Wednesday, 11 January 2017

JALALUDEEN 40

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 4⃣0⃣


    Zainab kam tunda ta shiga d'aki hankalinta ya kasa kwanciya, ba shakka wannan wulakancin da aka ma Abba ya k'ona mata rai, bata fiya fishi ba haka take sai dai in ranta ya b'aci bata ganin komai, wayarta ta d'auko ta danna number Jalal, ringing uku Jalal ya d'aga tare da sallama ta amsa sannan tace " Yaya dama akwai lokacin da zaizo har ka fifita soyayya akan iyayenka?"

   Cikin b'acin rai Jalal yace " ke Zainab meke damunki? Ni kike fad'ama wannan banzan zancen?"

  Zainab rai b'ace tace " meye ma bazan fad'ama ba yaya? Akwai abinda yafi b'acin rai irin a wulakanta iyaye? Mahaifinta Har da shake ma Abba wuya? Sannan kai kuma anjima kazo kace kana santa ko me?"

  Jalal ya mik'e tsaye idanunsa suka kad'a sukai jaaa, cikin fad'a yace " me kika ce?" Shiru tai bata amsa ba, tsawa ya daka mata yace "ME KIKA CE?"

   Nan tai ajiyar zuciya ta shiga fad'amai abinda akai a gabanta, cilli naga yayi da wayarsa kan gadon Sagir, dama Sagir baya nan, wani hucci ya shiga saki ni kaina sai dana tsorata alk'alamin dake hannuna sai daya fad'i, tun yana karami ko a wasa bayasan irin zagin nan na yarinta da ake, d'an shi ko kad'an baya san a zagi iyayensa, bari har me?? Shakemai wuya?.
  A zuciye naga ya fito daga d'akin ai da gudu nai gaba nikam kar a huce akaina.....

  Ammar kam tunda Jalal ya tafi yake faman lallab'a Seemah sai dai dakyar ya samu tai bacci, sai dai kamar wata yarinya tana bacci tana ajiyar zuciya, Ammar dake tsugunne saitin fuskarta ya saki murmushin ganin yanda take ajiyar zuciya, a hankali naga fuskarsa ta koma ta damuwa, ya matso da fuskarsa saitinta ya kwantar, ya k'ura mata ido, a hankali ya furta " Seemah wani irin so nake miki?
Na jini ne?
Ko kuwa na 'yan uwa ne?"
    Ko kuma soyayya ce ta d'a namiji?"

  Shiru yai kawai yana kallanta can baisan sanda zuciya ta d'aukeshi ba, a hankali yakai bakinsa kan kuncinta ya sumbata, motsin datai ne yasa ya mik'e tsaye da sauri tare da sa hannu a bakinsa, jiyai d'akin yamai zafi duk da A.C da kuma sanyin da akeyi, bakin window yaje ya tsaya yana firfita da hannunsa.

  ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧

   Habib kam suna isowa Abuja yai asibiti da Hajiya, suna shiga akai emergency da ita dan gaba d'aya bata hayyacinta, kawo duk ya rikice hakama Habib,  dakyar Habib ya lalubo wayarsa ya k'ira Abbansu Zaid sannan ya k'ira Dad, Dad dake hanya jin mahaifiyarsa ba lafiya yasa ya rikice, ya kalli driver yace kara gudu hajiyata ba lafiya, nan ya amsa da to tare da kara gudu.

  Habib na kashe wa ya k'ira Ammar, Ammar yana kallan wayar sai data kusa katsewa ya d'aga ba tare dayace komai ba, Habib yace" Ammar kazo Asibiti Hajiya ba lafiya."

  Da karfi Ammar yace " me ya sami Hajiyar?"

Seemah dake bacci ta bud'e ido, tana kallan Ammar, Habib ya cigaba " bansani ba nima Ammar gata dai a emergency tana jin jiki."

  Ammar yace " *Inalilahi wa ina ilaihi raji'un* bari muzu yanzu." Yana kainan ya katse.

  Juyowa yai ya kalli Seemah dake zaune akan gado, ta kalleshi tace "yaya me ya sami Hajiyar?"

Kai ya girgiza alamar a'a yace "Seemah bansani ba ki tashi dai muje."

  Da sauri ta sauko ta gyara d'ankwalinta ta yafa mayafi suka fita.

  A asibiti kuwa Likitoci sundai yi nasu k'okarin sai dai su kansu sunsan inaaaa, ganin dai ta dawo hayyacinta yasa aka bata d'aki, kawo ya zauna kusa da ita,  ya rik'e mata hannu, yace " Sannu Hajiya!! Bakiji yanda naji ba nad'auka kema mutuwa zakiyi ki barni kamar yanda sauran matan nawa sukai."

  Hajiya tai murmushin karfin hali tace " Isma'il fa?" Kawo yace " yana hanya."

  Habib ne ya shigo shi dasu Abba da mami, da sauri Abba ya karasa kusa da ita,  yace " Hajiya?"

  Ta kakaro murmushi tai tace " D'an nan kaima tasoka akai?"

Sannu hajiya abinda ya fad'a kenan, ta d'aga kai sannan ta kalli Mami dake mata sannu, tace yauwa Allah ya muku albarka, sukace Amin.

  Abba ta kalla zatai magana sallamar su Ammar ta katseta, suka shigo shi da Seemah, Ammar ya kalleta duk ta rame yace " matata ya banje gaidake ba sai in ganki akan gadon asibiti?" Tace " yaushe ka shigo?"

  Murmushi yai sannan ya gaida kawo dasu Abba, Seemah ma ahankali ta gaidasu, sai dai mami ce kawai ta amsa, Ammar ya kalli Abba da kawo yace" wooo yanzu kanwar tawa mai tsada tana gaidaku shine kukai shiru?"

  Kawo ya kalleshi yace " Ammar kana nan dai yanda kake." Hajiya kam tunda Seemah tai gaisuwa ta kafe ta da ido, Abba ganin haka yana tsoron kar ciwonta ya tashi yasa yace " Seemah d'an fita waje, Habib dake tsaye ya kallesu, ba shakka matsalar daga Seemah ne ba Ammar ba.

  Seemah ta d'ago ta kalli Abba,  tsawa ya daka mata yace "bakiji me nace ba,"

  Duk ta rikice tama rasa hanyar fita,  Ammar ne ya jawota jikinsa yace " me kakeyi hakan Abba? Yaza'ai yarinya tazo gaida kakarta ka nemi korarta?"

  Abba yace " Ammar ina wasa dakai ne?"

  Ammar yai ajiyar zuciya yace " yahkuri in na b'atama rai Abba sai dai ba inda Kanwata zataje inkuma anaso ta fita to sai dai ku fita tare."

  Yana kainan ya jata sukai waje.

  Seemah duk ta rikice kawai hawaye takeyi.

Jalal kam a sukwane yaje gidansu Habib sai dai mai gadi ya sanar dashi yanzun nan motar Farida ta fita suna asibiti, hakan yasa da sauri yasa mai machine d'in yabi bayan motar.

  Sun isa asibitin, Farida ta fito da sauri tai ciki, shima ya bita, a harabar gun ya kallo, wata kamar Seemah, hakan yasa ya tsaya yana kallanta, Seemah kam hannun Ammar ta rike kam dan jikinta duk rawa yake, ganin haka yasa Ammar ya jawota jikinta ya rungume, Jalal dake tsaye yaji ransa yayi mugun b'aci, karasa wa yai inda suke Ammar ya d'ago ganin kafar mutum ya kalleshi, da mamaki yace " Jalal? Me kake anan?" Seemah najin sunan tai saurin d'agowa ta kalleshi.


Idanunsa sun kad'a sunyi jaa dama ga bakin cikin abinda aka mai ga kuma wani sabon salo, babban yaya namiji ya kama rungume kanwarsa, Seemah ta kalleshi da idanunta dake hawaye tace " My Deen?"

  Kallanta yai yace " Meemah me kike anan?"

  Ta kalli Ammar sannan ta kalli Jalal, Ammar yace " kai ya kamata kabada wannan amsar, mu tinda ka ganmu anan ai akwai dalili, Jalal yace " Dad nake nema."

  Ammar ya jinjina kai sannan yace " tunda Dad kake nema bayanan." sannan ya kama hannun Seemah zai koma cikin asibitin da ita, da sauri Jalak ya kamo d'ayan hannunta, ta juyo ta kalli Jalal ta lumshe idanunta, Jalal ya sakar mata murmushi sannan ya kalli Ammar yace " sry yayan Seemah inasan magana da ita."
   Wani kishi ne ya kama Ammar ya bugamai wani kallo, Jalal mamaki ya kamashi, ba shakka wannan kallan ba kallan yaya bayasan shi bane kallan kishi ne, amma......Ammar ne ya katseshi da cewa " ka manta me ka mata?"

  Jalal da sauri ya kalli Seemah, meya mata? Nan Seemah ta tuno kalaman Zainab, a hankali tai fara baya, tana kokarin zare hannunta, jisukai ance " *Me kukeyin hakan?*
Da sauri suka juya dukansu, Dad ne a tsaye rai a b'ace.








© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

No comments:

Post a Comment