����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 3⃣8⃣
Dad ganin Abba na kakari yasa ya sakeshi sannan yace " me kakeyi a nan?"
Kafin Abba yai magana Zainab tayi saurin zuwa kusa dashi tace " Abba sannu." Hakan yasa ya gane wato gidan sa ne, cikin tsananin mamaki da takaici Dad yace " Jalal d'anka ne?"
" Eh" zainab ta fad'a sannan ta cigaba" amma malam menene hakan?"
Wani kallo Dad ya mata yace " dama ina 'ya'yan Amadu zasuyi tarbiya? In ba haka ba yaza'ai yarinya dake kid'inga shiga maganar manya?"
Da sauri tai kasa dakai itakanta batasan ya akai tai magana haka ba, jitai Umma tace " Zo ki wuce ciki."
Simi-simi Zainab tai ciki, Abba ya d'ago yace " Isma'il!!!" Dad ya nunashi da yatsa yace " karkaga wai na maka magana ka d'auka wai na yafe maka abinda kamin ne a shekarun baya, Amadu kaine mutum na farko kuma na karshe da bazan tab'a yafema ba, alhakina dama Fatima shine yasa ka kasa ci gaba, kuma wlh kaji na gaya maka kayi gaggawar fad'a ma d'anka ya barmin 'yata tun kafin na aikashi prison. "
Yana kainan Dad yai hanyar waje, Umma ce da sauri ta matso ta tsugunna a bayansa hawaye na zuba a idanunta sosai, tace " Malam d'an Allah kayi hakuri ka yafe mai, na sani......."
Dad bai jira ta karasa ba yasa kai ba bar gidan, yana fita waje ya juyo ya k'ara bugawa gidan kallo, sannan yai gaba.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Jalal kam a waje ya tsaya ya rasa meya faru da Seemah ta canza lokaci guda haka, to amma yazaiyi? Sun hanashi shiga, wayar sa ya d'aga kawai ya k'ira number Ammar sai dai tanata ringing ba'a d'aga ba, cilla wayar yai gefen kujera ya shafi goshinsa tare da cewa Ya Allah!
Seemah kam tana shiga d'akin ta tadda Ammar a tsaye ta jikin window da gudu ta karasa ta rungumeshi ta saki wani irin kuka mai tab'a zuciya, Ammar kamar ta sosa mai inda yake mai kaik'ayi shi kansa so yake yai kuka kamar haka, jiyai idanunsa ya shiga kawo ruwa, d'an kukan gar zuciyarsa yake tab'awa, Sam ya kasa cewa tai shiru sai ma shima kukan da yakeyi, sunfi minti 10 a haka kafin cikin kuka Seemah tace " Yaya ya zanyi?" Ta karasa maganar tare da d'agowa ta kalleshi, ganin yana kuka shima yasa ta shiga girgiza kai tana hawaye tace " yaya me yake damunka please? " hannu yasa ya goge hawayen yace " fad'a kukai da Deen d'in naki?"
Baya ta juya ma Ammar tace " yaya shikenan, rayuwata tazo karshe."
Da sauri Ammar yadawo tagabanta ya rike kafad'arta yace " Seemah me kike fad'a haka?"
Hawayene ya zubo mata tace " yaya aure za'amai nextweek."
Ta karasa maganar da fashewa da wani kuka, Ammar ya kama hannunta ya zaunar a kan gado, sannan shima ya zauna a gefenta ya juyota setinsa yace " Seemah?" Kallansa tai da mamaki jin yanda ya kararra gurin k'iran sunan, yace " Seemah!!" Tace " yaya inaji menene? Ka tsoratani."
Fasa fad'ar abinda yai niyya yai ya wayance da cewa "Seemah ki rage wannan soyayyar da kikema Jalal bana tunanin yana sanki kamar yanda kike sansa."
Hawaye ta share tace " kaima haka kake gani ko yaya? Na sani yaya, nasan nafi sansa akan yadda yake sona, in fad'ama gaskiya yaya ni na fara cewa ma ina sanshi."
Ammar ya juyo ya kalleta, hawayenta suka cigaba da zuba, tace " amma yazanyi yaya? Ina sanshi sosai, kome nakeyi yana raina, in ban ganshi ba ji nake zuciyata kamar zata fashe, in muna tare kuma ji make kamar kar mu rabu."
Tai ajiyar zuciya tace " ya Ammar banaji zan iya rayuwa ba Deen."
Ammar duk da kalamanta sun mai zafi a zuciya amma bai nuna ba murmushi ya kakaro ya matso kusa da ita yace " Seemah yaushe zuciyarki ta kamo haka?" Tace " ban sani ba Ya Ammar ni kaina ban sani ba." Ta karasa tare da sa kuka, jawota yai jikinsa yana shafa bayanta alamun lallashi.
Jalal ya dad'e agun ganin Seemah tak'i fitowa yasa ya juya gidansu Sagir, yai parking motar yashiga gun Sagir, d'akin a bud'e yake sai dai ba kowa a ciki, shiga yai ya hau kan gado ya kwanta tare da d'aura hannayensa akan goshinsa, tunanuka sun mai yawa a hankali hawaye suka ziraro ta gefen idanunsa, sam bai ji sallamar Sagir ba, sai da yaji an dafashi, kallan Sagir yai sannan ya mik'e zaune yace " Sagir ina kaje?"
"Ummanmu ce zasu fita shine na musu sallama"
Jalal yace " Amma bansan sunanan ba dana gaidasu ai."
Dariya Sagir yai yace " kana cikin tension ina zan fad'ama?" Ya cigaba " amma ya? Ka ganta?"
Kai Jalal ya d'aga alamar eh, Sagir yace " Amma kamar baka farin ciki, fad'a kukai?"
Ajiyar zuciya Jalal yai yace " nikaina bansani ba, da alama Seemah hard to get take neman yimin, sai dai ni a wannan lokacin batasan banasan muyi fad'a ba sam d'an ni kad'ai nasan me nake ji."
Sagir ya kwashe da dariya yace " Lalai Mr Romeo."
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♢♡♢♢
Habib ya isa Suleja sai dai jikin Hajiya ba dad'i sosai kusa da ita ya zauna, ya kalli Kawo yace mu wuce Abuja kawai kawo a kaita asibiti, kaga Abba da Dad duk suna can, Kawo yace haka ne wannan ma shawara ce.
Hajiya ya kalla ya rik'e hannunta, jiyai itama ta kama hannunsa da karfinta tace " Isma'il bakasan mahaifin yarinyar nan ba kai kanka, taya za'ayi ka nemi had'a zuri'ata da jinin da bamu sani ba."
Idanu Habib ya zare da jin kalamanta ya kalli Kawo a zabure me Hajiya take fad'a? Da sauri kawo ya d'an matsar dashi ya zauna kusa da Hajiya yace " Amina kalle ni nam ba Isma'il bani Habibu ne me kike fad'a haka?"
Jikin Habib ne yafara rawa ya mik'e tsaye a rud'e yace " Kawo me take nufi da kalamanta?"
Kawo ya kalleshi cikin tsoron furucin da Hajiya tai, yanzu me za'a ce?
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
Thanks.
ReplyDeleteThis comment has been removed by the author.
ReplyDeleteNi dai ina roko kuma ina tuni cewa "wadanda suka shaku da littafi kuma suka buk'atu dashi kuma basu da lokaci ko hakurin jira, kuma suna da halin saya, ai daidai ne a sayar musu da littafin bisa kima da daraja saboda a saukaka musu kuma a cigaba da rike su a matsayin masoya "fans".
DeleteSaboda idan mutum ya zama ya zaku ko bashi da hakuri ko ba shi da lokaci kuma ba a Samar masa da mafita ba toh sai a rasa soyayyar "fandom" din tasa ko kuma ya cigaba da bi amma a takure kuma ba shauki ko soyayya. Don wasu su nayi ko kowa abinda yake kenan, baya nufin ya zama k'aida ko dole sai marubuchi ya bi tunda ba talla kuke a shafin ba, ba wani programme ake gabatarwa ba balle ace Sauran abinda ake yi zai gurgunce, karatunne kawai ake shigowa shafin a yi a fice, marubutan turawa dama na kudanci suna da irin wadannan mafitan Ga masoyansu.
Wallahi a rana na kan shigo sau biyar ko bakwai ko goma ina dubawa kuma ba komai, ba bayani.
Mun San rubutun da wahala, kuma akwai wasu hidimomi da ake yi, to amma tunda marubuchi ya fara kuma ya jawo hankalin mutane Yana da kyau ya sama wa kansa da masoyansa da basu lokaci ko hakuri kuma suke da halin sayan littafi Guda a matsayin Guda goma fiye maslaha.
Sai mun ji bayaninki.
Allah ya taimaka.
Idan bukatar kebantacciyar amsa my whatsapp shine +2348038367703 ko Facebook page Mukhtar Lawal Suleiman.