*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
{ *48*}
Ganin yanda jikin Nafi yai sanyi yasa Little tace " Me ya ce miki?"
Nafi tai murmushi tace " tambaya ta yai kawai yaushe zamu dawo nace wasu yau mukuma sai gobe."
Little ta dan tab'e baki tace " akan haka ne naga ya zuciya?ni wlh na d'aukama ko laifi kikai."
Habib yai dariya yace " kinsan yayan naki ai Gimbiya."
Haka dai sukai ta hira sama sama sannan sukai sallama tare da tafiya da kayan Nafi yanda gobe sai dai ta taho ita kad'ai.
********
Shikam Ashraf har ya isa gida zuciyarsa batai sanyi ba, sai ma kara tunano abinda tamai kawai dayakeyi, sannu yaya? Lalai kalman nan ta bala'in b'atamai rai ya cije leb'e tare da yin kwafa lalai yarinyar shi zata dizga???
Da karfi ya shiga gidan ko mai gadin bai kalla ba ya fito tare da rufe kofar motar da karfi yai bangarensa.
A falo yaga Anisa tana ganinsa ta taso da sauri tana neman rungumeshi gocewa yai ya wuceta yai gaba.
Kallan takaici ta bishi dashi tana kallo ya shige d'aki tare da rufo kofar da karfi, wanda har sai dayasa tadan razana.
Yana shiga ya cire kaya ya wuce toilet, ya dade yana zuba wa kanshi ruwa kafin ya fito.
Ya kwanta akan gado tare da daura hannu akan goshinsa, Anisa ce ta shigo cikin kissa ta zauna a gefenashi tace " Dear muje kaci abinci ko?"
Juya mata baya yai yace " banasan magana yanzu bacci zanyi."
Kallansa tai tace " Amma......"
Wani kallo daya mata yasa ta mike tai waje.
******
Nafi ce bayan isha'i zaune a hostel itada Ferry da Jibiya suna cin abinci, sai wasa kawai take da cokalinta sam ta kasa kaiwa bakinta, Ferry ta kalleta tace " banga laifinki ba Feena gaskiya Ashraf ya hadu karshe sannan rashin maganarsa da hade fuskarsa charm dinsa ne."
Nafi ta buga mata harara, Ferry tace " sai dai bawai ina nufin haduwarsa da charm dinsa ba ko kudinsa sune zasusa yafi karfinki ba ko ki karaya ba, sai dai......" shiru tai batare da ta karasa ba.
Nafi jiki a sanyaye tace sai dai me??
Ferry tace " sai kinyi da gaske dan irinsu ko suna san abu in har ka nuna musu soyayya dayawa to fa zakasha wahala, kinada kyanki ga gashi gaki 'yar chas in har kika bi yanda ya kamata Ashraf bazai miki wuyar samu ba."
Nafi ta kalleta sannan ta dan yi murmushin yake tace " Ferry ni fa ba 'yar gidan bace, na dade inaso in sanar da ku hakan."
Harararta Ferry tai tace " Nasani ai."
Mamaki ne ya bayyana a fuskar Nafi ta kalleta tace " How? When?"
Ferry tai dariya tace " kin manta nasan sunanki?sannan sanda muna Junior ai kowa yasan bafulatana ce ke kuma kema dakanki kin fada kince daga karamar hukumar gwaram kike."
Nafi tai dariya sannan tace " lalai Ferry."
Ferry tace " bansan matsayinki a gidan ba sai dai inaso ko ma meye matsayinki karki bari wannan ya rage miki daraja."
Nafi ta kalli jibiya tace "Jibiya lalai ki kiyaye yayan nan taki kwakwalwarta a cike take fam da plan."
Sukasa dariya, nan suka shiga hirar bikin jibiya wanda za'ayi bayan sun koma ba da dadewa ba.
A ranar dai basuyi bacci ba dan hirar karshe a makaranta.
Washegari da safe kuwa suka shirya suka kamo hanya, Ya Nabil ne yazo ya d'aukesu, a hanya ma hira sukai tayi Nabil na kara sasu dariya dan mutum ne mai tsananin barkwanci.
Nafi suka fara ajiyewa sannan sukai sallama, ganin gidan yasa Nabil ya kalli Ferry bayan Nafi ta shiga ciki yace " Farida dama a gidan Marigayi Abbas Saleh take?"
Ferry tace " ka sanshi ne?"
Nabil ya juyo yace " kin manta? Ta kalleshi tace me fa? Ya harareta yace " inda Dad yai aiki da ai company dinsa ne."
Ta mai kallan mamaki tace " haba?inda ya ajiye aikin bayan mai company din ya rasu?"
Nabil yace "Bingo! Kinsan ai da Secretary din marigayin ya fara daga nan har ya zama Chief Director."
Jibiya tace " me yasa dan ya rasu ya ajiye aikin?"
Nabil ya girgiza kai alamar bai sani ba sannan yace " kawai dai nasan ya taba cewa mutuwar mutumin akwai conspiracy."
Sunyi mamakin jin hakan sai dai agun suka bar maganar sukai gaba.
*******
Nafi kam bangaren Mumy ta fara zuwa bayan sun gaisa ta mata murnar gama makaranta sannan tace "taje tai wanka ta kuma ci abinci."
Nan Nafi ta mike ta fito tai b'angarensu, Little ba tanan dan dama tasan nazata sameta ba sakamakon jarabawar da sukeyi a makaranta.
Wanka tai tana fitowa taga an aiko da abinci inji Mumy, sai data shirya tai sallah sannan taci abinci ta kwanta akan gado, ko minti goma batai ba bacci yai gaba da ita.
Ashraf wanda ya kasa samun Little yana shigowa gida yai b'angarensu, knocking yai yaji ba motsi bai kawo komai ba dan baima san Nafi ta dawo ba ya murd'a kofar dakin.
Tsayawa yai daga bakin kofa ya kura mata ido, a hankali ya tako zuwa cikin d'akin ya tsaya tare da kallan fuskarta, bacci take sosai ba wani kwalliya tai ba, ya kalli jikinta riga ce doguwa mai ba wai ta bacci bace sai dai ta bi jikinta ga hanun rigar karami ya mata kyau sosai 'yar kanti ce.
Kansa ya girgiza yace " me kake kallo?" juyawa yai zai tafi yaga tad'anyi motsi, ya juyo ya kalleta sannan ya juya zai wuce.
Hannunsa yaji an rike, juyowa yai tare da hadiyar wani abu, Nafi tace "Yaya?"
Ta fad'a cikin muryar bacci, kallanta yai tare da dakewa yace "Yaushe kika dawo?"
Ta saki hannunsa sannan tace " d'azu."
Kai ya jinjina alamar to sannan ya kara kallanta, ta daure tace "me kake anan?"
"Little, little nake nema."
Batanan, abinda ta fada kenan ta juya mai baya tare da rufe ido, ya kalleta, is that all? Yauma? Ba ko gaisuwa?
Ya dauka ko in ya fqra tafiya zata kulashi amma sai yaji dif, ya juyo yaga har yanzu bata juyo bama, komawa yai rai a b'ace yasa hannu da karfi ya zaunar da ita.
Kallansa tai cikin tsoro, tace cikin tsoro mai nai kuma?"
Yatsa ya nuna mata yace " ni wanene?"
Tace "ban gane ba?"
A zuciye yace "waye ni? Just answer nake so."
Tace " Ya Ashraf mana."
Ya ce "ok good, in har zaki kirani da yaya ban isa ki gaidani ba ko me?"
Kallansa tai sannan tadan shagwabe fuska tace "Bacci fa nakeyi ka tasheni."
What?
Tace " sannan naga kamar baka fiya san gaisuwa ba dan naga da in na gaida kai ba koda yaushe ma kake amsawa ba."
Wata irin dariya yai yace "And so?"
Tace "nima shiyasa naga in kana cikin mood din amsawa sai inyi gaisuwar."
Kallan mamaki ya shiga yi mata, kanta ta d'auke ta juyar dashi gefe, a zuciye yasa hannu sai juyo da fuskarta ita kuma tai saurin gocewa gashi gaba dayanshi dama ya gama sakar jiki, ya kara sa hannu ai kam ta matsa da sauri ta koma can karshen gado.
Mamaki ya kamashi yace " ni kike gudun ma?"
Ya fad'a tare da hawowa gadon yazo kamata ta tai saurin kwanciya, tare da yin rufda ciki.
Babbakewa yai ya juyo da ita da karfi, nan shima kuwa ya fada kan gadon sukai facing din juna, kallan juna suka shiga yi, Nafi ta daure ta d'auke fuskarta, cikin wata irin murya yace "Yaushe kika zama haka?"
Ta kalleshi gabanta na fad'uwa tace " Na zama me?"
Hannunsa yakai kan bakinta yace " fitsarariya mana."
Hannunsa ta ture tace " ni ka tashi ka tafi.........."
Bakinta taji cikin nata, gaba daya numfashinta ne ya tsaya, shikansa bai san me yakeyi ba, sai dai ya kasa daina abinda yakeyi.
Nafi anyi luf ana karbar sako, sai can ta farga da abinda sukeyi, tureshi tai iya karfinta, Ashraf takaicin kansa ya kamashi, da sauri suka mike zaune.
Nafi ta sauka daga kan gadon har yanzu hannunta bai bar rawa ba tace "Yaya me kake yi hakan?"
Jitai yace " wannan ita kadai ce hanyar saita bakin da bashida kunya, ki cigaba da min fitsara ni kuma zan koya miki hankali."
Da sauri tai hanyar toilet tana 'yan kokoni."
Ya bita da kallo, cikin takaicin abinda ya aikata ya mike, shikenan yasan ta gama rainashi yanzu kam, ya gaka jama kansa raini, amma me ya sashi yin hakan? Bayan ko Anisa da suke gida daya tun suna kanana bai taba sha'awar tabata ba har sai da sukai aure????
Itakam a toilet, gaban sink ta tsaya jikinta na bari.......
*AISHA ISMA'IL JIBIYA*
( _Allah ya raya mana baby ke kuma ya kara miki lafiya Ameen suma Ameen_)
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment