Tuesday, 3 January 2017

JALALUDEEN 33

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 3⃣3⃣

 

Jalal har sun d'anyi nisa sam haji hankalinsa ya kasa kwanciya juyowa yai ya kalli Sagir yace " Sagir please d'an taimaka ka ajiyeni anan, akwai inda nakesan zuwa."

Sagir ya girgiza kai yace " Kai Jalal, baka da lafiya na d'aukama zaka yadda na wuce dakai gidanmu, ina kuma zaka?"

  Jalal yai ajiyar zuciya yace " gidan su Chairman akwai wacce nakesan gani."

Mamaki yasa Sagir yai baki sannan ya juyo cikin namaki yace " ban gane ba?"

Jalal ya juya kai yace " I don't know why but I feel that I must see her."

Sagir ya kalli Jalal yace " jalal me kake nufi da kalamanka? Wazaka gani? Ko ince wa kakesan gani?"

  Jalal yai shiru, sagir yace badai Seemah ba ko? Jalal yace " Sagir bari na sauka nagode sosai."

Dasauri Sagir yace " a'a bandai san meke faruwa ba amma bazan iya barin ka katafi kai kad'ai ba."
Jalal ya kalleshi tare da cewa tnx alot.
Sun fara tafiya kad'an Seemah tak'irashi.

Murmushi ya saki tare da d'agawa, tace " My Deen!"

Jalal yai ajiyar zuciya tare da cewa " kina ina?" Tace gida d'azu muka dawo da ya Ammar.
Yace ganinan zuwa, yanajin karar datai tace " haba? Dagaske? Wayyo naji dad'i, ka kusa isowa?"

Murmushi yai yace " nad'auka zakice mezan zo yi?"

Tace "wa? Ni? Kaima kasan ko kullum zamu had'u bazan ce haka ba."
  Yace " tsokanarki nakeyi bari inzo shaf shaf in ganki."

  Sagir kam tuki yake amma gaba d'aya hankalinsa na kan Jalal meke faruwa? Soyayya suke ko me? Anma anya Seemah ce? Kodai wata ce a gidan?

  Suna isa suka parking a gefen gidan, Jalal na mata flashing kafin wayar ta katse yaga ta fito, kamar irin tana waje tana jiranshi d'in ne.

Kodayake hakan ne d'an suna gama waya taji hankalinta ya kasa kwanciya, gyara fuskarta tai tad'an fesa turare ta sauko, a falo taga farida ta tambayeta Ammar tace ya fita yanzun nan inaji ya tafi, ta fito ta tsaya a waje.

  Sagir ya fita daga motar ya kurama Seemah ido itakam dayake hankalinta baya kanshi bata na kula dashi ba, kawai juyawa tai tana neman Jalal, murmushi Jalal yai sannan ya fito daga motar tare da d'aga mata hannu, murmushi ta saki sannan ta karaso inda yake, Jalal ya kalleta ya saki murmushi itama murmushin tai tace " yau meya sameka? Nemana na ba zata haka?"

Ya kalleta yai ajiyar zuciya yace " meya sameni? Ahhh ni kaina ban sani ba, ko d'an d'azu bamu rabu ta dad'i bane? Kawai nakejin kamar ina tsananin san ganinki."

  Murmushi tai sosai tasa hannu a kirjinta tace " wow naji dad'i sosai for this honour."

  Tad'an rangwab'ar da kai tace " amma kamar numfashinka yana fita da sauri."

  Murmushi yai yace " kawai maybe ko d'an kaina na ciwo ne."

Ai batasan sanda takai hannu goshinsa ba jin zaffin zazzab'i mai karfi yasa ta rik'ice, tace " My Deen ya haka? Meya sameka?."

  Hannunta ya zare daga goshinsa yace " Don't worry ba wani abun bane, bari mu wuce."

  Kallanshi tai idanunta sukai raurau kamar me shirin kuka tace " My Deen kaji jikinka kuwa? Yama za'ai kacemin karna damu?"
Kai ya kwantar a jikin kujera yace " karki damu in nasha magani komai zai dawo normal."

  Sagir kam mutuwar tsaye yai, kawai kallansu yake, basu ankara ba kawai sukaji cikin muryar fad'a sosai ance " Seemah uban me kike anan?"

  Da sauri ta juyo jin muryar Ya Habib, Sagir ma ya juya da sauri, Habib ya maka mata harara cikin zafin rai yace " ba magana nake miki ba?"

Jalal ya fito daga motar tare da kallan Habib yace " Chairman what do you mean by me takeyi anan?"

Habib ya had'e rai sosai wanda yasa cikin Seemah ya d'uri ruwa, ta kalli Jalal sannan ta kalli Habib tace " Yaya Deen bashu da lafiya please kamai a hankali."

  Ran Habib ya kara tuzura yacw yace" kin wuce gida ko kuwa? Me yadaman da abinda ke damunshi?"

  Zatai magana Jalal yace " Sorry Yaya zata shigo amma nan da minti 5."

Habib yace " what?"

Jalal yai murmushi yace " ban fahimci me kake nufi da metake yi anan ba bayan kafi kowa sanin meke tsakanin mu, bana tunanin kana zargin wani abun datake anan da ya wuce ganina."

Habib yace " mene?"

Jalal ya matso kusa dashi yai murmushi yace " yaya ka shiga ciki, yanzu kanwarka zata shigo sallama kawai zamuyi nima sauri nakeyi."

  Habib sai hucci yakeyi ransa ya gama b'aci, lalai ma Jalal d'in nan, meya d'aukeshi?

  Jalal ya juya kusa da Seemah ya rangwab'ar dakai yace " da alama dole muyi sallama yanzu,  naga kamar yayanki jiranki yake."

  Ta kalleshi hawaye suka zubo mata, kai ya girgiza mata yace " banasan kukan nan please. " ta kalli hannunsa tace " agoggonka?" Tai maganar cikin raunaniyar murya, da sauri yasa hannun a aljihu, idannunta suka sake zubar da kwalla, meya sami agoggon mu? Jalal ya kalleta yace " karki damu."

Share hawayen tai tana kallansa, yace ki shiga gida.

  Habib ganin rainin hankalin yafara yawa kawai ya matso tare da fizgar hannun Seemah, tafiya suke da Habib anma kaba d'aya ta juya fuskarya kallan Jalal kawai take tana hawaye, shima shi kad'ai yasan me yakeji.





© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

2 comments:

  1. Bin littafin da kake so kullum kullum fah bai da sauki, a taimaka wa masoya dai, don a rage musu zullumi, da yawan shigowa da fita hannu rabbana.
    Watakila da za a yi wa littafi kudi mai kauri, wadda ba zai iya hakurin bi yau da gobe ba ba tare da damuwa ko Shiga wani yanayi ba, sai ya biya ya karanta, gaskiya ina ganin da an taimaka kuma ya zama nasara kan nasara wa mai littafin da me karatun.
    Da fatan za a duba wannan shawarar.

    ReplyDelete