Monday, 10 July 2017

ZUCIYA....kowa da irin tasa 37

*ZUCIYA*
  _Kowa da irin tasa_

  © *AYUSHER MUHD*

   37

   Sun dade a haka kafin Ashraf ya d'agota daga jikinsa, kansa ya maida yana kallan gefen titi, a zahiri kunyar kallanta ma yakeyi, Nafi kam anyi dif kamar kazar data fad'a ruwa, kallansa kawai takeyi, Ashraf ya juyo ya kalleta ganin har yanzu bata dawo daidai ba yasa yai saurin cewa " Ke wai yarinyar nan yaushe kika yi baki haka? Sai magana kike ba tsayawa?"

   Nafi ta bud'e baki zatai magana sai shakuwa, jikake heee'i, kanta tai saurin sawa a cinyoyinta tana kokarin maida shakuwar, Ashraf yai saurin tada mota suka fara tafiya, shiru ne ya biyo baya Nafi ta d'ago a hankali ta kalleshi, ganin sun wuce hanyar gida yasa tace " Yaya ina zamu?"

  Kallanta yai sannan ya maida kansa titi tare da cewa " Hotel."
A tsorace ta kalleshi sannan tasa hannu a kafafunta ta matse jikinta, ya juyo ya kalleta dariya ta kusa zuwa mai, yace " lalai yarinyar nan me kike tunani?"
  Kallansa tai sannan a hankali tace " bakomai."
A ransa yace " lalai makarantar nan ta b'ata yarinyarnan, bayaji sanda tazo garin nan tama san me ake nufi da aure amma yanzu aga zancen hotek har tana wani matse cinyoyi? Shi me zaiyi da yarinya karama ma kamar wannan? In ma iskanci zaiyi?"

  Nafi kam aranta abubuwa da dama take ayanawa, ne zai mata a hotel d'in? Tunowa tai da sanda ya rungumeta da sauri ta girgiza kai alamar a'a, Ashraf kam kallanta kawai yake saura kad'a ya bigi wata mota, da sauri yaja burki sannan ya kalleta yace " badai tunani kikeyi ni? Kamar ni Ashraf zanyi miki wani abu ba? Banaji kinkai wannan matsayin ko da kuwa iskancin na keyi."

  Nafi wanda kalamanta suka b'ata mata rai tace " nima ai bance wani abu zakamin ba, sannan ko wani abun ne ai banaji nakai wannan matsayin."
Kallan mamaki ya mata, sannan ya had'e fuska tamau yace " Da alama raini yafara tasiri a tsakanin mu."
Juya kai tai batace komai ba sai d'an kunkuni datai, a zuciye ya fizgi motar, lalai yarinyar nan shi take ma kunkuni? Sun isa Hotel din ya karasa gun parking, kallanta yai sannan yasa hannu ya fizgota sam baisan da karfi ya jawota ba wanda hakan yasa ta fad'a kirjinsa, a hankali ta d'ago cikin tsoro, ya kalleta yace " me kika ce d'azu?"
  D'an karamin bakinta ta turo gaba tace " ni me nace?"
Yai wani murmushi yace " bakima san me kika ceba ko rainin hankali? Da alama ma zagina kikai."
Idanu ta zaro cikin mamaki ta d'aga jikinta daga nashi tace " ni? Yaushe? Taya za'ai in zageka koda kuwa naman jikina kake yanka?"
  Ya kura mata ido sannan yace " inkinaso in yadda baki zagen ba to ki fad'amin a ina kikaji zancen za'a tareni a hanyar zuwa office."

  Kallan sa tai cikin tsoro, ya matso da fuskarsa kusa da nata yace " what? Bazaki iya fad'a ba?"

   Idanu ta kifta sannan ta had'iyi yawu, ya sa idanunsa cikin nata sannan yace " bazaki iya ba?"
  Idanunta tai saurin maidawa kasa saboda wani abu dataji ya taho mata, komawa yai yazauna tare da d'aukan wayarsa yace " kijirani ina zuwa."
Yana kainan yai hanyar fita, batasan sanda tasa hannu ta riko rigarsa ba, yazo fita yaji an rikeshi, ya juyo ya kalleta sannan ya kalli rigarsa inda ta rike.

  Nafi cikin tsoro tace " tsoro nakeyi Yaya."
  Idanunsa ya kankance yana kallanta, ta cigaba " Tsoro nake kar na zama silar jawo gaba ko fad'a a tsakanin ku."
  Ashraf yai karamai ajiyar zuciya sannan yace " Nafisa me kika sani? Me kika sani game dani da 'yan uwana? Mutane sun d'auka ganin fara'a a fuskar mutane shi yake nuna suna cikin farinciki sai dai abin sam ba haka yake ba, kowa da kike gani shi kadai yasan wace rayuwa yakeyi a cikin zuciyarsa."

   Nafi tai shiru kanta na kasa bata kuma sakeshi ba, Ashraf ya sa hannu akan hab'arta ya d'agota yace " Asim ne?"

   Kai ta d'aga mai tare da maida kanta kasa, Ashraf yace " sakini inje in dawo lokaci na tafiya."

  A hankali ta saki rigarsa, ya fita.
Kallo ta bishi dashi jikinta duk ya gama sanyi.
Shikam Ashraf sam baiyi mamaki ba dan dama jikinsa ya bashi hakan, ya sani mutane dayawa ba sanshi suke ba a gidan amma kowa na kokarin b'oyewa banda Asim.
  Yana shiga ya bada takardun dayazo badawa sannan ya fito.

Nafi kam abin duniya ya dameta, Ashraf ya bud'e ya shiga, ganin yanda take kallansa yasa ya d'aga mata gira yace " ya akai kuma?"

   Nafi ta girgiza kai alamar ba komai sannan ya tada mota sukai gidan lawyer d'in babansa, nan ya ajiye wannan motar ya d'au tasa ta da sannan sukai gida.
B'angarensa suka nufa, yana gaba tana binsa a baya, sunje wuce wa ta b'angaren su Asim sai gashi.

   Ashraf ya saki wani murmushin rainin hankali sannan ya cigaba da tafiya, ba wanda yama juna magana har Asim ya gifta Ashraf kad'an.
  Yaji Ashraf yace " ASIM"
Ba Asim ba hatta Nafi wanda Asim d'in ke saitin ta ta tsorata da yanda Ashraf ya kirashi, Asim kam tsoro ne karara a fuskarsa, Ashraf ya tako a hankali yazo kusa dashi sannan ya sa hannu ya dafashi yace " ka tab'aji inda kura ta nemi kama zaki?"
  Asim yamai kallan mamaki sai dai bai amsa ba, Ashraf yai murmushi sannan yace " Ita kanta kurar da take tsoron zaki kaga kuwa ta ina ta isa ta kama sarkin dabobbi?"
  Ya kara matsowa kusa dashi sosai yasa bakinsa a saitin kunnensa yace " In har kurar tana neman halaka sarkinta to lalai sai tayi amfani da kwakwakwarta." Ya fad'a tare da nuna tasa kwakwalwar.
Sannan ya cigaba " in har batai amfani da nan ba to lalai ita zata fad'a cikin trap d'in datai na kama sarkinta."
Yana kai nan yasa hannu ya bubugamai kafad'a sannan yai gaba.

   Nafi kam a tsorace tabi bayan Ashraf.
Shikam Asim anan suka barshi sai dayai kusan minti biyar a tsaye kamar abu kara motsi kafin ya juyo da niyyar kallan Ashraf sai dai sam baya gun.

  Sun isa b'angaren sa, Ashraf ya kalli Nafi yace " D'akina nakeso ki gyaramin."
Ta kalli falon wanda duk yayi kaca kaca ko sanda yake shi kadai baya taba yanda falonsa yai  haka bare yanzu.
Ta kalleshi tace " nifa d'akinka kawai zan gyara."
Yace "Falon fa?"
Tace " Wannan kuma matarka sai tayi ai aikinta ne ba nawa ba."

   Matsowa ya farayi ita kuma tana matsawa baya, tsoro takeyi sai dai itakam bazata taba yadda ta gyara musu falo ba wato ta gyara suzo su zauna suyi soyayyarsu a ciki?
Jin tazo jikin bango yasa ta tsaya tare da kallansa a tsorace, Ashraf ya kalleta sannan yace " Maimaita kalamanki."
Kasa tai da kanta ba tare data maida ba, ya saki wani murmushi yace " in aka tambayi iyayenki matsayina a gunki me zasuce? Ahh i am really curious."
Zaro ido tai cikin mamaki tace " ban gane ba."
Yace " Menene matsayina a gunki?"
Gabanta ne ya fad'i da sauri tace " Yayana mana."
Yace " Good."
Menene matsayinmu a gun iyayena da 'yan uwana?
Tace " Wanda ya taimakeni."
Yace " Bravo!, to menene kuma matsayina a gun 'yan kauyenku da mahaifinki?"
  Baki ta shiga motsawa tana san magana sai dai bazata iya fad'a ba.
Ya juya ya fara tafiya sannan yace " in kina san 'yancinki kimin biyayya sai in baki takardarki cikin sa lama ki auri wanda ranki yakeso."
Cikin takaici tace " in naki fa?"
Yace " Well! Wannan kuma ya rage naki kinsan dai ba'a aure kan aure ko? Haka nan zakiyi ta zama har ila masha Allah."
Yana kainan yai hanyar dinning.
Tabishi da kallan takaici, ba ma zaka zauna dani ba sai dai haka zan ta zama har ila masha Allahu, lalai ma Ya Ashraf.....

  Cikin takaici ta shiga gyaran gida ranta inyayi dubu to fa ya b'aci, takaici duk ya turnuketa, ko inama wannan matar tasa taje? tai maganar ranta a b'ace.
Hotunsu ta kalla dake manne a falo sunyi masifar kyau kamar me, taja tsaki sannan tace " Aikin kawai ko kyau ma."

Lol nikam ai dariya ce ta kamani na kara kallan hoton wanda yaune rana ta farko danaji an kushe wannan hoton.....Su Nafi ko me yasa akaga munin hoton da ni kaina na bash A1?????

  *THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment