Tuesday, 25 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 55

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *Someone!!!*
      *Somewhere!!!*
        *Is Made For U*

  {55}

   Sun yi nisa sosai, Ashraf ya saketa a hankali, da sauri ya shiga d'akinsa, itakam kafafunta ta had'e dan jitai har su rawa suke, tun da take bata taba jin abinda taji yau ba, wani irin feeling ne wannan???"

  Ashraf kam kwanciya yai rufda ciki akan gado, wata muguwar sha'awa ce take tasomai sai dai bazai taba kusantarta ba har sai ta aminta dashi a matsayin miji, juyi ya shiga yi.

  Nafi kam ta dade itama a zaune kafin tabi kofar d'akinsa da kallo, ya kamata ta tafi kafin dari yayi sosai, a hankali ta mike tai d'akin.

   Sallama tai jin shiru yasa ta murd'a kofar d'akin, Ashraf najin haka yai saurin rufe idanunsa, kallansa tai a hankali ta tako tazo inda yake.

  Zama tai a gefensa takai hannu kan sumar kansa, ta kurama fuskarsa ido, a hankali tace "bacci?"

  Jin shiru yasa tad'an turo baki tace "shine ka barni a zaune kai ka taho ka kwanta?"

   Shiru tai tare da cigaba da kallansa a hankali takwantar da kanta saitin fuskarsa suka zama fuskokinsu na fuskantar juna, ta sa hannu a kan kuncinsa sannan tace " please let me be the first person whom you can trust."


   Murmushi tai sannan ta kai bakinta a hankali kan leb'ensa ta sumbata, sannan tace "Goodnight."

  Ta mike tare da jamai bargo tai waje, b'angarensu ta nufa a zaune taga little a falo ta matso da sauri zata mata magana taga Little ta mike tayi ciki, Nafi tabi bayanta.

  Toilet ta wuce direct dan da alama tanajin jikinta ba yanda yake ba, a gun tsarki ta gano lalai abinda ya zubo na sha'awa ne, nan ta wanke wandon ta ta gyara jikinta tasa wani sannan ta fito.

  A kwance taga Little ta kalleta tace "Little yanzu haka zamuyi ta zama bakya kulani?"

  Little bata tanka taba, Nafi tace " ban taba tunanin zaki iya kin kulani ba saboda kinji ance ni yar kauye matar yayanki bace, ni kaina nasan ban kai wannan matsayin ba, sai dai........"

  Little ce ta katseta da cewa " kin dauka saboda matsayinki a gun yaya nake miki haka?"

  Nafi ta kalleta tace "to menene in ba shiba?"

  Little ta mike zaune tace " shekararmu nawa tare?nikenan da miki zancen saurayi akan ki kula wane ki kula wane, bansani ba ashe mahaukaciya kika mai dani."

  Nafi cikin mamaki tace "mahaukaciya kuma?"

  Cikin zafi Little tace "mahaukaciya mana, inba haka ba da igiyar auran yayana a gunki amma nake neman had'aki da wani?"

  Nafi ta matso tare da rike hannun Little tace "Little kiyi hakuri wlh ni kaina mantawa nake akwai abu a tsakanin mu."

  Nan dai Nafi tai ta bata baki har ta hakura, sun dan yi hira kadan kafin Nafi ta kalli Little tace " nikam Little wani abu na damuna."

Kallan mamaki Little ta mata tace name kenan?"

Nafi tai shiru can tace " Abban Ashraf na ga shine ya fara zancen had'in auren Yaya da Ya Nisa, to menene dalilinsa na ajiye wasiya yace a ba matar Ashraf ta farko bayan yasan ko ince Yaya Nisa yakesan ya fara aura?"

  Shiru Little tai can ta girgiza kai tace "ban sani ba, ni banma taba kawo abin a raina ba, amma kina ganin da wani abun ne?"

  Kai Nafi ta girgiza tace "ba komai, bari nai sallah."

  Ta mike tana tunani tabbas da wani abun, sai dai menene?????

*************

A b'angaren Ashraf kuwa tana fita yabi bayanta da kallo yanaji kamar ya jawota ya rungumeta sai dai ina bazai iya hakan ba, bayan yayi sallah ya d'aga katifarsa ya d'auko wani karamin makulli sannan ya zugi wardrobe dinsa ya ture kayan, nan wata yar karamar kofa ta bayana, nan yasa makuli ya bud'e ya zaro wasu takardu a ciki sannan ya koma ya kulle kofar d'akinsa da makulli ya zauna tare da baje takardun nan, bayan ya gama bincikensa da 'yan rubuce rubucensa ya maida ya rufe sannan ya juye fuskarnan a murtuke kamar mai tafiya yaki yace " Mu zuba mu gani."

  Kan gado ya kwanta ya sa diary d'in mahaifinsa, wani shafi ya bud'e an rubuta _Someone! Somewhere is made for u my dearest son_"

  Murmushi yai da ya tuna abinda nafi tace da kiss din data mai, hannu yakai kan leb'ensa yace " yarinyar nan kamar ba ruwanta ashe itama killer?"

  A haka har bacci yai gaba dashi.

  Da safe ya tashi tare da sawa a kiramai dan litti, sunyi breakfast kafin Ashraf ya kalli Dan litti yace "yanzu me kakeyi?"

" Achaba."

  Ashraf ya jinjina kai yace "mota fa ka iya?"

  Dan litti ya d'aga mai gira yace "ka sanni ai akwai karambani ai zamana a kachako sai da na koya."

  Ashraf yace "gaskiya nafa sanka."
Dariya sukai kafin Ashraf yace " zaka koma kauyene?"

  Da sauri yace "a ina?ai ni yanzu i am big for them."

  Ashraf ya sa dariya yace "u are big?wato baka daina bako?"

  Ashraf ya mai alamun zip a bakinsa yace "na daina kai kawai nake san ma."

  Ashraf yace "to in ba matsala nafisan ka zama driver d'ina, saboda nafisan wanda zan yarda da shi."

  Zaro ido dan litti yai yace " Ashaf kana kasheni in nazama driver dinka ai na zama dan gomna."

 
  Dariya sosai Ashraf yai yace " whoa! Dan litti kai kadai ke sani dariya akai akai."

  Dam litti ya mike tare da yima Ashraf salute yace "yes sir!"
Ashraf yai murmushi yace " kaii ban taba ganin mutum irinka ba."

Dan litti ya zauna yace "Ashaf karka damu zan zama mutum mai rike ma amana, dama tunda muka hadu nake sanka bazan taba bari wani abu ya cuceka ba."

Ashraf yai murmushi sannan ya dafashi yace "thanks, amma kanaso kacemin wai baka iya fadar Ashraf bane ko ya?"

  Dan litti yai dariya yace "in na cema Ashraf ai mantawa zakai nine d'an littin gayu."

  Dariya suka sakeyi kafin su mike su fita.

  Makullin motarsa yaba Dan litti shikuma ya wuce b'angaren kawu.

  A tsaye ya ganshi shima zai fito, mumy na kusa dashi, wani takaici ya kara kamashi ya matso kusa da kawu ya gaisheshi fuska dauke da murmushi sannan ya gaida mumy.

  Bayan sun amsa ne kawu yace "Ashraf ya akai?"

Kallan mumy yai yace "magana nakeso muyi."

Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tai waje, ya matso kusa da kawu fuskarnan a sake yace "naji shiru ne, jiya banga takardar appointment ba."

  Kawu ya kalleshi yace "wai da gaske kake?kasan fa matsayin Asim ne ya kakeso inyi."

  Wani murmushin rainin hankali yai tare da jinjina kai yace "ahhhh! Na manta ko da yake ba matsala ka barshi a matsayinsa kai sai ka bani naka, dama ai can nawa ne ko ba haka ba???"

  Ya fada yana kallan kawu.

  Kawu ya shiga hucci, Ashraf yai murmushi sannan ya dan girgiza d'an yatsansa yace "No no no, kawu how can u get angry? Bayan a sama kaga komai?wanda ya sha wahalar yana karkashin kasa?"
  Kawu ya kalleshi sannan yai yake yace "ce maka akai raina ya b'aci?" 

  Ashraf ya d'an kanne idanuwansa yace " why?kunya kake na gano hakan? Hmm ko da yake ba matsala yi zamanka a kujerarka nizansa ka sauka da kanka in har baka ajiye da hannunka ba."
Yana kai nan yai waje,yana fita kawu ya shiga hucci, jakarsa ya cillar can gefe sannan ya zauna a kujera yana maida numfashi kamar wanda yai gudu......

  Ashraf ya fitowa ya harari d'akin sannan ya juya, jiyai ance "Ya Ashraf."

Juyowa yai ya kalli Anisa wace duk ta dan fada a kwana biyu, ya matso yace" ya akai?"

  Kallansa tai tace " yaushe zaka zo ka maidani b'angare na?"

  Kafada ya d'aga yace "da nina kawoki nan?"

  Kallansa tai tace "yaya ni bazan koma bane harsai ka saki wannan yar kauyen dan pride dina bazai bari in iya kallanta ba, kace ta koma kauyensu."

  Hannu yasa ya dafata yace " a maysayinki na wa kenan?"

Tace "yaya!"
Yai murmushi yace " karki damu kiyi ta zamanki a gun mahaifiyarki gani nake zatafijin dadin hakan, nima kuma zan samu saukin bincike min d'aki da akemin."

Yana kainan yai gaba, kallo ta bishi dashi yasan komai meyasa bai taba magana ba????

  Mota ya wuce, dan litti ya bud'e mai baya nan ya shiga ya rufe shikuma ya shiga mazaunin driver.

 

  *#ASHRAFEENAH TEAM*

👩🏻‍✈

2 comments:

  1. Salam sis, kwana 2 mun ji ki shuru Allah yasa dai lafiya. Muna godiya sosai, Allah ya kara basira.

    ReplyDelete
  2. slm dan ALLAH idan akwai pdf complete na wannan lttfin a taimakeni dashi,,,a gskiya bana karatun irin wdannan lttfan amma na fahimci wannan shi na daban ne,,,ALLAH ya kara miki basira,,,nagode

    ReplyDelete