Monday, 10 July 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 36

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

*Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku Haske Writers Association*

*©na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

{ *36*}

   Little ta kai bakin gate wayarta ta fara kuka, Nafi ta zaro wayar daga cikin jakarta ganin Sunan Big Bro yasa Nafi tai saurin mika mata, Little ta amsa tare da gaidashi.

   Nafi duk ta tattara hankalinta kan Little tanasan taji me yake cewa sai dai batajin komai sai amsar da Little ta bashi "Yaya har mun fito fa?" tai maganar tare da had'e fuska, Nafi sai ji tai tace " Yaya dan Allah ka....." da alama katseta akai wanda ta karasa maganar da cewa " To Yaya."

   Tana kashewa ta kashe motar tare da kallan Nafi ranta duk a b'ace, Nafi ta kalleta tace " ya akai?"

   Little tace " wai Yaya ne yace kije ki gyaramai b'angarensa."
Nafi ta kalli Little da mamaki tace " Ni kuma?"
Little ta d'aga kai alamar eh, Nafi ta canza fuska sannan tace " Matarsa fa? Ita bata iya gyaran bane ko me yake nufi?"

  Little tai karamin tsaki tace " wannan uwar san jikin me zatayi? Banda chatting."

  Nafi ta d'aure fuskarta tamau sannan tace " Mu tafi kinji?"

  Little ta kalleta cikin mamaki tace " Me kike nufi?"
" Mu tafi inda zamu."
Little kam tayi mamakin Nafi dan bata taba tunanin zata iya ture maganar Ya Ashraf ba ganin yanda take girmama shi.

   Little ta kalleta tace " Feena....!"
Nafi tai murmushi tace " Mu tafi kinji, wato matarsa bazata gyara musu muhallinsu ba shine ni zanje in gyara musu, sannan ba kunya su shiga suna farin ciki, sannan gobe ma aa kara kirana in gyara, to ba da ni ba."

   Little ta jinjina kai alamar ta gamsu da zancen Nafi sai dai tana jiye mata b'acin ran Ashraf, iya kuluwa Nafi ta kulu wato ita da bai damu da ita ba shine yake neman sata gyara musu b'angaren su a lokacin da suke shirin fita, ta d'anyi kwafa kadan a ranta tace " ni d'azu kamar zan zauce jin wani abu zai sameshi ni kuma wato wannan ne sakayyar da zaimin.

  Bata sake magana ba har suka ita gidan su Yusra sai dai kana kallanta kasan ranta a b'ace yake.

   A bakin gate Al_Amin wanda ke zaune yana ganinsu ya saki wata fara'a tare da mikewa ya nufo su, sam Nafi bata kula ma da shi ba, har ya iso inda suke Little ta mai murmushi sannan suka kalli Nafi wanda sam hankalinta baya gunsu sai ma ci gaba da tafiya da takeyi.
Hannu Little tasa ta rikota wanda hakan ne yasa Nafi ta juyo ta kalleta, ganin Alamin a tsaye yasa ta mai kallan mamaki.
  Rausayar da kai yai cikin salon soyayyarsa yace " I am disappionted Feena."
Nafi ta kakaro murmushi sannan tace " Sry wlh ban kula ba, sam hankalina na wani gurin."

  Ya d'an shagwab'e kadan yace " in har damuwarki ba akan wani namiji bane na hakura in kuma har akan namiji ne ba ni ba banaji zan hakura."

  Little ta saketa tai gaba ta barsu ganin Alamin ba kunya agabanta yake wannan sakalcin.
  Nafi ta juya kai gefe sannan tace " just 4get, ya kaje gida jiya?"

  Alamin ya kura mata idanunsa wanda ya kashesu kai kace a haka idanunsa suke, Jitai bazata iya kallansa ba hakan yasa tai kasa da kanta, ya kara matsowa sannan yace " Feena jiya na baki waya amma sam ko kunnata ma bakiyi ba, sannan yanzu kin wuceni ko kallona bakiyi ba, Feena please kar ki wahalar da zuciyar dake tsananin kaunarki."

  Nafi ta d'ago jiki a sanyaye, ganin yanda har yanzu kallan nan yake mata yasa tad'an kalli gefe sannan tace " Ba haka bane, jiya bayan na shiga gida bacci nai da wuri, yau kuma sam ban ganka ba."

  Alamin yai kasa dakai sannan yace " Ko dai....."
  Katseshi tai da cewa " Alamin me yasa kake da yawan complain ne? Na fada ma uzuri na why not kai believe da abinda nacema meyas kake neman tursasani akan fadar abinda na shine ba?"

  Tana kai nan ta juya ta nufi hanyar da zata sada ta da ciki, da sauri Alamin yasha gabanta tare da rike kunnuwansa biyu yace " Sry Feenah please!!"

  Nafi ta kalleshi bata cemai komai ba sai kokarin canza hanya tai gaba da takeyi, bai san sanda ya riko hannunta ba, Nafi ta watsa mai wani mugun kallo sannan ta fizge hannunta tai gaba.

  Kai ya dafe cikin tsananin tsoron abinda ya aikata, me zata d'aukeshi?

  Nafi tana shiga ciki aka nuna mata d'akin da su Little suke nan ta shiga ta taddasu ana ta hira, duk yanda sukaso su jata da hira taki aminta a karshe ma kwanciya tai batasan sanda bacci yai gaba da ita ba.

  Can cikin bacci taji Little na tashin ta, ta bud'e ido a hankali, Little ta kalleta tace " Feena ya zamuyi?"
Nafi ta mata kallan da me fa?
Little tace " Ran Yaya ya b'aci yana waje yana jiranki."

Idanu ta zaro gabanta ya yanke ya fad'i ta mike zaune da sauri tace " Da gaske?"
Little tace " wlh, yace ki fita yanzun nan, in kuwa kika bari ya shigo sai ranki ya b'aci."

  Nafi ta mike tare da d'aukan mayafinta tai waje.
Little tace " inzo muje?"
Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a sannan tai gaba.

  Nafi tana fita ta shiga neman motarsa dan itakam bata ganta ba, horn taji an mata wanda yasa ta juya ta kalli inda taji horn d'in, nan ta karasa gun jikinta duk ya mutu ga bacci ga tsoron me zai biyo baya, tana zuwa jikin motar ya zuge glass d'in motar sannan ya mata alama da hannu akan ta shiga.

   Nafi ta bud'e motar ta shiga tare da rufe kofar.
Bai mata magana ba sai jan motar da yai, sai da sukai nisa ya juyo ya kalleta rai a b'ace yace " wato ni ban isa dake ba ko? Maganar saurayin ki ta fi tawa ko?"

  Cikin mamaki ta kalleshi ta daure tace " ban gane ba."

  Wani irin burki dayaja sai da numfashinta yai gaba na wucin gadi.
Nafi a tsorace ta kalleshi, ransa a b'ace yace " ban bada sallahu ki gyaramin part d'ina ba?"

  Nafi ta kalleshi tace " ka fada amma gani nai ni meye nawa na shiga part din mai mata?"

  Ashraf mamaki ya kamashi yaushe 'yar nan tai baki haka?
Yace " to ita kinsan ba 'yar wahala bace dan nace ki taimaka mata shine zaki tafi gidan saurayinki?"

  Wani mugun kishi ne ya taso ma Nafi, ita ba 'yar wahala bace?"
Kallan mamaki take mai, yacigaba da cewa " sannan ke harkin isa in saki abu ki kama hanya kiyi tafiyar ki??"

   Nafi batasan sanda ta saki wani murmushin takaici ba, ta goge kwaIlar data taho mata, tace " Yaya ba sai ka fadamin magana akan matarka ba, nafi kowa sanin ita ba 'yar wahaka bace, ni da ka d'aukoni daga riga mai shan madara da nono kullum, mai kiwon dabobbi nice 'yar wahala."

  Jikinsa ne yai sanyi, a zahiri shi gidan saurayin ne bayasan taje ya kuma rasa dalilinsa na rashin san hakan, shi yasa yasata aiki bawai wulakantata yakesanyi ba.

  Nafi ta share kwallarta sannan ta cigaba da cewa " Yaya ka maidani garinmu inda nake, na fi kowa sanin banda matsayi a gunka dama sauran mutanen gidan, Little ce kadai mai sona dama can ni haka Allah ya halliceni da bakin jini, ubana ma ba sona yake ba, uwata ta d'auki kanina ta tafi dashi ni da bataso ta barni a riga, ban taba samun wani wanda yake sona tsakani da Allah ba in har ka cire little, gwara ka..........

   Jitai an jawota an rungume ta, kalamanta ne suka tsaya cak, bama su kadai ba duk wata gaba ta jikinta jitai ta daina aiki, shi kanshi sai daya rungumeta hankalinshi ya dawo jikinsa, me ya aikata? Sai dai ya kasa zare jikinsa..........

*THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment