Sunday, 1 January 2017

JALALUDEEN 31

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

_To you all my fans, wish you happy new year���� May Almighty Allah help us Ameen_

   No. 3⃣1⃣

   Juyawa tai da sauri ta koma office d'in Habib.

  Ammar ne ya tsaya kallan Habib cike da mamaki yace " yaya waye waccan d'in?"

  Habib ya juya baya yace " bakaji abinda Seemah tacemai ba? Shine wanda takeso, bakuma soyayya ta wasa ba harda maganar aure take nufi."

  Dariya Ammar yai yace " haba yaya kamar bakasan kanwata ba? Na sani guy d'in daya fita yana da cikar zati da kirar jikin da maza ke so, amma kanwata bata damu da wannan ba, wanda takeso shine wanda zai kula da ita, wannan kuwa kana ganin yanda yaganta ya wani d'auke kai?"

   Habib ya matso kusa dashi ya rik'e hannayensa  yace " Ammar, Dad fa nacikin tsananin damuwa bansani ba ko shine dalilin ko kuma da wani abun."

  Ammar yace " Dad kuma? Nifa na kasa fahimtar abinda kake nufi? Kanasan kacemin yaran nan shi Seemah keso.................."

  Da karfi sukaji an bud'e kofar, suka juya atare Seemah ce tsaye fuskarta a had'e, ta karaso kusa da Habib ta kalleshi ido cikin ido tace " Yaya mai kawa Deen?"

  Habib ya had'e rai shima yace waye wani Deen?

  Ta kara had'e fuska, tace " Jalal, mekamai?"

Ammar da mamakin abinda yake gani yace " Seemah waye waccan d'in dahar zai sa ki zo ki tsare yayanki da kike girmamawa?"

  Idanta ne ya ciko da kwalla ta kalli Ammar tace " Ya Ammar na rasa dalilin dayasa akemin haka, na d'auka kowa yana da right d'in dazaiso abinda zuciyarsa take so?"

  Ammar kam yama kasa furta wata kalma, haka kawai yaji ransa na b'aci, me yarinyar nan take nufi? Bai ankara ba kawai yaga ta tsugunna tare da rufe kanta da hannu tana kuka, cikin kukan take cewa" Ya Habib please karku rabani da Deen, yanzu gashi ya tafi bansan ya zanyi ba."

  Habib haushi ya kamashi kawai yai waje da sauri duk da yanajin kukan kanwartasa har cikin ransa.

  Yana fita Ammar ya tsaya kawai yana kallanta, Jin idanunsa suna neman kawo ruwa saboda kukan datakeyi yasa ya matso ya zauna shima kusa da ita a hankali ya jawo kanta ya kwantar akan kafad'ar sa.

  Kwanciya tai lamu, ta fara share hawayenta, Ammar cikin sanyin murya yace " Seemah do u love him that much?"
  Kai ta d'aga sannan tace " yaya bansan ya zanyiba yayi fishi dani?"

Ran Ammar yakara b'aci sai dai ya d'aure yace " Seemah kinsan me? Ta girgiza kai, yace" Falling in love is so easy but keeping that love is very difficult., bansan yaushe harkika fara soyayya haka ba, but karki bari soyayya da kikeyi tajawo fad'a tsakaninki da iyayenki da kuma 'yan uwanki."

  D'agowa tai ta kalleshi ta kara share kwallarta, sannan ta kalli idanunsa da kwalla ta taro murmushi ta saki, tace " yaya please please kar ka k'i abinda nakeso, in har kaima kak'i Deen it will make it difficult for me. "

  Murmushi ya kakaro wanda kana ganinshi kasan a iya leb'ensa suke, ta mik'e tace "yaya kataimaken please kaji?"
  Yace name fa?

Tace ka k'ira Jalal a wayarka kacemai yai hakuri duk dabansan me ya Habib ya mai ba.

   Ammar ya kalleta cikin mamakin gaske yace what? Me? Kai ta d'aga cikin halin ko in kula tace " kaine best bro d'in na kaikad'ai nake tunanin zakamin abinda nake so kuma, kaji yaya please? "

  Kallanta yake da mamaki, sai dai haka ya sabar mata bai iya ce mata a'a ba akan duk abinda tace, wayar ya mik'amata tai tsalle tare da ansa tasa number tai dialling.

  Jalal kam yana fita waje yai kawai tafiya yakeyi, zuciyarsa taf take da tunani kala kala, yarasa meya kamaceshi, sai dai abinda yafi bashi takaici kud'in da Habib ya bashi, me ya d'aukeshi? Jin karar waya yasa ya zarota daga aljihu ganin number ne yasa sai data kusan katsewa ya d'aga tare da Sallama, Seemah naji sallamarsa tai saurin mekama Ammar waya, Ammar ya mik'e tare da ansa duk da ransa bayaso, ya amsa tare da cewa "Yayan Seemah ne da muka had'u a office d'in Habib yanzu."

  Ran Jalal ya kara b'aci yace " Wani kud'in kaima zaka kara bani akan in rabu da Seemah ko me?"

  Sai a lokacin Ammar ya gane abinda ya faru, amma saboda bayaso Seemah tagane yace" Hmm da Alama wannan saurayin na kanwata yanada zafin rai."

  Jalal ya kara had'e rai kamar Ammar na ganinshi yace " Ya akai to?"

  Ammar yai ajiyar zuciya tare da kallan Seemah data rik'e hannunsa tana rokonsa, ajiyar zuciya ya sakeyi yace " Kanwatace tace in k'ira in baka hakuri."

  Jalal yace " me kace?"

Ammar ya kara kufula yace " Kanwata ce ta damu da yanda taganka shine takeso naji ko komai lafiya."

  Jalal yace " kana nufin saka tai ka k'irani ko me?"

  Ammar ya had'e rai sai dai yazaiyi? Yace " gata tana san magana dakai." Yana kainan ya mik'ama Seemah wayar yai waje da sauri.

  Seemah na amsa tace " My Deen ka sauko?"

Jalal yace " wannan yayankine?"
Tace " eh special brother na ne." Ya d'an tab'e baki kad'an yace" shine kikasa ya k'irani? Yama za'ai ya biye miki? Kuma ce miki akai in kika k'irani bazan d'auka ba?"

  Turo baki tai tace " menene d'an nasashi yamin abu? Ni duk abinda nace masa inaso yimin yakeyi, sannan yanda naga kayi shine yasa nai tunanin bazaka d'aga ba."

  Murmushi Jalal yai a ransa yace lalai an sangartata dayawa, a fili yace naji, zan k'iraki a wayarki anjima.

Tace zan jiraka fa? Yace eh zan kira.

Sunyi sallama ta kashe wayar tare da sakin murmushi.

Jalal ma yabi wayar da kallo ya saki murmushi.

  Ammar kam yana fita toilet ya shiga yai ta watsama fuskarsa ruwa, kalaman Jalal ke dawomai, mirror d'in toilet d'in ya kalla sannan ya goge fuskarsa ya fito.

  Habib na fita daga office ya nufi gidan Abba, ba yan sun gaisa da Zahra ne ya tambayeta mahaifiyarta, tace " taje Suleja d'azu da safe."
  Habib yace wani abun ya faru ne? Zara ta girgiza kai tace " wlh bansani ba Yaya naga dai da safe Abba ya k'irata tana dawowa tace suleja zata."

  Habib ya d'aga kai sannan yace" Abba fa?"

Tace yana falonsa kaje, Habib ya tura kai b'angaren Abba.

  Yai sallama Abba ya amsa tare da bashi izini, Habib ya shiga, a zaune yaganshi kamar yanda ya saba da jarida a hannunsa, bayan Habib ya shigo ya ninke jaridar tare da kallansa, Habib ya karasa ya zauna a kasa tare da gaidashi.

  Abba ya amsa yace " Habibu daga ina haka?"

Habib ya d'ago yace " Abba wani abu ke damuna." Abba ya kalleshi da mamaki.

  Habb yace " d'azu naje gun Dad na ganshi a wani yanayin da bazan iya fad'a ba, Abba abin nan ya dameni ya hanani sukuni, da farko nai tunanin ko Saurayin da Seemah takeso ne bayaso, amma yanzu kaina ya kulle, bansan menene ba."

  Abba ya gyara zama yace, saurayin da Seemah takeso? Kamar ya? Akwai wanda takeso ne?"

Habib ya d'aga kai yace " eh tasanar mana ni da Dad jiya."

  Abba yai shiru, wato wannan ne dalilin dayasa Dad yake tunanin abubuwa kala kala? Yanzu gashi ganin seemah da Hajiya tai dakuma zuwan Dad dayai yasa ta takwanta d'an ciwonta ya tashi.

  Habib ne ya katseshi yace " Abba ya za'ayi?"

Abba yace " zamuyi magana da Isma'el d'in sai dai inaso kaima inkaje gida ka kwace wayar Seemah ka kuma hanata fita harsai mun gama yanke hukunci da Mahaifinka."


Habib yace " to Abba amma Seemah zata yarda kuwa? Tanasan yaron....."

  Katseshi Abba yai ya mik'e yace " Seemah gwal ce? Kai meyasa kaida mahaifinka halinku yake d'aya ne? In kasan abinda mahaifiyarta taja mana bazaka tab'a bin bayanta ba."

  Habib ya kalleshi da mamaki yace " bangane mahaifiyarta ba? Ba Maman mu bace ta haifeta kake cewa ko me?"

  Sai a lokacin Abba ya tuna, Habib da Jalal da babban d'an Abba Jafar tare suka kaisu karatu tun suna yara yan 15yrs da Habib da Jafar, junaid kuma 12yrs aka kaisu England gun Kanwar mahaifiyar Jafar dake zaune acan, Abba shiya had'asu ya biya musu karatunsu, a lokacin da abin ya faru suna can, Ammar ne kawai a gaban mahaifiyarsa  lokacin yana d'an shekara 5.

  Habib ya sake cewa" Abba bakace komai ba?"

  Juya baya Abba yai yace " wani abune a raina, sam hankali na yana gun, kaje ka aiwatar da abin da nasaka kawai."

  Yana kai nan ya juya yai d'aki, Habib ya bishi da kallon mamaki, me Abba yake nufi? Daga yanda Abba yai maganar yama za'ai ya yarda wai badashi yake ba? Shidai a iya saninsa Seemah mahaifiyarsu tana haifarta tabar duniyar, wannan shine abinda suka sani kuma dashi suka taso, to amma me Abba yake nufi da kalamansa..........?

 

❓❔❓❔❓❔❓❔da alamar tambaya......injini��

© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*



��‍♀

1 comment: