Friday, 20 January 2017

JALALUDEEN 48

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 4⃣8⃣


    Anyi suna lafita kowa na murna, Abba kam shima a lokacin Mamie nada tsohon ciki hakan yasa batazo ba, sai dai tunda akai suna jikin Samira yak'i dad'i kullum cikin cuta.

   Fatima kam duk karshen sati suna zama da Isma'il a makaranta ya koya mata karatu, a sanu a sanu wata shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu batare da Isma'il ya farga ba, sai dai bai tab'a tunanin zai iya furta mata yana santa ba saboda sau dayawa yanaji tana zancen batasan kishiya.

   Rayuwa kenan yanzu an wayi gari shekararsu Jalal 5, kusan kullum Jalal na gidansu Ammar inkuwa baizo ba to zakaga Ammar a nasu gidan.

Jalal ya taso yaro mai zuciya, shikuma Ammar hakuri gareshi, a duk lokacin da yara sukaso rainama Ammar hankali, Jalal ne ke zuwa ya musu shegen duka, hakan yasa suka daina tsokanar Ammar.

   A b'angaren Fatima kam tana shiga gidansu Isma'il sosai sai dai a randa tasan yanada aure harda 'ya'ya ranar tasha kuka harda zazzab'inta, yanzu Fatima ta kile sosai d'an inba fad'ama akai ba bazaka tab'a cewa 'yar kauye bace.

   Samari kuwa dake santa a k'aueyen nan yawa garesu, sai dai ita zuciyarta nakan Isma'il, ta kasa tsayawa da wani sam.

   Kamar yanda ta saba yau asabar ta gama duk ayukanta, tace " Hajiya zan fita."

  Hajiya tace " Fatima jiya da daddare sai nawa Abdul ya shigo?"

  Fatima ta kalli Hajiya tace " Hajiya wlh bansani ba nidai harnai bacci banji motsin bud'e kofa ba, amma ai dama yace Campain yakeyi."

  Hajiya tai shiru tace " wani campain me da daddaren Allah? Keda kin yarda? So yake yaja min zagi dama mutane nacemasa d'an mace tunda mahaifinsa ya rasu da daddewa."

  Fatima ta matso kusa da Hajiya tace " Hajiya Allah ya gani kinayin daidai kokarinki ga matsalar kafar da kike fama da ita sannan ni fa hajiya? Kinsan iyayena sun rasu tun ina karama agun kanwar mahaifina na taso."

  Hajiya tai murmushi tace " jeki ko ba gun karatu zaki ba?"

Mik'ewa tai tana murmushi ta mata sallama ta fita, Hajiyar Abdul ta bita da kallon k'auna.

  Tazo fita taji an cafko hannunta, ko bata juyaba tasan waye hakan yasa ta dage ta fizge hannunta da karfi, Abdul haushi ya kamashi, yana takaicin yanda take nunamai kamar tana kyamarsa, sa hannu yau ya fizgota ya matseta jikin bango, ta d'ago tare da had'e rai, Abdul ya kalleta ya saki wani mugun murmushi yace "Fatima na yanke hukuncin muyi aure kawai."
  Batasan sanda ta bugamai wata harara ba, batai auni ba taji ya kifa mata mari yace " ni kike harara? Ko kin manta ni waye?"

  Kasa tai da kai tare da rik'e gun, ya saketa yace " ankusa nad'ani Chairman a garin nan, in har mai aikin gidanmu bata bani girma ba wa zai bani?"

  Ta kalleshi a ranta tace " tir da wannan mik'amin da ake shirin ba ka." Ya saketa tare da shiga ciki, cikin takaici itama ta wuce waje.

  Abdul na shiga ya gaida hajiya tare da cewa " Umma nikam aure nakeso."

Kallansa tai cikin mamaki da kuma murna tace  " wa kakeso Abdul? Naji dad'i?"

Ya d'an sosa k'eya yace " ni Fatima zaki auramin."

  Murmushin fuskarta ne ya fad'ad'a tace " Da gaske Abdul?"
Yai murmushi yace " sosai ma, amma d'an Allah Umma tunda yarinyar nan a gunki take kuma anan gidan zata zauna asa auren nan da sati 2."

  Dariya ta saki tace " Abdul matsuwar ta menene haka?"
Yace " ni kawai so nake ayi nan kusa."

Shiru tai lalai dole ta yarda ai nan kusa, d'an tasan inka ga namiji ya matsu da aure sosai to gwara amai kafin abin kunya ya ratsu ciki.

Tace to naji jeka.

Nan ya mik'e tare da Murmushin mugunta, d'an shikam kullum da sha'awar ta yake kwana.

  Fatima kam tana fitowa a waje kan dakali taga Jafar da Ammar, ta matsa tare da cewa " Me kukeyi a nan?"

Jafar ya kalleta yace " a zaune kawai muke."

Fatima tai murmushi tace " ku bakwa wasa irin na yara?"

Jafar ya kalli Ammar yace " yaran ne 'yan rainin hankali, munfisan muyi wasanmu mu biyu."

Tace " Ammar ina Babanka?"

Yace ya fita, tai murmushi tad'auko naira goma a jakarta tace " ungo kusai alawa."
  Jafar ya kalleta yace " mun gode amma bazamu ansa ba."

Ta kalleshi sannan tace "Ammar kaifa?" Kallan Jalal yai yace "a'a mun gode. "

  Ta d'an yi kasa dakai alamar rashin jin dad'i sukam sauka su kai suka shiga gidan da gudu.

A hankali take tafiya, samarin garin kowa na sha'awar yanda take da hankali ga kyau, harta isa makaranta, ta tadda Isma'il a zaune, ta gaidashi ya kalleta cikin kulawa yace " yau kin d'an dad'e Allah yasa lafiya."

  Ido ta kuramai kamar batasan me yake cewa ba, ganin yanda take kallansa yasa yai murmushi yace "da alama kunyar fulani tabar jikinki."

  Da sauri ta d'auke ido tace " Malam duk kunyata?"
"Hmm a da ba? Yanzu naga harkin fara kurama mutane ido."
Ta had'e rai tace " kaine mutane?"

Yai murmushi ya wayance da cewa " matso muyi sauri matata batajin dad'i."

Had'e rai sosai Fatima tai dama yasani, shikuma harga zuciyarsa yasan yanasanta sosai, sai dai yasani bazata iya auransa ba, ga 'ya'yan masu kud'i na santa samari, ina zai so abinda yake neman fin karfinsa?shiyasa yakesan itama ta daina sanshi.

Mik'ewa tai cikin tsananin kunar rai ba tace mai komai ba tai hanyar waje.

Isma'il ya kalleta yace " nayi zuwan banza kenan?"
  Tsayawa tai cak batare da ta juyoba idanunta na zubar da kwalla, mai yasa zuciyarta bata iya b'oye so ba? 

  Haka ta juya sukai karatun ba dad'i.


  Tana dawowa gida Hajiya tasanar da ita zancen aurensu da Abdul,  cikin mamaki ta kalleta tace " ni kuka Hajiya? Mai zai yi dani 'yar kauye?"

Hajiya tace " Fatima kitaimakeni bad'an shi ba d'an ni ayi auren nan,wannan shine buri na d'aya da ya rage min a duniya, d'azu na k'ra kanwar Babanki bakiga murnar datai ba."

  Fatima ta d'ago a ranta tace tayi murna mana tunda taji zan auri mai kudi.

  Murmushin yake Fatima tai mata sannan ta mik'e ta shiga d'an d'akinta, tana isa ta fad'a gado kuka sosai ta shiga yi, meyasa ba wanda zai tambayeta ko akwai wanda takeso? Tasani da mahaifanta nada rai dasai sun tambayeta ko tanaso, ta dad'e tana kuka kafin ganin ba mai lalashi ta mik'e.

   Isma'il kam ya dawo yana shiga d'aki, ya tadda Samira a zaune, ya shiga shima ya zauna, tamai sannu da zuwa tare da cewa" dagaske kaima kanacikin jerin masu san Fatima?"

  Da mamaki ya kalleta yace " me kike fad'a haka?"

Ta juyarda kai tace " d'azu na fita gunsu Hajiya naji wani saurayi yazo kawo musu kara wai kana santa duk asabar da lahadi sai kun had'u a makaranta kunyi zance."

  Ya mik'e tsaye yace " kuma sai kika yarda da zancen nakejan yarinya zuwa makaranta inayi?"

Juya kai ta sakeyi hakan yasa ya gane wato ta yardan kenan, a zuciye ya fito waje,  Hajiya ya gani dasu Goggo suma suna maida zancen, kallansu yai cikin takaicin abinda kowake fad'a zaiyi magana sai ga Jafar ya shigo, ya kalli Isma'il yace " Dad wai ana magana dakai."

  Yace " Jafar inji wa?"

Yace " Abba nane."

Tare suka juya sukai waje, bayan sun gaisa da Amadu ne yace " Amadu ya akai?"

  Amadu yai shiru can yace " haryanzu kana koyama Fatima karatu ne?"

Kai ya gyad'a alamar eh, Amadu ya dafa kafad'arsa yace "kayi hakuri ka rabu da yarinyar nan, nasan ka sosai Isma'il nasan kuma kana santa, wani karatu kake koyamata har shekara 5?"

  Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba " kaga d'azu a shago naji ana gulmarka, sannan naji ma yarinyar yaron gidan zata aura, Isma'il ka hakura kasan Abdul wanda za'aba Chairman ba mutunci garesu ba su da abokansa."

  Isma'il zuciyarshi ta tab'u dajin wai anmata miji, ya d'aure yace " nagode Amadu, insha Allah kuma mungama karatun."

  Tun daga wannan rana bata sake sa Isma'il a idanunta ba, zuciyarta takasa hakura da rashinshi, wani sa'in har gidan take zuwa sai dai kowa taga ya daina sakar mata fuska, ga abin takaici shirye-shiryen bikinsu kawai sukeyi ba wanda ya damu da halin da take ciki.




   Isma'il kam shima komai nasa ya canza bai fiya magana ma sosai ba, duk 'yan gidan hatta Samira sun fahimci yanasan Fatima sosai, sai dai yaza'ayi?

  Abdul kam abokansa sai dariya sukemai wai zai auri 'yar kauye, yace " nimafa bawai d'an inzauna da ita d'ind'ind'in nakesan auranta ba, d'an kawai in kauda kwad'ayi nane, dariya suka kwashe dashi sukace " in wannan ne ba kawai sai ka....."
  Shidai kam zuciyarshi batasan wannan kawai....d'in.

  Yau saura kwana 2 biki, d'anginsu Fatima sun cika gida, itakam kallan kowa take a baibai, sai dai ba yanda zatai, duk ta rame ta canza.

  Dad nakawo nan yai shiru tare da kallan Seemah dake zubar da kwalla kamar an bud'e famfo, Ammar ma hawaye ke zubar mai, ya kalli Habib shima haka.

  Yai shiru can yace " Ana saura kwana 2 auranta ne Ammar yazo ina zaune kusa da Samira da ba lafiya ya sanar dani wai matar nan ta gidan nan, tace d'an Allah tanasan ganina a shagon Abban Jafar. "

  Samira dake kwance ba lafiya na kalla, na share maganar tare da kallan matata, Samira ta juyamin baya tana zubar da kwalla, tausayinta dana kaina ya kamani hakan yasa na watsar da maganar Fatima nasan ganina.

   A b'angaren Fatima kam tun karfe 2 tazo gefen shagon take tsaye, har la'asar, Amadu tausayinta ya kamashi yace " Fatima anya zaizo kuwa?"

  Ga mamakinsa murmushi yaga tayi tace " zaizo."

  Anan shagon ta la'asar Amadu yabata biscuit da lemo, duk da yunwar datakeji taki amsa, duk k'iran da Amadu yake makama Isma'il a waya sai ace wayar a kashe, ga magrib ta duso, Jalal ne yazo gunsa, yace " yauwa Jalal zauna ka taya Aunty hira bari naje gidansu Ammar in dawo."



_Dad ya kallesu tare da matse kwallar sa_


  Yace " Seemah bansan meya faru ba, nidai Amadu yazo mukai sallar magrib a massallaci tare muna fitowa yasanar dani komai, da sauri muka nufi shagon ni dashi.

  Sai dai me? Shagon muka gani kamar ba kowa, hakan yasa na shiga ciki da sauri shi kuma ya zagaya, ina shiga na tadda Fatima tsirara ba kaya a kwance, kamar ma ta ruga ta suma, kana ganinta kasan ta karfi aka mata, na matsa da sauri na tallabota idanuna a rufe na riko zaninta na lil'iba mata, Amadu ya leko cikin tsoron abinda ya faru ya zube agun, nikam rungumeta nai na shiga wani irin kuka mai ban tausayi, ban farga ba naji mutane a waje ana hayaniya.

   _Dad ya share kwallarsa_
_Seemah kam kukanta ya tsananta anan_

  Amadu ne ya kallan yace " yi sauri ka fito da ita samarin garin nan ne bansan wa ya k'irasu ba."

  Na d'agota tare da nad'a mata zani, ina fitowa aka fara jifansa da dutse, ganin zasu sameta yasa na juya sukai ta dukana, wani daga cikinsu ma bamusani ba ashe yasa kalanzir kawai sai ashana mukaga an kyasta, haka na d'aureta abayana dakyar mukasha zuwa gida.



   Sai dai me? Bala'in dana tarar a gida a wuce nacan, Hajiya harta suma, Samira ma ciwonta ya tashi, sai numfashi kawai takeyi, tana ganina d'aure da Fatima kawai tayi baya luuuu, abinda ya firgitani agun tace ga garinku nan.

   Kuka ma rahama ne, a wannan ranar hawaye ma kasa zubomin sukai, Kawo da jama'ar gurin suka had'u aka fara zancen yima Samira wanka, nan Kawu ya kalli Amadu a tsakiyar mutane yace " Amadu ka tabbatar da abinda ka fad'a cewar Isma'il shiya mata fyad'e?"

   Da mamaki na kallesu ni kuma? Abinda ban tab'a zataba sai jinai Amadu yace wai eh, ya ganni da idanunsa.

   Kuka sosai kawu yai, kowa ya shiga ala wadai dani, Abdul ya koma gida cikin taron jama'ar biki yace " bazai aure Fatima ba, d'an ankamata da wani a shago."

  Tsinuwa kuka nashata, wani abin takaicin Fatima data farfado, sai kuma ba baki, ta kasa magana, duk yanda taso tai magana ta kasa, anan aka fara jifana akan lalai kafi namata da alama ma abu nasa na danne bakinta, yunk'urin ihun dataitayi yasa muryarta ta tafi.



    Dad ya kallesu hawayensa sun tsanan ta yace ban tab'a ganin bala'i kiri kiri irinta wannan ranar ba, kowa ya gujeni, A lokacin na ba Fatima takarda akan ta rubuta min sunan wanda yamata fyad'e, tana kok'arin rubutamin, Tayi baya luuu, bakinciki harya gama cin jikinta, haka na kaita asibiti aka bata gado, sai dai kamar ba rayayyiya ba, tana kwance ne kawai sai numfashi, d'anginta suka sallamata aka watse da ala tir.

   Fatima na asibiti har wata 2, Kawu da Hajiya sunyi sunyi inrabu da ita sai dai gani nake in na kyaleta mutuwa zatai d'an bakin ciki, alokacin ne kuma akace tanada ciki.

  Ganin zaman garin na neman gagararmu yasa muka dawo Suleja, anan ne har Fatima ta kawo watan haihuwa, tana haihuwa tace ga garinku, Hajiya kam da Kawu sun ma dainamin magana sam, yaya ma duk yanda yaso da in rabu da Fatima sai dai na kasa, haka na zauna agun gawar naita kuka kafin aje amata sitira.


Dad na zuwa nan yakasa magana Seemah kam jitai kanta na juyawa Ammar ya matso kusa da ita yace " Seemah, in ihu ne kiyi amma karki had'iye komai a ranki."

  Kallansa tai kawai tai baya luuuuuu, Habib ma kuka yake sosai, Dad ya mik'e dasauri ya d'auketa yai waje da ita.



  © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

3 comments:

  1. Ibtila'in rayuwa kenan, Allah yasa mu gama Lafiya.
    Amin. Kuma mugode Allah Duk halin da muke ciki don tabbas akwai wadda ninki dubu na halin da muke ganin muna ciki na kunci shine rayuwarsa, misali mutane Syria, Yemen da sauransu.
    Allah kara basira.

    ReplyDelete
  2. Ameen, Allah yasa mu gama da duniya lafiya

    ReplyDelete
  3. Oh!Kai wannan masifa da mai tai kama?oh Allah,ka ji qanmu..

    ReplyDelete