*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*46*
Ashraf ya gyara zamansa a cikin mota sannan ya kira lawyer kuma abokin babansa, bayan sun gaisa ne yace " Uncle taimako nake san kamin."
Yace "me kakeso Ashraf kasan saboda kai nake ta d'aga time din retire dina."
Ashraf yai murmushi sannan yace " Nasani Uncle please so nake kaje Slc company kace ina tuhumarsu da satarmin project ka basu takardar shaidar sammaci a kotu."
Lawyer yai murmushi yace " da alama yanzu ka shirya fito na fito da su."
Ashraf yai dan kwafa yace " Uncle a duk sanda sukamin abu kalaman Abba daya rubutamin shi ke fad'omin sai dai inaji ajikina yanzu shima Abban bazaiso in barsu su kara b'ata ba."
Lawyer yai dariya sannan yace " Hakane, dama ance Eye for eye, tooth for tooth."
Sunyi sallama Ashraf ya bud'e mota ya fito, Asim ya gani ya nufoshi yana wata tafiyar kasaita.
Ashraf yaja tsaki yace " The biggest fool is here."
Asim ya karaso cikin isa sannan ya shiga tafama Ashraf, kallansa Ashraf yai yace " kai kuma me ke damunka?"
Asim ya saki dariya sannan yace " Ashraf shi yasa nace maka ka kiyayeni ni ba sa'an yin ka bane."
Kallan sa Ashraf yai yace " kana tunanin kaika aikata hakan?"
Asim ya jinjina kai yace " sosai ma tunda ninasa aka sace project din."
Kai Ashraf ya jijiga alamar tausayawa sannan ya matso yad'an bigi kafadar Asim da hannu yace " u are such a big fool, ka daiyi tunani dakyau amma ninasan kanka bashida wannan basirar, kaidai basirarka d'aya ka turo a kasheni."
Yana kai nan ya juya yai gaba.
Asim yabishi da kallo cikin kuluwa yace " me? Yasan Abbanane yasani ko me?"kai ya jijiga alamar a'a sannan yace " ai ba yanda zaiyi ya zargi mijin mahaifiyarsa.
Ashraf kam office ya koma ya cigaba da aikinsa, wanda akasa ya saci takardun a cikin members dinsa sai b'uya yake yi, sam Ashraf bai kulashi ba sai ma wani abu dake mai yawo a zuciya, wato kawu abin tsoro ne na gaske, ya tura d'ansa yayi abu yanzu in asiri ya tuno fa? Lalai mutumin nan wato akan abinda yakeso he can use anyone."
Yaja tsakin takaici inya tuna uwarsa ma amfani yake da ita.
Sai yamma ya tashi nan lawyer ya sanar dashi yace Slc ya sanar musu sai dai sunce a jira director ya shigo gobe dan shine yai proposing din project din.
Gida Ashraf ya wuce, yana shiga yai parking sannan ya kira Little a waya, bayan ta d'aga ne yace " turomin kawarki."
Little tace " wa kenan?"
Ashraf ya had'e fuska yace " wace kawa zance ki turon bayan Nafisa."
Da mamaki tace " naga kunyi sallama d'azu ta tafi ai."
Da sauri taji yace " bangane ba? Ina ta tafi?"
Little tace "Skul ba ta kiraka ba?"
Katse wayar yai sannan yai wirgi da ita gefen kujera sai a lokacin ya tuno mai sukai, yai hucci sannan yace " waya bata permission?"
Kansa ya shafa sannan ya fito ransa duk a jagule, b'angarensa ya nufa ya bud'e kofa ya shiga, kamshin turaren daya jine yasa ya d'ago dan ganin meke faruwa? Anisa ya gani sanye da wasu 'yan iskan kaya riga ce iya cibiya sai wani mini siket a jikinta tayi kyau sosai sannan kwalliyace ta tada hankalin duk wani namiji indai yanada lafiya, duk da shigar ta daki Ashraf matuka gashi dama ya dade rabonsa da ita dan dama ko da tana gidan haushin abinda takemai yasa yake kin kusantarta.
Idanu ya kankance yace " ke kuma me kikeyi anan?"
Cikin takun jan hankali ta taso ta fara tahowa tana tuno shawarar Umma ki maidashi naki, zuciya da gangan jiki bayan mun gama amfani dashi sai mu munamai yayi kuskuren fifita kucakar yarinyarcan akanki."
Ta karaso tare da zura hannayenta ta wuyansa ta kwanto a jikinsa sannan ta saki ajiyar zuciya tace " Hubby do u know how much i miss u?"
Ashraf ya d'agota sannan yace " me kikeyi anan......."
Bakinta ta saka a nashi nan fa kaji tsit malam....Duk yanda yaso ya daure ya ture Anisa ya kasa dan kuwa in zuciyarsa bataso to fa jikinsa naso.
Nan ya sungumeta sukai d'aki........Ni kuma da jawo musu kofa nai gaba.
Bayan sun gama ne sunyi wanka sannan Ashraf ya had'e fuska tamau, ta matso kusa dashi tare da daura kanta akan kirjinsa Tace " Hubby bazaka yafemin ba?"
Kallanta yai sannan yace " Anisa sam ni na rasa mai ke damunki."
Ta cusa kanta a kirjinsa tare da sakala hannunta ta bayansa tace " tuba nake dear, kaji? Bazan sake ba."
Yai shiru hakan yasa ta cigaba " Bakasan yanda nakeji ba in ina zaune a gun Umma."
D'agota yai zaiyi magana Nafi ta fad'o mai a rai, jiya ya tuno sanda ya rungumeta a jikinsa me yasa bayajin irin wannan yanayin inyana tare da Anisa?
Mikewa yai tsaye ya wuce toilet tabi bayanshi da kallo sannan ta tuno sanda tagansu sun shiga mota da Nafi.
Ashraf kam a toilet ruwa kawai ya sakar ma kansa a ya sa hannunsa ya rike bango ruwa na dukansa a bayansa, idanu ya runtse sai dai abin takaici Nafi ya hango sanda ta shiga cikin ruwa, ya bud'e idanunsa tare da kallan madubin dake toilet din mamakin kansa yakeyi ace kamar shi yazauna yana tunanin wata 'yar karamar yarinya?"
**********
Nafi kam tun bayan isarta makaranta sam ta rage ko magana dan daba ba kawar da zatai hira da ita, karatunta kawai takeyi sai dai a 'yan kwanakin nan har rama tai saboda ko abinci takeci tunanin Ashraf takeyi wannan abun duk ya isheta ta kosa su Ferry su dawo ko dan ta samu damuwar dake damunta ta ragu.
******
Scl hankalinsu ya tashi jin gaskiyar al'amari agun director cewarsa abokinsa ne ya bashi, wannan dalili yasa suka rubuta takardar hakuri suka aika company din su Ashraf wanda hakan ya sa ma'aikatan company d'in suka tausaya ma Ashraf sannan sukai dana sanin abinda suka aikata a gareshi, matsayinsa ya d'aukaka dan su cewa sukai a bashi matsayi babba wanda ya dace dashi.
Kawu kam duk yanda kaso kasan bakin cikin dake ransa bazaka taba sani ba a fili yafi kowa farin ciki dan har murna aka dinga tayashi ganin yanda yake ta farin ciki kamar me.
Sai dai Ashraf kam kallansa kawai yakeyi dan yasan sarai yafi kowa bakin ciki.
*********
Sati biyu da komawar Nafi makaranta 'yan skul suka dawo, farin ciki agunta kuwa ba'a magana, nan suka had'u da Ferry da Ferry da Jibiya, sai dai Ferry na ganinta tasan akwai abinda ke damunta.
Da daddare bayan jibiya tayi bacci Ferry ta kalli Nafi tace " Feenah meke damunki?"
Nafi tai yake tace " ba komai."
Ferry tasa hannu ta dafata tace " Nafi akan yayanki ne?"
Hawayen da ta dade tana had'iyewa ne suka zubo, Ferry hankalinta ya tashi tace " Feenah menene?"
Nafi ta goge hawayenta sannan cikin muryar tausayi da radad'in zuci tace " Ferry inaji san Yaya Ashraf shine zai zama ajalina."
Ferry ta kalleta tace " Feena me kike fad'a haka?"
Nafi ta kara share hawayenta tace " Ferry ko bacci nake da tunanin mutum nan nake kwana kullum sai nayi mafarkinsa, rashin ganinsa na hanani komai a rayuwan nan na rasa ina zansa kaina."
Ita kanta jikin Ferry sai dayai sanyi tace " Feenah."
Yanda ta kira sunan Nafi ne yasa Nafi ta tattara hankalinta kanta.
Ferry ta cigaba " Na fahimceki sai dai Feenah inaso ki koyama kanki danne so, kada ki kuskura ki bari shi wanda kikema wannan san ya fahimceki in kuwa kika bari har hakan ta faro? Maganar gaskiya ko shima yana sanki zai dinga wulakanta ki."
Nafi ta kalleta tace ta ya ya? Ferry tai dariya tace karki damu zan koya miki yanda zakiyi ki mamaye zuciyar wannan yayan naki, ba tare da kin wulakanta ba.
Nafi tai murmushi tare da rungume Ferry tace " Ferry shiyasa nake ma Allah godiya dayasa kike a matsayin Aminiyata."
Ferry ta harareta tace " ba wani nan bayan nayi nayi kizo muje gidan mu kinki?"
Nafi tai murmushi tace " nafisan zaman skul."
Ferry tace " Shikenan in kinasan kisan komai na kama saurayi sai kin yadda zaki bimu wannan hutun, Ammi nasan ta ganki kuma kinga daga wannan hutun sai extension."
Nafi tace " I will think about it."
Sukasa dariya dukansu.....
********
A riga kuwa yayyan Datti suka matsamai sai da sukasa shi ya sake aure, ya auri wata bazawara bafulatana, tanada 'ya'ya uku sai dai yace shi bazai rike ba, ita kadai ya d'auko sannan yamata kashedi sosai akan dabobinsa, ko garken ma ya hanata zuwa saboda bayasan ma tasan yawan dabobinsa, in zai fita kwad'o yake sawa a kofar karken sannan ya kakara itace.
Itama sam ta nunamai ba ruwanta da shirginsa hakan yasa yakejin dadin zama da ita......
*#THE INNOCENT TEAM*
This comment has been removed by the author.
ReplyDeleteWe do appreciate, I like your moves. You moved my ego so far. Keep it up Dear.
ReplyDeleteAllah yah kara miki basira plx kidinga yi dayawa Dan allah
ReplyDeleteMuna godiya pls kidan rinka mana da Dan yawa,Allah ya kara basira
ReplyDelete