����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣6⃣
Zahra ta taimaka mata tasaka kaya, hannunta ta kama suka fito falo.
A falo kuwa Dad na zaune a saman kujera yayi shiru zuciyarshi na cikin damuwa, mami na zaune daga can b'angaren itama, Habib kuma da Ammar suna zaune a kasa, Zahra ce ta fito rik'e da hannun Seemah ta zaunar da ita a kasa kusa da Dad, hannu Dad yasa ya shafi kanta.
Kamar ba Seemah ba sam ta canza ga lab'anta duk sun bushi gwanin tausayi, Ammar ma ya kalleta tausayinta na k'ara ratsa gab'obin jikinsa.
Dad ne ya d'aure yai gyaran murya.
*TUNA BAYA*
Malam Isma'il wato Dad kenan, ya kasance malamin makarantar boko ne, a garin Birnin/gwari dake kaduna, yana zaune a jikin gidan mahaifinsa ne saboda rashin hali, gashi anyi sa'a dama gidan kawo gida ne babba, kawo matansa 3 ne, sai dai duk Allah bai basu haihuwa ba sai akan mahaifiyarsu Isma'il.
Hajiya 'yaranta biyu wato Dad da Abba (Abubakar) anyi sa'a Abba tun yana saurayi ya samu wani babban mutum d'an kasuwa a garinsu yake d'aukansa suna yawan kasuwancinsu tare, ganin kwazo dasan aiki irin na Abba yasa ya aura masa 'yar sa wato Mamie(Bilkisu) sannan ya d'aurashi akan harkokin business d'insa dake Abuja, tun daga nan ya koma can da zama.
Dad an masa auren zumunci da mahaifiyarsu Habib wato Samira, duk da baso yakeyi ba sai dai a lokacin bashida wacce yake so kuma zab'in iyayensa shine zab'insa, bayan auransu ne Kawo ya basu b'angare d'aya suka zauna a gidan.
A kwana a tashi har Samira ta haifi d'anta Habib, sannan ta sake haihuwar Junaid sai dai akwai ra ta a tsakaninsu, lokacin da Samira take da cikin Ammar ne ranar Isma'il ya dawo daga makaranta yaga wata bus tayi parking a mak'otansu, yarane 'yan mata su 4 suka fito daga motar, kana kallansu kasan fulanuwa ne aka kawo su irin aikin nan na aikatau.
Isma'il ya kauda kansa tare da wucewa gidansu, yaje daidai zai shiga yaji ance " Malam Isma'il?" Juyowa yai da fara'arsa saboda ya gane muryar, ya kalleshi yace " Amadu kaine yau a gidan namu?"
Wanda ya k'ira da Amadun yai murmushi tare da cewa" wucewa nazo yi shine naga kamar ana sauke 'yan aiki na d'auka kaine ka d'aukarma Samira." Yai maganar cikin zolaya.
Isma'il ya d'an kallesu caraf suka had'a ido da d'aya daga cikinsu, d'auke kai yai yace " lalai kai dai yakamata ka d'aukarma matarka."
Sun dad'e suna hirarsu har 'yan matan suka gama shiga da kayansu suma suka shiga, Isma'il ya kalli Amadu yace " ni dama shagon ka naje na amso ma Samira kayan shayi, naga kamar wannan cikin na wahalar da ita sosai bata iya cin abinci."
Amadu yace " Hmm nima haka nake fama da Hauwa'u inata so in tambayeka dama haka masu ciki suke shan wahala."
Isma'il ya maida jakarsa d'aya hannun yace " A'a wlh yanayi ne dai yake zuwa kaga Samira data haifi Habibu da Junaid ai duk batasha wahalar laulayin nan ba."
Amadu ya gyad'a kai yace " muje shagon in baka da har na kulli zance ganin Hauwa anma saboda kai zan koma."
Suna tafe suna hirarsu har suka isa Babban Shagon Amadu ya shiga ciki ya had'omai kayan shayi, Isma'il ya bashi rabin kud'in yace sauran sai karshen wata.
Haka Isma'il ya taho yan tafe ana gaidashi saboda ganin girmansa da mutane keyi, har ya isa gida.
Yanzun ma yazo shiga ya k'ara ganin 'yan matan sun fito sai dai ta d'azun nan tana matsar kwalla da alama kukan rabuwa sukeyi, wucewa yai ya shiga gida.
A kwance ya tadda Samira ta kasa komai, nan ya taimaka ya had'a mata shayi ta sha, da kanshi ya shiga gyara d'akin sannan ya taimaka mata ta kwanta a kan gado.
Ganin lokacin shiga makarantar su Habib da Junaid yayi ga kuma babban d'an Abba yasa Mamie ta ba Abba shawara akan akaisu England gun kanwarta, Abba yayi farincikin wannan shawarar ya k'ira kaninsa ya sanar dashi.
Ba Dad ba hatta matan gidan sun tayasu murna, su Habib sai murna sukeyi sukam, bayan sati biyu da maganar Dad dakanshi yakaisu Abuja suka wuce ta can.
Dad ya dawo daga Abuja a gajiye ya shiga gida anan ya tadda Samira ba lafiya su Hajiya da ragowar matan kawo na kanta, ya kallesu yace "Hajiya lafiya dai ko?" Hajiya tace " fita waje nak'uda ce."
Dad ya kalli Samira yaga yanda takeshan wahala yace " Kodai akaita asibiti?"
Hajiya tace " bakaji me nace ba?"
Jiki a sanyaye Dad ya fita ya zauna akan dakalin gidan, bai dad'e da zama ba sai gata ta dawo daga kai nik'a, a hankali cikin sanyin muryarta yaji tace " Ina wuni?"
D'agowa Dad yai ya kalleta ranar daya fara ganinta kaya daban daban ne a jikinta gashi tayi zanen baki duk a fuskarta yanzu kuwa ba wannan shirman a fuskarta sannan kayanta tsaf,ba shakka tanada kyau sosai.
Dad yace " ina gajiya."
Yana fad'ar haka ya kauda kai, matsowa tai kusa dashi tace " Malam menene? Naga kamar kana cikin damuwa."
Kalanta yai da mamaki, baisan sanda yai murmushi ba yace " Ta ya akai kika sani?"
Ta saki murmushi itama tace " kullum ina ganinka ai in na fito anma ba haka nake ganinka ba."
Dad yai murmushi yace "a ina kike ganina?"
Tai kasa dakai batace komai ba, yace " kije kikai aikenki kar a miki fad'a."
Ta d'ago ta kalleshi sannan tace to, wucewa tai ta shiga gida, ya bita da kallo haka kawai yaji damuwarsa ta ragu sosai, anma ya akai yarinya karama da bata wuce shekara 18 ba tagane yana cikin damuwa?
Yarinyar tana shiga gida ta kai markad'an sannan ta kalli matar gidan tace " Hajiya in d'an fita?"
Ta kalleta tace " Fatima ina zaki ke kuma? Naga yamma tayi."
Tace " yanzun nan zan dawo."
To sai kin dawo ta fad'a, da sauri Fatima ta juya ta fita, sai dai abin haushi tana zuwa taga ba kowa agun, waige waige ta fara yi sai dai bata ganshi ba, jitai anzo daidai kunenta ance " Fatima me kikeyi anan?"
Da sauri ta juya ta kalleshi, d'an gidan da take aiki ne ko ince d'an lele, da sauri ta matsa ya kalleta sannan ya kalli abokansa jitai sun kwashe da dariya, kifkif da ido tai tace " menene?"
D'an lelen wato Abdul yace " Abokaina kesan ganinki nace musu ankawo mana kyakyawar mai aiki shine nakeso su ganki ko zasu kyasa kamar yanda na kyasa."
Kallansa tai da mamakin kalamansa tace " mene?"
Dariya suka kara kwashe mata dashi, kana ganinsu kaga tantirai, Fatima kam ba abinda ta tsana irin Abdul ya shigo gida ya d'inga nanik'e mata kenan ita kuma batasan haka.
Cikin takaicin abin yasa tai saurin shigewa gidansu Isma'il.
© *THE SEEEMAH'S LOVE TEAM*
��♀
An zo wajen.... Tnx
ReplyDelete