ZUCIYA*
Kowa da irin tasa
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
41
" Mansir ya shiga wani yanayi ganin anata shirye shiryen auren yayansa da budurwar da yake masifar so, sam ya daina zama a gida wanda hakan ya tada hankalin yayansa.
Abbas duk abin duniya ya dameshi ganin kaninsa a wannan hali, ana saura wata d'aya biki Mahaifin Ruma ya nemarma Abbas aiki a wani company na AL-Food.ltd, dan takardun Abbas sunyi kyau sosai.
Company ne babba wanda ake ji dashi bama garin kad'ai ba har kasa baki d'aya.
Kowa yayi murna sosai da wannan al'amari sai dai wanda ake dominsa sam baya farin ciki, an tsaida bayan aure da sati uku zai fara zuwa aiki a nan garin kano.
Saura sati biyu biki Mansir ya shirya bada sanin kowa ba ya tafi kano,address din Ruma daya amsa agun wata kawarta yabi yaje gidan.
Ruma kam alokacin ta dawo kenan daga amso dinkunanta na biki ta ganshi tsaye a bakin gate.
Fara'arta ce ta karo ta karaso inda yake tace" Mansir yau kaine a garin namu?"
Idanu ya kura mata gani yai ta kara wani kyau jiyai santa na kara ratsashi, ita ta katseshi da cewa "Mu shiga ciki mana."
Kai ya girgiza alamar a'a, tad'an had'e rai tace "na d'auka mun zama d'aya?"
Sun shiga ya fara kallan tangamemen gidansu, lalai yaya ya cuceshi ya kwacemai Ruma sannan an bashi aiki ga iyayenta masu kud'i sosai?auren da yake fata kenan.
Falon baki ta kaishi sannan ta shiga gida ta had'omai abinci da drinks.
Fita tai ta barshi yaci abinci kafin nan ta koma,suka sake gaisawa sannan tace" D'an lelen Abbas ya akai?"
Mansir yasadda kai kasa tare da d'agowa a marairaice yace "Ruma!"
Yanda ya kira sunanta yasa jikinta yai sanyi cikin tsoro tace " Badai wani abun ne ya samu Abbas ba?"
Kai Mansir ya jijiga alamar a'a tai ajiyar zuciya sannan tace" Kaine ka tsorata ni Mansir."
Ya d'anyi yake sannan yace" Wata magana......"
Katseshi ta sakeyi da cewa" kasan Mansir ni in na tashi da kai zanyi kishi?"
Cikin rashin fahimta yace name fa?
Ta d'an rangwab'a kai tace "yanda yayanka ke sanka mana, shifa babban burinshi shine yaga ya samu aiki ya fara kula da karatunka da kansa sannan yaga duk wani abu da kakeso a duniya ya maka shi."
Mansir jikinsa ya d'anyi sanyi,Ruma kam zuciya d'aya ta cigaba da sanar dashi tsarindaya shirya na ganin ci gaban ka,sam baya tunanina da kansa."
Mansir yai shiru, Ruma tace " ya akai bai fad'amin zaka zo ba??"
Kallanta yai da sauri yace " shima baisan nazo nan ba"
"Why?"ta fad'a cikin mamaki.
Ya kara gyara murya yace "garin na shigo shine naga bari nazo mu gaisa, dan banaji zamu had'u da bikinku."
Bata gamsu ba sai dai da alama bayasanya fad'i gaskiyar abinda ya kawoshi.
Murmushi tai sannan ta mai alama da ta tauke bakinta tace " nima bazan fad'amai ba"
Yai murmushi jiki a sanyaye ya mike zai tafi, ya kalleta yace "Me kikeso game da Yaya?
Tai dariya sannan tace " Mutum ne mai mutunta na gaba dashi, yanada ilimi,ga addini, gashi bashida kyashi."
Shiru yai, a zahiri gaskiya ta fad'a, yasan kuma yaya yafishi da komai,ya saki yake yace "Allah ya baku zaman lafiya."
Da sauri tace "Amin."
Ya fito jiki a sanyaye.
yayan Ruma shine ya nemomusu gidan haya anan kano dan sam Abbas yaki yadda akan ya zauna a d'aya daga cikin gidan Mahaifinta ko na yayan nata.
Ranar d'aurin aure da sassafe Mansir yabar garin maiduguri ya shiga motar Jigawa.
Tunda Abbas ya tashi yaga ba d'an uwansa ya shiga wani yanayi nan ya bazana naimansa sai dai sam ba Labari, ga duk wayoyinsa a kashe.
Har lokacin d'aurin aure Abbas bai dawo ba nan shima aka shiga naimansa a tasha aka ganshi duk ya rikice da naiman kaninsa,da kyar aka samu aka mai dashi aka shiryashi aka wuce dashi gun d'aurin aure.
An d'aura aure sai dai ko jira baiyi ayi gaishe gaishe ba ya fita,wannan abu yaba iyayen Ruma haushi, a maiduguri aka d'aura auren gidan yayan babanta, dan dama mahaifinta ne kawai a kano da iyalansa.
Mansir kam ya isa kila sai dai yayi dana sai,babu inda zai zauna kakaninsu sun rasu, mahaifiyarsa kuma tana aure a wani gidan tare da yaranta.
Haka aka wuce da Abbas kano yana cikin tsananin tashin hankali, a ranar aka kai Ruma sai dai ganin halin da yake ciki yasa itama hankalinta ya tashi,Abbas ya sanar da ita akan gobe dole zaije Kila neman kaninsa, ba tantama ta amince.
Abbas ya isa kila yaje gidan mahaifiyar Mansir nan aka kirashi, da kyar Abbas ya shawo kansa ya yarda suka taho, wannan ma sai da Mahaifiyarsa tasa baki,ganin in ya zauna a garin ma a ina zai zauna yasa ya amince suka koma,Abbas ya dage yanata tambayarsa akan menene matsalarsa sai dai Mansir yaki fad'amai, kano suka wuce,Abbas ya roki mahaifin Ruma akan subar Mansir ya zauna a b'angaren baki dake gidan,Abbas ya naimomai Buk.
Haka rayuwa ta cigaba, sam Mansir baya sh ga harkar yayansa, har ya gama karatu shima yai aure, a lokacin Abbas ya kara samun matsayi saboda kwazonsa.
Ruma har Mansir yai aure ko b'atan wata batai ba wannan abu na tsananin damunta, har matar Mansir ta haihu ta haifi namiji aka samai Asim, shekarar Asim 3 Allah ya ba Ruma ciki, farin ciki kamar suyi ka ka,a kuma wannan lokacin ne Abbas ya Fahimci ashe Mansir matarsa yakeso tun yana Js1, hakan ya faro ne sanda yaji Mansir suna hira da abokinshi wanda suke a maiduguri sai dai yana gama aji uku aka kaishi makarantar kwana, tundaga nan suka rabu sai yau suka had'u shine yake tsokanarsa ina Ruma kuwa? Dafatan ya aureta.
Hankalin Abbas ya tashi ya tausayama kaninsa wanda yake gani kamar shine sanadiyar durkushewar farin cikin kanin nasa.
Daga sanda Ruma ta haihu alheruruka sukai ta faruwa da Abbas, ansama d'anta suna Muhammad Ashraf.
Dukiyar Abbas tayi yawa a lokacin da Ashraf yakai shekara 8 yanzu company ne nasa na kansa, sanda ya gina tafkekn gidan wanda zai ishesu rayuwa duk yawan 'yayan da zasu tara shi da kaninsa.
Ashraf ya taso mai tsananin san mahaifinsa, sun shaku sosai, alokacin ne kuma Abbas yake yawan zancen had'in aure tsakanin Ashrafda Anisa wacce take shekara biyu."
" Abbas ya sanar da Ruma akan lalai ko bayan ransa karta kuskura tabar gidan nan sanda ta taimakeshi ya cika alkawari na ganin gidan nan ya zauna lafiya."
Mansir kam yana kishin yayansa ta harkar komai ganin duk abinda yakeso aduniya daga arziki, ilimi,mata da sauransu Allah yabad'aj uwansa ba shi ba."
Little tai ajiyar zuciya tare da share kwallarta tace "a lokacin Yaya na shekara 9 ne Mahaifinsa ya rasu,hatsarin mota yai, sannan Mumy na gama Takaba aka d'aura mata aure da Mansir wanda kowa bai san dalilin amincewarta ba.
Har Baban Yaya ya rasu bayan an kaishi asibiti zancenshi d'aya ne akan Mansir ya yafemai.
Nafi ta share kwallarta cikin tausayi, chakwakiya kenan, ta fad'a a ranta..........
THE INNOCENT TEAM
No comments:
Post a Comment