Thursday, 27 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 56

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *56*

 
    Ashraf yacema dan litti akan su tsaya a wani babban shago na wayoyi, nan suka fita tare.

   Waya ya d'auka kirar Samsung S7+ karamar ta hannunsa, sannan ya kalli Dan litti yace"kaifa wanne kakeso?"

  Kai Dan litti ya sosa, Ashraf yace "shikenan in ba ka so."
Da sauri yace " ni kowacce ma ina so."

Ashraf yai murmushi yace "a d'auko mai Iphone 5."

  Wani ihu da dan litti ya sake sai dayasa mai wayar ya kwashe da dariya, nan suka sai sim sannan ya kara siyan wani extra sim sannan suka fito.

  Suna shiga mota ya d'auko wata yar karamar waya daga cikin jakarsa, yasa wannan d'ayan sim d'in a ciki sannan ya maidata jakar.


  Sun isa gun aiki Ashraf ya fito d'an litti yabi bayansa, Asim ne wanda yake tsaye yake jiran isowar Ashraf ya taso da sauri, ya taho gun Ashraf fuskarnan a had'e.

  Dan karamin tsaki Ashraf yaja a ransa yace "The fool is here."

  Asim na karasowa ya kalli Ashraf yace " Kai bakaji kashedena ba ko? Akan kaba yarinyar nan takardarta ta bar gidan nan ba ko?"

  Dan litti ya matso yace " Malam meye hakan?"

Murmushi Ashraf yai yace " barshi magana zamuyi."

Nan Dan litti ya matsa tare da had'e fuska kamar irin shi akama abun nan.

Kallo Ashraf ya maida kan Asim yace " Mahaifinka yace zai bani matsayinka, mai kake tunani?"

  Idanu Asim ya zaro tare da kumburo baki yace "matsayina? What do u mean?"

  Ashraf ya dafashi yace " what do i mean? Da alama sai ka tambayi mahaifinka da ya dage akan bani matsayinka, mayb kuma ya kula ne u are useless."

  Yana kaiwa nan yai gaba, Dan litti yabi bayansa rike da jakarsa yana hararar Asim.

  Ashraf ya kalleshi yace " Dan litti kasan kanin mahaifina?"

Kai ya girgiza alamar a'a yace "jiya dai na ganshi sai dai banaji zan iya gane shi."

  Ashraf yace "zan nuna maka shi inaso ka dinga kulamin dashi akan abubuwan da yakeyi da kuma wadanda yake gani, sai dai karka bari kowa ya ganka kar kuma asan abinda kakeyi."

  Dan litti ya mai salute da hannunsa yace "yes sir."

Hannunsa Ashraf ya ture yace " sorry ba a military muke ba."

   Nan sukai dariya sannan suka shiga.
Jakarsa Ashraf ya kaimai sannan ya juyo ya fita.

Asim kam yana gama magana da Ashraf yai office dinsa kamar zai fadi saboda sauri, yana zuwa ya ture takardun kan desk dinsa da hannayensa biyu, ciki hucci yace " ni zakama haka Abba?"

  Kawu kam yana zuwa office yasa aka rubuta takardar ragema Asim matsayi aka aika mai.

  Asim yai shiru yana kallan takardar, can cikin takaici ya yaga takardar sannan ya mike cikin fishi yai office d'in kawu.

  A zaune ya ganshi shi da  manager  suna magana, nan ya tsaya suka gama, manager din ya fita sannan ya shiga.

  Tsayawa yai a kan mahaifinsa yace "ban yarda da ragemin matsayin nan ba."

  Kawu yace " kasan complain din da ake kawomin naka kuwa?in ban rage ma matsayi ba mai kake tunani mutane zasu daukeni?"

  Mamaki ya kama Asim yace " wa zaka ba matsayina? Ashraf?"

Kawu ya juya kai yace " haka shareholders da director's suka yanke."

Dariya Asim yasa yace " ko kuma ka tsara ba?"
Kawu ya had'e rai yace "kai ni kake fadama haka?"

Asim cikin hucci yace " ni dai na fada kar a kuskura a ragemin matsayina in ba haka ba zan iya tona abubuwan da na sani."

  Mikewa kawu yai tare da dukan desk dinsa da hannu yace " me zaka tona?"
Yai dariya yace "abubuwan da kai, kana tunanin in Ashraf yaji zai barka?wato yanzu tunda kaga Anisa batada matsayi a gunsa shine kake neman juya mana baya ka koma gunsa ko?"

  Kawu a zuciye ya d'aga hannu ya kai mai mari, Kallansa Asim yai sannan yai waje rai a b'ace."

  Kawu ya bi bayansa da kallo sannan ya zauna tare da rike kansa.

  Asim sama yahau cikin takaici yahau hucci tare da kara, ko aure bai taba kawowa ba saboda yanasan ya gaji Company din nan, shine yanzu mahaifinsa zai fara juyamai baya??"

   ************

  Nafi kam bayan ta gama aikin gyara musu d'aki ta zauna tare da daukan qur'ani tana karatu.

   Mumy ce ta aiko a kirata, nan ta mike gabanta na faduwa tai waje.

  B'angaren Mumy ta nufa ta zauna tare da zama a kasa.

  Mumy ta kalleta tace " jiya ina kika je?"

  Nafi kanta na kasa tace " Gidan wata kawata da mukai makaranta."

  Mumy ta kalleta tace " ina sanki a natsayinki na yarinyar da aka taimaka amma ba wai a matsayinki na matar Ashraf ba."

Nafi ta d'ago a hankali ta kalli Mumy.

  Mumy ta cigaba "Ashraf bai samu kulawa daga gareni ba sai bakin ciki dana dinga kunsa mai, mahaifinsa ya rasu hankali bai gama shigarsa ba."

Idanun Nafi suka ciciko, Mumy tace " sai dai hakan ba yana nufin zan yarda ya auri mara ilimi ba alhalin aiki babba yana gabansa, yana bukatar matar datasan gari sannam takeda ilimi at least degree, shine wanda zai gaji mahaifinsa."

   Nafi tai kasa da kai hawaye suka zubo mata, Mumy tace " kije kiyi tunani in har kina san Ashraf to kiyi tunanin menene abinda zaifi amfanarsa a rayuwar nan."

  Nafi ta mike a hankali tana share hawayenta, b'angarensu ta nufa, da gudu mai gadi ya karaso yace " yallabai yace wai ki mai abincin rana zai dawo da anyi la'asar."

  Kai ta d'aga sannan ta koma ciki.

Ana azahar ta fito tai kitchen ta fara mai girke girken Asabe na tayata.

   *********

  Umma da Anisa kam suna zaune abin duniya ya damesu, Anisa can ta nisa tace " duk laifinku ne Umma, meyasa kuka hanani haihuwa dashi?"

  Umma tace "mene?"

  Anisa ta cigaba" da yanzu akwai zuri'a a tsakaninmu ko baya sona ai nasan halin Ashraf bazai wulakantani ba."

  Umma ta mike tsaye tace " Anisa meke damunki?"

  Anisa cikin dan fada tace " wlh ni duk ku kuka cuceni, da ace na haihu dashi ai da d'ana shine zai zama yanada gadon dukiyar Ashraf amma dayake ba ni kukeso na gaji dukiyar ba shi yasa ba wanda yai wannan tunanin."

  Tana gama fadar haka ta mike tai cikin d'aki tare da bugo kofa da karfi, Umma ta bita da kallan mamaki.

  *******

  Karfe hud'u da rabi Ashraf ya dawo, b'angarensa ya nufa, shima dan littibya wuce nasa.

  Zama yai tare da d'aukan waya ya kira Little, yace "kin dawo?"
Tace eh yaya.

Yace "ki turomin Nafi."

Ta amsa sannan ya kashe.

Nafi ta kalla wacce tai wanka tai kwalliya cikin atamfa riga da siket, bata d'aura d'an kwalli ba kanta ba kisto sai dai ta tifkeshi da ribon.

  Kan nan yayi gwanin sha'awa.

Little ta kalleta tace " Yaya na kiranki, da alama dama shi kike jira."

Nafi ta harareta tace " ni wai ina mutumin ki? Naji shi shiru kwana biyu.

  Little tace "tafiya yai wlh amma gobe zai dawo."

Nafi ta zari d'an kwalinta tai waje.

  Kitchen ta nufa ta d'auko tiren data jera mai abincinsa sannan tai b'angarensa fuskarnan fal take da farin ciki, dukda dai kalaman Mumy suna kara yimata yawo a zuciyarta.

  A bud'e taga kofar hakan yasa tasa kai tare da sallama, Ashraf wanda ke zaune akan kujera ya kalleta fuskarnan d'auke da murmushi, dinning ta wuce ta ajiye sannan ta tsaya daga gun tace "ka taso."

  Hannu ya mata alamar tazo nan tad'an yi kasa dakai sannan ta make kafada tace " naki ni dai ka taso."

  Murmushi yai ga mamakinta sai taga ya taso ya nufota, jingina tai da jikin dinning din tana kallansa fuskar nan d'auke da murmushi.

  Ya karaso kusa da ita batai zata ba sai jitai ya rungumeta.

  Murmushi tai sannan tace " Yaya ka dawo lafiya?"

  " Hmm lafiya lau, jiya yaushe kika tafi?"

  D'agowa tai ta kalleshi tad'an mai hararar wasa tace " ba bacci kai ka shareni ba."

  Idanu ya zaro yace garin yaya?"

Ta turo baki tace "Allah yaya indai ina zuwa gunka kana min bacci ko?"

  Bakin data turo ya d'an sumbata hakan yasa ta maida shi da sauri, yace " me za amin?"

  Kallansa tai tace " kazo kaci abinci."

  Murmushi yai sannan ya saketa ya ja kujera ya zauna tare da nuna mata kujerar kusa dashi.

Nan ta zauna ta zuba mai, kallanta yai yace " muci."

  Tace " am full."
Idanu ya kafeta dashi hakan yasa ta mike ta d'auko wani spoon din ta zauna.

  A hankali suke ci sai dai ya kamo hannunta na hagu ya rike.

  Bayan sun gama ne ta zubamai juice ya sha sannan suka mike.

  Hannu yasa a kugunta ta kalleshi tai murmushi a haka suka karasa ya zauna akan kujara tare da jawota kan cinyarsa.

Kallansa tai tace " yaya inada nauyi fa."

Dariya yai yace " indai kinada nauyi to lalai Afra ma tanada nauyi."

  Cikin shagwab'a tace " Afran?""

Ya d'aga mata kai sannan ya d'auko ledar dake gefensa yace " Gift."

  Kallansa tai ta amsa zata bud'e yace " ba anan ba sai kin tafi kya bud'e, yanzu dai tukuicina zaki bani."

  Yai maganar yana mata wani kallo, itakam in Yaya na mata irin wannan abun mamaki takeyi dan a iya saninta da gani take mutum ne wanda bashida sakin fuska, sai dai ferry dama ta fada mata maza duk daya suke indai a harkar so ne, kenan shi yana santa da gaske."

  D'an kwalin kanta ne ya zame, kanta ya kurama ido, a hankali yakai hannu ya shafa yace " i like this."

  Murmushi tamai sannan tai kasa da kanta tace " tukuicin me kake so?"

  Nesa dashi ya nuna mata yace zauna, nan ta tashi ta zauna a gun, zatai magana taji ya kwantar da kansa kan cinyarta yace " a gajiye nake, so nake inji ya bacci yake a kan cinyar matata."

  Kallansa tai tare da sa hannunta kan fuskarsa tace " amma ai kana kwanciya akan cinyar yaya Nisa."

  Yai murmushi bai ce komai ba sai idanunsa daya rufe.

  Murmushi tai sannan tasa hannu ta fara shafar kansa.

  Ta ina zata iya rabuwa da Ashraf?

  Bataji zata iya, in kuwa tai to gaskiya rayuwarta ta gama karewa.

*#ASHRAFEENAH*
💋

2 comments: