Monday, 10 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 38

*ZUCIYA*
  Kowa da irin tasa

   ©Ayusher Mohd.....

38

    Tsayawa yai cak cikin tsananin mamakin Nafi yarinyar da a iya saninsa sanda ya d'aukota ko dukanta zakai bazatai magana ba illa ma inka gama ta b'uya a wani gun tai kukanta yau kuma itace........
  Katsemai tunani Anisa tai da zanzaro ashar, tace " Lalai yau za'ayi kan babban b*********, ni kika rikema hannu?"
 Nafi ta sake mata hannunta batare da ta tanka mata ba sai neman giftata datai zata wuce.
 Cikin zafin rai Anisa tasa hannu iya karfinta ta hankad'a Nafi, saura kiris ta kifa taji an tareta tare da rungumeta, nan suka karasa kasa su biyu, basai ta tambaya ba tasan waye ko ince zuciyarta ta isar da sakon waye zuwaga gab'obinta.

   Aneesa mamaki ya kamata ta saki baki dalala tana kallan wannan al'amarin shikam Ashraf suna karasa faduwa, ya mike tare da sake Nafi sannan ya kalli Aneesa cikin fad'a yace " kinada hankali kuwa? Yanda kika hankad'ota inta fad'a kan wani abu fa??"

   Aneesa kam cikin mamakin kalamansa tace " Ya Ashraf kana nufin tare mata kai ko me?"
 Ya kalli Nafi cikin b'acin rai yace " wa zan tare wa? Ina miki fad'a akan zakiyi b'arna wata rana in har baki kula da abinda kikeyi ba kina min wani zancen banza."

Aneesa tace " Naji na d'au laifina amma inaso inji me yasa ka tareta kai ka fad'i ita kuma ta fad'i a jikinka?"

  Kansa ya shafa da hannu cikin takaici ya kalli Nafi yace " malama kama hanya ki fita, sannan in sakeji kin raina na gaba dake wlh inbakiyi wasa ba sai jikinki ya gaya miki."

  Nafi kalamansa sunsa gwiwarta tai sanyi ranta kuma ya sosu sai dai ya ta iya? Mikewa tai jiki a sanyeye tai waje.
 Tana fita Ashraf ya kalli Aneesa cikin takaici yace " ke bakiji kunya ba??yarinya karama ita take nusar dake nan d'akin aurenki ne ba wai na wani ba? Akan me zatama gyara miki gun da yazamar miki dolenki?"

   Aneesa wacce idanunta suka ciciko tace " Yaya nikam inaji a jikina kamar ba auren soyayya mukai ba, kamar ni kad'ai ce nake sanka kai kuma sanda kakemin kawai na 'yan uwan taka ne."

  Idanu ya runtse sannan ya kalleta yace " a soyayyar danasan ina miki da, banaji yanzu ina miki ko rabinta sannan bana tsamannin zaki tambayeni dalili ganin ke kikafi kowa sannin abinda ya jawo hakan."
 Yana kai nan ya zari makullin mota yai waje.

  Aneesa ta fashe da wani irin kuka na bakin ciki itama ta fito tai b'angaren Ummanta tana kuka wiwi kamar wacce akama duka.

  *************

  A b'angaren Asim kuwa yana ganin su Ashraf sun tafi yai b'angaren mahaifinsa cikin tsananin tsoro da firgicin kalaman Ashraf.

   Yana isa ya kwankwasa tare da murd'a kofar ba tare da ya jira an bashi izini ba.
 Kawu wanda ke zaune gaban wani karamin akwati (kit) yana duba wasu takardu yanajin motsin mutum yai saurin rufe takardun tare da maidashi cikin kit d'in, yana kokarin tura kit d'in karkashin gado Asim ya fad'o d'akin tare da kallan mahaifin nasa.
 Shikam Kawu da sauri ya karasa turawa sannan ya had'e rai tare da cewa " Kai Asim bakada hankali ne zaka fad'omin d'aki ba sallama?"

  Asim ya karaso kusa da mahaifinsa tare da tsugunawa a gabansa yace " Abba ya zanyi?"
 Cikin mamaki yake kallansa yace " Da me fa?"
 Asim ya share zufa nan ya sanar dashi duk abinda ya faru sai dai ba fad'amai da sanin Umma a harkar ba.

  Kawu ya kalleshi cikin b'acin rai sannan yasa kafa iya karfinsa ya ture Asim, ya cigaba da magana cikin fad'a, Asim me yasa ne sam bakada hakuri? Banine nace kabar komai a hannuna ba?"

  Asim ya rusunnar dakai yace " Abba kayi hakuri wlh ni sam banasan ganin yaron ne."
 Tsaki kawu yaja sannan yace " zancen banza ma kakeyi, yanzu idan wad'anda ka tura sun kama Ashraf kenan 'yan sanda suka zo fa?"
 Kana tunanin bazasu sanar dasu kaika aikosu ba? Daganan sai me? Kamaka zasuyi a banza."
  Asim yai kasa dakai cikin dana sanin gaggawar daya aikata, kawu yacigaba " ni nace kabar komai a guna, akan me zamu halakar dashi bayan bamu gama sannin iya dukiyar dake karkashin sa ba?"

  Asim ya jinjina ma mahaifinsa kai sannan ya bashi hakuri, nan kawu ya sallameshi tare da zama akan gadonsa yai shiru yana tunani, can cikin wata irin murya yace.

" Yaya ya zakayi??? D'an da kakeji duk duniya baya shi gashi a tafin hanuna, ya auri 'yata sannan matar fa kake santa kamar ranka ta dawo karkashina." Wata irin dariya ya saki wanda ni kaina saida tsoro ya kamani, da sauri nabar d'akin ina mamakin dama haka mutumin nan yake??? Lalai wata zuciyar akwai hassada da mugunta a cikinta.

   Asim na fita yai murmushin farin ciki tare da kara kallan kofar d'akin yace " Kai!!!! Amma Abba karshen mugu ne."
 Ya sa dariya sannan yace " ko menene a  akwatin nan???"
 Kad'a kai yai ya nufi b'an garen Umma, ya shiga kenan ya zauna yana jiran ta fito daga b'andaki sai ga Aneesa ta shigo da kuka.
  Cikin kulawa ya mike ya rungumota yana tambayarta menene? Aneesa kam kuka take sosai, nan Umma ta fito ta samesu a haka.
 Itama zama tai suka cigaba da tambayar Aneesa abinda ya sata kuka, Aneesa cikin kuka tace " Umma Ba Ashraf bane ya fifita yarinyar nan a kaina."
 Cikin rashin fahimta Umma tace " Ban gane ba?"

  Asim yace " Malama dalla daina mana kuka ki fad'a mana menene ke faruwa."
 Hawayenta ta share ta shiga sanar da su duk abinda ya faru tun daga farko har karshe."
  Umma ta mike cikin fad'a tace " Lalai za'ayi tashin hankali a gidan nan."
 Asim ya mike tare da cewa " akwai meeting dole ne yau ayi taron gaggawa na gida dan kuwa Ashraf yayi kadan ya wulakanta mana ke."
 A zuciye yai waje......

  *****************

   Nafi kam tana fita daga b'angaren Ashraf ta nufi nasu b'angaren taje shiga taji ance " Yaya Feena."
 Juyowa tai tare da kirkiro fara'a tace " My Amrah kece da kanki?"
 Amrah tai murmushi tace " yaushe kuka dawo?"
 Nafi tad'an jujuya kai sannan tace " ni kadai na dawo."
 Amrah tad'an yi hucci kad'an kamar babba, Nafi tai dariya tace " Yaya Amrah ya akai ne?"
 Tace " Mumy ce tace " in mun dawo daga makaranta muzo gun yaya Little ta mana wanka sannan ta d'auko mana kaya."
  Nafi ta d'an canza fuska kad'an tace "Amrah naji haushi fa! Wato ni bazan iya muku abinda Little zata muku ba ko me?"
  Amrah ta matso kusa da ita tace " Yahkuri Yaya Feenah wlh ba haka nake nufi ba."
 Nafi ta kama hannunta sannan tace " naji muje mu taho da Afrah." 
 Nan suka fara tafiya hannayensu rike da juna.

    ***************

A can kauye kuwa Datti yana cikin tsananin farin ciki da walwala, a 'yan shekarun nan dabobbinsa sun kara bunkasa sosai yazamo kaf kauyen garin ba wanda ya kaishi yawan dabobbi, shi kadai yake rayuwarsa cikin farin ciki ba wanda zai kashema kud'i bare har arzikinsa ya ragu.

   Sam bai damu da halin da Nafi take ciki ba bare kuma matarsa da d'ansa da suka gudu.
  Duk sanda aka tambayeshi gidan Nafi sai yace sai dai a tambayi Dan Litti dan kuwa shi bazai iya gane wa ba, hakan yasa duk 'yan garin sun d'auka da gaske yaje gidan 'yar tasa.
  Sanda Dan Litti yai wata 5 a garin kachako yad'an tara kud'insa ya shiga garin kano neman Ashaf sai dai duk yanda ya nemesu ya kasa samunsu kasancewar garin da girma sannan baisan wani kwatance ba sai Ashaf mijin Nafi, wannan yasa duk inda ya tambaya sai dai amai dariya gani suke kamar shirme yake ko kansa ne ya tab'u.

  Bayan kud'in hannunsa sun karene ya koma garin kachako ya cigaba da achabar sa har ya d'an samu wasu kud'i, ya sanar da uban gidansa akan zaije kauyensu ya dawo.
  Mamaki ne ya kamashi ganin kowa ya ganshi sai ya tambayeshi wai 'yar gidab Datti a wani irin gida akai kaita? Wasu ma cewa suke zasuzo ya kaisu.

   Datti yanajin labarin D'an litti ya dawo ya taho takanas ya tareshi suka keb'e, Datti ya kalleshi yace " ya kaje gidan?"
 Dan Litti ya girgiza kai alamar a'a, Datti yace " ka taimaken duk wanda ya tambayeka gidan Nafi kace musu munje ka taimaka min."
  Mamaki ya kama d'an Litti yace " What u say?"
 Datti yai tsaki yace " malam ni banasan wannan yaren arnan naka kamin hausa."
 D'an Litti yai saurin rufe baki dan yace ya daina turancin shima.
  Nan Datti ya lalaba Dan Litti akan yai karya wai sunje gidan Nafi.
 Shikam d'an litti ko sati baiyi ba ya koma garin kachako ya cigaba da kasuwancinsa, ganin yayi abokai acan ga uban gidansa na sansa sannan can yafi kawo masa kud'i.

   Wannan Kenan....

   To be continue ......

  *THE INNOCENT TEAM*

( _Dan Allah kuyi hakurin jina dakukai shiru wlh Wayatace tad'an same matsala sai do akai resetting d'in d'inta Tukunna.....Thanks 4 ur Love._ )

No comments:

Post a Comment