*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
{ *49*}
Yau kwananta biyu kenan da dawowa, Little na zaune tana karatun jarabawa ita kuma Nafi tana zaune tana ninke underwears dinsu data wanke, Little ta kalli Nafi tace "Feenah haryanzu bakice komai ba."
Nafi tace "Name kenan?"
Hararta Little tai tace "Alamin mana kinsan dai yanda yake neman sanin lokacin da zaki dawo."
Nafi ta ajiye ninkin sannan ta kalli Little tace " Little nifa wlh ko kadan ba san Alamin nake ba, banaso sam na yaudareshi ne shiyasa kikaga ina baya baya dashi."
Little ta maida hankalinta kan Nafi tace "I know that, sai dai in har kikace da haka zakiyi soyayya kina ganin zai yiwu?"
Nafi ta mata kallon alamar tambaya ?
Little ta gyara zama sannan tace "tunda kikazo garin nan wa kika kula? Samari dayawa namin zancen suna sanki sai dai ganin yanda kike dauke fuska yasa kowa yake shakkar miki magana, sai yaushe ne zaki saki zuciyarki ki sami mai sanki saboda Allah?"
Nafi a ranta tace "Little bazaki gane bane." amma a fili sai tace " Little nifa soyayyar ce sam bata gabana."
Hararta Little tai sannan tace "ko dai akwai wanda kike so?"
Da sauri Nafi ta mike, sam bata kula karfen bra ya makale a rigar material din dake jikinta ba."
Kallan Little tai da sauri tai hanyar waje tana cewa "lalai Little na kula yau tambaya mara amsa kike neman yi."
Waje tai da sauri tana fita tai ajiyar zuciya daga nesa ta hango motarshi yayi parking, ta dan kurama motar ido sannan tadan harari gun tace "duk laifinka ne kasa Little na neman tsuyeni."
Tafiya ta fara cikin nata salon, shikuma ya fito daga mota ya tsaya kallanta, tun randa abin nan ya faru bai kara sata a idansa ba, sai dai ji yake kamar yayi wata d'aya bai ganta ba, pride dinsa kuma bazai bari ya nemeta ba da kuma tsoron karta rainashi.
Ganin yanda yake kallanta yasa ta kara canza tafiya tare da dauke kai daga gunsa shikuma ya jingina da jikin mota, murmushi tai a ranta sannan ta cigaba da tafiya, sai datazo kusa dashi sannan ta kalleshi tace " Yaya Ina wuni?"
Bai bata amsa ba sai kallanta da yake ta karaso kusa dashi sosai sannan ta hade rai tace "shi yasa banasan gaisheka sai ka ga dama kake amsawa."
Ganin bashida niyar bata amsa yasa haushi ya isheta ta juya zata karasa kitchen, hannu yasa ya rikota harta giftamai kadan, ya dawo da ita gabansa, ta kara bata rai tace "Hanuna."
Bai saketa ba sai dai ya matso da kansa saitin kunenta jikinsa na taba nata kallansa tai gabanta na faduwa, ganin a waje suke.
Jitai yasa hannunsa ta kugunta, tsoro ya kamata a hankali tace "Yaya me kake yi haka?"
Bai tanka mata ba sai kara matsota dayai, tace "Yaya a waje muke fa me kake yi hakan?"
D'agowa yai sannan ya mika kata bra d'in yace " Bakya kunyar mutane susan size dinki?"
Idanu ta zaro cikin tsananin kunya ta wafta tare da b'oyewa a cikin rigarta, da sauri ta juya ciki, tafe take tana sauri, shikuma sai murmushi yakeyi.
Nafi tana shiga ta jefar da bra din akan gado tare da kwanciya itama da karfi ta hau birgima kamar karamar yarinya, Little ta kalleta tace "Me kuma ya faru?"
Nafi tana juyi tace "shikenan na gama nikuma."
Little tace "menene wai?"
Kai Nafi ta girgiza sannan ta d'an jade rai tace "Little bakiga bra ta makale ajikina ba sanda na fita?"
Little tasa dariya tace "haba? Garin yaya!"
Nafi ta baza tagumi tace "shikenan ni kuma."
Kallanta Little tai tare da guntse dariyarta tace "to menene? Ai ba abin kunya bane, wani ne ya ganki?"
Nafi ta dan harareta tace " ba abin kunya ba kamar ya???" wayyo ni...."
Little tai dariya tace " to menene? Ai kowa yasan kinkai lokacin sawa kuma ansan haka kawai da saninki bazaki fita dashi ba."
Nafi ta kwanta tare da rufe kanta da bargo.
Wayar Little ce tai kara ta daga tare da cewa to yaya.
Tana kashewa ta kalli Nafi tace "Yaya yace ki amso kai lunch dinsa ki kaimai."
Ido Nafi ta zaro tace "ni kuma? Ina matarsa?"
Little tace "inkinje wannan kya tambayeshi."
Gyara kwanciyarta tai little tace "ya?incemai bazaki kai ba."
Nafi tace "kice bacci nake."
Little tace "ba ruwana."
Tafi minti 15 akwance kamar bazata mike ba sannan ta tashi fuska a had'e tai waje, Little ta bita da kallo tare da dariya.
Nafi kitchen ta nufa ta amso mai abincinsa sannan tai hanyar b'angarensa.
Bayan ta kwankwasa ya zo ya bud'e tare da komawa cikin falo, Nafi kam tana shiga ta ajiye mai akan dinning ta juya da niyar fita, jitai ance ke zo nan.
Cak ta tsaya bata kuma je ba haka kuma bata tafi ba, Ashraf dake zaune yana kallo yace "bada ke nake ba?"
Nafi bata amsa ba, yace "Ke Nafisa!"
Juyowa tai tace "na kasa tantancewa ko da ni kake shiyasa na tsaya."
Wani murmushi ya saki yace " da alama mu goma ne a falon."
Ta kalli falon sannan tace "na sani ko matarka na kusa?"
Kallan mamaki ya mata yace "Matartawa ke nake ce mata?"
Fuska ta kara daurewa tamau tace " to nima kuwa ba sunana haka ba."
Ta juya, jitai yace "Nafisa bakiji nace kizo ba?"
Kallansa tai batace komai ba, yace "au yanzun ma da bra din kika fito?"
Da sauri ta shiga duba bayanta ya saki murmushi, ganin ba komai yasa Nafi ta shagwabe fuska tace "haba yaya?"
Mikewa yai ya karaso gunta sannan yasa hannu ya riko habarta yace " ba na hanaki min fitsara ba? Ko rannan baki daddara bane?"
Tace "yanzun kuma me nai?"
Yace " wlh kin canza gaba daya."
Ta kwace fuskarta tace " ni ba wani canzawa danai."
Hannunta ya kama ya jata zuwa dinning ya nuna mata kujerar dake kallan tasa yace "zauna."
Kallansa tai tace " inzauna inyi me? In ma abinci ne ni naci nawa."
Dariya taga yayi yace "Ohh abinda kikeso kenan? So kike ince muci abinci tare?"
Ta zaro ido cikin mamaki tace "yaushe nace haka ko kuwa haka ka fassara?"
Ashraf ya zaunar da ita sannan ya koma ya zauna, kallanta yai yace " ki zauna ki jirani naci abinci."
Tace "ni? Akan me?"
Yace "haka kawai."
Wata irin dariya tai tace " wannnan kuma banaji aiki nane." ta fada tana neman mikewa.
Yace zauna.
Kallansa tai fuska a hade, yace " ba dake nake ba?"
Zama tai tare da juya kai gefe, yace " zubamin."
Tace "me fa?"
Da ido ya mata alama da abinci.
Tace "yaya nikam menai ma ne yau?"
Kuramata ido yai yace "bansan ni kaina me nakeyi ba sai dai kawai naga inasan inga kinmin abinda nace."
Labanta tadan ciza sannan taja plate ta fara apkamai abinci sai data kusa cika plate din ya kalleta yace " Me kike hakan?"
Gabansa ta tura mai sannan ta mike ta fara tafiya, mikewa yai da sauri ya fizgota, tare da sata a bango, ta kalleshi idanunta sun fara ja, yace "wai Nafisa meke damunki?"
Ta kalleshi tace " na kasa fahimtar dalilin sani abubuwan nan sai dai yanzu na gane, u take me as a joke."
Idanunta ya kalla zuciyarsa na raya masa wani abun, ya daure yace " joke? Taya zaki fassara shi a haka?"
Hannunsa tadan ture batace komai ba ta juya zatai gaba, bai san sanda ya rungumeta ta baya ba, dif kamar an dauke wutar lantarki haka tai.
Cikin wata irin murya wanda bata taba jinshi da ita ba taji yace " Ni kaina bansan me nakeyi ba."
Shiru tai sai dai jikinta duk ya mutu, yacigaba " shiyasa nakesan ki cigaba da zama inda nake har sai na san me nakeyi tukunna."
Shiru tamai hakan yasa ya juyo da ita yace "Uhmm?"
Kallansa tai sannan tace " in zauna a kusa dakai kamar yaya?"
Ya dan juya kai yace "kamar yanda na kiraki yanzu."
Hannunsa ta dan zare tace " after that?"
Kallanta yai tace " eh after that, then what?"
Ya shafa kansa yace " ban fara wannan tunanin ba."
Murmushi tai sannan tace " I am sorry."
Kallanta yai yace " for what?"
Tace " bazan iya abin da kace ba, me yasa a koda yaushe zuciyarka ita kadai ce mai amfani agunka? Me yasa baka tunanin tawa?"
Ya kalleta yace " Me kike nufi?"
Kai ta girgiza sannan tace " Ka dinga ajiye matarka akusa dakai ba ni ba, nima daga yanzu zan fitar da wanda naga yana sona inyi aure."
Tana kaiwa nan tai waje, kallo ya bita dashi sannan ya runtse ido ya bud'e tare da naushin iska yace " Ashraf meke damunka? Me yasa duk lokacin da ka shirya abu daidai pride dinka ke hanaka????
Wata iska ya furzar ta takaici.....
Nafi kam tana fita hawayen datake boyewa suka fara zubowa tafiya kawai takeyi sam bata kula da Asim ba wanda suke zaune suna hira.
Shikuma yana ganinta ya mike tare da shan gabanta yace "ke yar iska?"
Kallansa tai da jajjayen idanunta, yasa dariya yace "au har kwarton naki ya fara b'ata miki rai? Ki dawo guna ni zankula da ke sosai."
Hararsa taicikin takaici tace " ni nafi karfin karuwa kuma inma karuwancin ne mai zanyi dakai?
Tana kai nan tai gaba, Asim kam ya kai kolowa gun bacin rai, ya juyo da niyar zaginta yaga wayam, hucci yai yace "lalai za'a kai gawar 'ya garinsu...."
Nace hmmmm......
*#ASHRAFFEENAH TEAM*
No comments:
Post a Comment