*ZUCIYA*
_Kowa da irin tasa_
*Na Ayusher Muhd*
39
Nafi ta shiryasu tsaf sun zauna a falo sunata hirar su, labarin makaranta kawai suke bata itakam kai kawai take d'agawa amma sam hankalinta ba'a gunsu yake ba, abubuwan da suka faru a d'akine suke dawo mata.
Ta zarfafa cikin tunani sam bataji shigowar Little ba, sai jitai an dafa ta, ta d'an xabura kad'an sannan tace " Amrah me kika ce?"
Little ta zagayo ta gabanta tare da harararta tace " Feenah wato baki mayi tunani na ba ko?"
Nafi ta kalleta sannan tai murmushi tace " My Little tuba nake wlh sam hankalina yayi wani gun ne."
Little ta zauna kusa da ita tare da cewa " Alamin yau ai karamar hauka yaso min."
Nafi ta d'an tabe baki tace " Name kuma?"
Little ta girgiza kai cikin takaici tace " wai shi a dole ke da Ya Ashraf akwai wani abu a tsakaninku."
Nafi ta zaro ido tace " kamar ya kenan?"
Little ta d'aga kafad'a tace " ohon masa, shi wai yanda kukeyi keda yaya sam bayaso, hankalinsa bai kwanta da yanayin yanda kuke ma juna ba."
Nafi tasa dariya sannan tace " lalai da alama baisan Ya Ashraf ba shiyasa, me zaiyi dani?"
Little ta d'an harareta tace " kijiki ke kuma, wai ashe yaje gunsa kafin ki fita yana gaidashi amma yaya wai da kyar ya amsa mai."
Nafi tad'an turo baki kad'an tace " wannan kuma ai yanayinsa ne ba wani abu ba."
Little tace " Na fad'amai amma kamar zigashi nake, sam ya hanani zama agun kamun nan shidai wai sai na fad'amai ko kina sansa."
Tsaki Nafi taja tace " daga had'uwa sai soyayya sai kace wata taxi?"
Little ta kwashe da dariya tace " Love at first sight yake so ku zama."
Nafi ta had'e fuska tace " lalai wayaga."
Dariya sukai a tare.
Bayan sallar sukaji kararrawar tarawa, Little cikin mamaki tace " Meeting kuma?"
Nafi tace " Ai nikam kafin ki dawo nayi bacci."
Mikewa Little tai tace " Bazaki ba?"
Nafi ta jawo pillow ta kishingid'a sannan tace " Family Meeting."
Little ta harareta sannan ta mike tai waje.
Nafi ta gyara kwanciyarta tare da kalan wayar da Alamin ya bata, kai ta girgiza alamar a'a dan zuciyarta na raya mata ta kunna wayar.
A can falo kuwa kowa ya hallara, Ashraf ne ya shigo daga karshe, ya ja kujera ya zauna.
Kawu ne ya fara sallama nan ya tambayi dalilin taron?
Asim ne ya mik'e sannan yace " Abba in anci abinci zan sanar da kowa."
Anci ansha kafin Asim ya mike yace " A gaskiya Abba bazan juri ganin abinda Ashraf yakema kanwata ba, yau cin mutuncin har yakai ya fifita wata kucakar 'yar kauye akan matarsa."
Wani murmushi Ashraf ya saki, Mumy kam kallan Ashraf tai cikin damuwa, ganin abinda yai yasa ta fara tsoron karfa ya b'allo wata maganar dan tasanshi sarai.
Kawu ne ya katseta da cewa " Ban fahimceka ba, Fad'an tsakanin Ashraf ne da Matarsa?"
Asim yace " Eh."
Kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf ya akai?"
Kallan Asim yai ba tare da ya d'auke idansa ba yace " Asim za'a tambaya ai kawu ni me na sani banda sani da akai nazo nan."
Kalaman sun ba kowa haushi sai dai ya zasuyi? Kawu ya kalli Anisa yace " ke me ya faru?"
Little kam fatanta Allah yasa ba Nafi ake nufi ba.
Anisa ce cikin sanyin murya tace " yarinyar nan 'yar kauye ce ta nemi kawomin raini dan na sata aiki shine na mata fad'a akan ni ba sa'arta bace shikuma shine ya shigar mata ya wulakantani a gabanta."
Mumy ta kalli Ashraf, Kawu ne yace " Ashraf me yasa ka wulakanta matarka akan tana nunama yarinya karama 'yar kauye laifinta?"
Ashraf ya kalli Anisa sannan ya kalli Kawu yace " wannan kuma itace takeda amsar tambayar, me yasa nabi bayan yarinyar? "
Mumy ta kalleshi tace " Ashraf me yasa kai haka?"
Bai amsamata ba sai juya kai dayai, ya sani sarai dama yarda zatai da duk abinda akace mata yayi.
Anisa ta kalleshi cikin sakalcin magana tace " Yaya kaine fa kamin fad'a akanta."
Ashraf ya mike tsaye cikin takaici yace " fad'a? Ai banaji wanda na miki yau sunanshi fad'a, sannan Umma ki maida 'yarki kusa dake dan banaji tasan me ake nufi da aure, da kuma darajarsa."
Yana kainan yai waje abinsa.
Cikin zafin rai Asim ya mike ya sha gabansa yace " ce maka akai mun gama magana?"
Ashraf ya kalleshi yace " Me ya rage?takardar kanwarka? Ko 'yan daban daka turo d'azu?"
Asim ya kalli Ashraf cikin wani irin yanayi, Ashraf ya bubugamai kafad'a sannan yai gaba.
Bakin ciki ne ya cikama Asim ciki a zuciye yai wani irin ihu.
An gama taro kowa zuciyarsa ba dadi, Little ta shigo d'aki.
A kwance ta hango Nafi rike da Qur'ani a hannunta.
Ta shiga ta zauna kusa da kafarta.
Nafi takai aya sannan ta kalleta tace " kun gama?
Little tace " A kanki ma akai taron."
A tsorace Nafi tace " ni kuma? Me nai? Nashina."
Little tai d'an yake nan ta zayyane mata abinda ya faru......
Asuba ta gari
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment