hankali tace " Yaya?"

  " wait for a moment please." Ya fad'a cikin wata murya dayasa Seemah tasha jinin jikinta, Ammar ya dad'e a haka kafin a hankali ya saketa, juyowa tai ta kalleshi tace " Yayana meke damunka wai?"
  Murmushi yai tare da cewa Seemah.......wayar sa ce ta katsesu da kara, da sauri Seemah ta d'aga wayar ganin number Jalal, cemata kawai yai yazo, tace ok, sannan ta juyo ta kalli Ammar tace " yaya my Deen yazo bari in d'an fita waje ina zuwa." Bata jira amsarsa ba tai waje da sauri, Ammar ya bita da kallo zuciyarsa ba dad'i.

  Seemah kam tana fitowa ta kara kallan inda taga wannan mutumin sai dai ganin ba kowa yasa tai tsaki tare da fita neman inda Jalal yake.

  Jalal kam daga nesa ya ganta, murmushi ne ya bayyana a fuskarsa ya bud'e motar ya fita,  kansa ya samu da d'aga mata hannu, tana ganinshi itama ta saki murmushi ta karaso a hankali cikin tafiyarta, tana zuwa kusa da shi suka kalli juna suka saki murmushi a tare kana ganinsu kasan suna tsantsar farinciki na ganin juna, Seemah ta kalli Jalal tace " My Deen ya jikin naka?"

  Yace " Ahhh!!!! Ni sam na manta ma banda lafiya a jikina."

Da mamaki tace " ban gane ba?"

"Zuciyata tana rashin lafiya wazai damu da ciwon dake gangar jiki?"

Dariya Seemah tasa sannan ta rik'e hab'a tace " tooh? Oh ni? Yaushe my deen yazama malamin kalamai? "

Hararta yai yace " bawani malamin kalamai abinda ke damuna na fad'a"

Zagayawa tai ta shiga mota, shima ya koma ya zauna tare da juyowa yace " ya Ammar d'in?"

Tai ajiyar zuciya tace " I don't know,  haryanzu bai cemin komai ba."

Jalal ya d'an matso da fuskarsa kusa da ita yace " ko dai bayasan ya fad'a miki ne? Ko sirri ne?"
  Ta murgud'a mai baki tace " ba wani sirri tsakanina da yayana."
  Jalal yace " naji, amma meyasami wayarki?"

Ta had'e rai tare da cewa " ba yaya Habib bane ya kwacemin waya."

  Jalal ya koma ya zauna jikin kujerar, sannan ya daure yace " because of me?"

   Ta kalleshi idanunta suka ciciko, tace " karkadamu Deen komai zai zo da sauki, ni takace, kaji?"

  Murmushi yai sannan ya matso tare da d'anjan kumatunta, kai ta karkatar tace " ya kukai a Birnin gwarin?"

  Jalal ya kalleta tare da neman zare hannunsa, da sauri ta rik'o hannun sa tare da kura mai ido, murmushi ya kakaro yace " karki damu kinji?"

  Daga yanda yai maganar tasan akwai wani abun, sakeshi tai tare da cewa " Deen ina tsoron kar a rabamu da......."

  Ya tsarsa yakai bakinta yace " please Meemah karki karasa, ba abinda zai fari sai alkairi."

Hawayen da take boyewa ne suka zubo, yasa hannu ya share mata sannan yace " banasan ind'inga ganin idanun dana fiso a duniya suna zubda hawaye, abin takaicin kuma nine nake sasu zubar da hawayen."

  D'agowa tai ta kalleshi tare da girgiza kai, Jalal jiyai kamar shima hawayen zaiyi, da sauri ya bud'e motar ya fita, Seemah ta bishi da kallo, tare da kokarin fita, vibration d'in dataji wayarsa nayi yasa ta kalli wayar *ZAINAB* abinda taga ya fito a jikin wayar kenan kawai sai ta samu kanta da d'aga wayar, Zainab kam kai tsaye tace " yaya ya zakayi? Su Abba fa da gaske suke d'azu ya fita kaiwa abugo Iv na d'aurin aure, da alama next week d'in nan za'a d'aura."

  Jikin Seemah ne ya shiga rawa, batasan sanda ta yarda wayar ba, duk bata hankalinta, bud'e kofar tai tafito, Jalal na ganinta ya taho, sai dai ko kallansa batai ba tafiya kawai take, ganin haka yasa Jalal yasha gabanta yace Seemah menene? D'agowa tai ta kalleshi, jitai kamar tasa ihu, matsawa tai gefensa ta cigaba da tafiya, Jalal ya riko hannunta ta baya yace Seemah? Janye hannunta tai kawai tasa gudu ta koma cikin hotel d'in, binta yai da kallo sannan shima yai ciki, sai dai inaa, sam bai ganta ba, securities sukazo sukace ya fita.





  Dad ya isa Birnin gwari lafiya, bai sha wahala sosao ba wajen neman gidan, saboda unguwar kusan duk sunsan gidansu Jalal,  tunda ya fara shiga lokon da kafa ransa yake a b'ace, mamakinsa amma lalai Jalal d'in nan yagama raina musu hankali, sai ma daya isa gidan, ba gate bane kawai koface ya d'an bubuga jiyai ance ana zuwa, ba'a dad'e ba wata yarinya budurwa sanye da hijabi tazo ta bud'e tare da mai kallan mamaki, sai kuma can tai saurin cewa " ina kwana?"

  Lafiya dad ya fad'a tare da cewa nan ne gidansu Jalal? Kai ta d'aga tace " nan ne amma bayanan."

  Dad ya kara kallan wajen gidan yace " nasani iyayensa nake nema." Zuciyar zainab ce ta buga, badai laifi yai ba ko? Ahankali tace shigo, Dad yasa kafa cikin gidan, yabi gidan da kallo, Umma ce ta fito tare da cewa sannu da zuwa, ya kalleta yace yauwa, tace shigo, wani kallo yakarama gidan sannan yace
" basai na shiga ba dama zuwa nai akan ku jama d'anku kune, yasan matsayinsa, 'yata Seemah namata miji ya fita daga harkarta tun kafin rai yazo yana b'aci gwara ayi magana a mutunce."

  Jikin Umma yai sanyi, tace " bawan Allah kayi hakuri mu kanmu kaga wace mukeso ya aura kuma ma wani satin za'ai auran, d'an haka ka kwantar da hankalinka."

  Dad ya matso tare da ajiyema Umma envelope yace " nagode da fahimtarku, ga wannan kyautace ba yawa, ku bawa d'anku shawara d'an masani shine ya makallewa 'yata."

  " ka koma d'an kuwa kayi zuwan banza."

  Da sauri Dad ya juya jin furucin daga bayansa, juyawa yai ya kalleshi harzai yi magana sai kuma ya kura mata ido sosai, shi kanshi Abba kalansa yakeyi, a hankali Dad ya karaso kusa da Abba, Dad yace " malam kamar na sanka ko?"
  Abba shima da mamaki yace " nima kamar na sanka,"

Dad ya d'an juya kai yace ya sunan ka? Da mamaki yace Ahmad.

  Idanun Dad ne suka rik'ed'e cikin wani yanayi ya riko wuyan Abba ya jashi zuwa jikin bango, yace Amadu mai shago?

  Idanu Abba ya zaro, Umma da zainab mamaki ya kamasu menene hakan.

  Cikin tsawa da fad'a Dad yace " Amadu ne? Kai ne?"

  Abba ya kara zaro ido yace " Isma'il?"

  Matsashi sosai Dad yai har numfashin Abba ya fara rawa, da sauri Umma da zainab suka matso sunamai magana, Dad cikin masifa yace " Amadu? Kaine? Yama za'ai in mantaka? Mutumin dakajazama rayuwata, ka lalatamin rayuwata."

  Umma najin haka tafarayin baya baya tana jijiga kai, idanunta na zubar da ruwa, zainab kam ganin yanda Abba yakeshan wahala yasa tai saurin tsugun nawa ta rik'e kafafun Dad.



© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

1 comment: