*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*42*
Shiru sukai can Nafi tace " Little to ai shi Mahaifin Yaya bai sani ba na tabbata daya sani da bazai ci amanar kaninsa ba."
Little ta kalli Nafi tace " A ido Abbana yana nuna komai ya wuce sai dai daga yanda al'amura suke tafiya a gidan nan banaji har a wannan lokacin da Mumy take matarsa ya yafema Abban Ashraf."
Cikin mamaki Nafi tace " To ita Mumy me yasa ta aureshi daga gama takaba?"
Little ta d'aga kafada tace " Allahu a'alam shiyasa sam haryanzu Yaya bai sako ba."
Nafi tai shiru tana tunani, little tace " kuma kinsan ba wanda ya fad'ama yaya mumy ta auri Abba na? Shikuma a lokacin baiyi hankalin da zai kawo komai ba har sai sanda Mumy ta haifeni, lokacin shi kuma hankali ya fara zuwa mai."
Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace aikam ba'a kyauta ba, amma meyasa Mumy tai haka?"
Little ta girgiza kai alamar bata sani ba."
Nafi ta daure tace " To naji ana zancen wasiyya har ga matarsa?"
Little ta share kwallarta tace " Feena akwai wani sirrin da Mahaifin Yaya ne kawai ya sani saboda ayanda tarihin yazo shekarar da zai rasu lokacin yaya bai dade da shiga shekara 9 ba Abbas ya canza, shiru zaka ganshi yayi shi kad'ai sannan a wannan lokacin yana yawan zama da lawyernsa wanda yake abokinsa, hatta aiki daina zuwa yai sai dai in Ashraf ya dawo ya sashi a gaba suyi ta hira, in baya nan kuma sai dai kaganshi da diary yana rubutu."
Nafi tai shiru, can ta ce " me yake rubutawa?"
Little tai d'an dariya kad'an sannan tace " Yaya ne kawai ya sani dan shi yakema rubutun, sai dai ganin yanda Yaya bai tab'a nunama kowa ba sirri ne babba a ciki."
Nafi tai shiru mamaki duk ya kamata, a cikin ranta tace " ina mamakin abubuwa guda biyu zuwa uku, na farko me yasa Abbas ya barma Ashraf duk wata kadararsa bayan yana tsananin san kaninsa kamar ransa?q
Sannan me nene dalilin yin wasiyyarsa ba rashin lafiya yake ba bare yai tunanin ya kusa rasuwa, me ya sashi yin haka? Sannan abu na uku, wato Mumy.
Wata irin ajiyar zuciya taja Little ta dafata tace " me kike tunani?" kai ta girgiza alamar ba komai.
Little tai dariya tace " Feenah da alama lawyer zamuyi irin wannan tambayoyi da kikamin d'azu?
Nafi tai dariya zatai magana sukaji ana knocking, Kallan juna sukai sannan suka kalli agoggo karfe 9 waye a daren nan?
Little ta mike tare da bud'e kofar, d'aya daga cikin mai aikinsu ta gani, yarinyar tace " Wai Nafi tazo inji Umma."
Nafi dake tsaye tace " ni kuma? A daren nan?"
Yarinyar ta daga mata kai, Nafi ta janyo mayafinta ta kalli Little wacce tai tsuru tsuru tana kallan Nafi, murmushi Nafi ta mata tace " karki damu ba komai."
Nafi ta wuce waje.
B'angaren Umma ta nufa batasan me yasa ba sam ba tajin tsoron ko zasu mata wani abun.
Knocking tai daga ciki akace ta shigo, nan ta tura ta shiga da sallama sai dai ba wanda ya amsa mata.
Kallan falon tai, Umma ce a zaune ga Asim da Aneesa a gefenta.
Nafi ta karasa ta zauna a kasa tare da gaida Umma, batare da ta amsa ba tace " ke yama sunan ki?"
Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tai d'an murmushi tace " Feenah!"
Dariya Anisa ta saki tace " Mee? feenah? Ha ha ha."
Asim ya kalleta yace " ke dan.........Har kin kai matsayin da zaki raina Anisa a gidan nan? Ko dan kinga Ashraf na bin bayanki?"
Nafi ta d'an kalleshi ta tuna kalamansa ka d'azu da safe akan a kashe Ashraf, jitai wani irin tsanarsa ta kamata tace " banaji nayi abinda zaisa a kirani a daren nan, sannan Ya Ashraf ne ya kawoni gidan nan duk wanda abun bai mai ba sai ya sanar dashi a sallaman."
Asim a zabure ya Mike ransa yai dubu gun b'aci, Umma kam da Anisa mamaki ne ya kamasu.
Asim ya matso a zabure ya dage ya kai mata duka, Nafi ko gezau batai ba ta d'ago ta kafe shi da ido, ranshi ya cigaba da azalzala yace "ni kike ma wannan kallan?"
Nafi ta ki sauke idanta jitai an kifa mata mari wanda sai da falon ya d'au kara, fulani akwai taurin kai balle Nafi wacce wahala tun tana karama take shanta ganin ko gezau batai ba yasa Asim ya tafi a zuciye ya zaro wayar CD ya taho zai fara zabga mata.
Nafi ta mike tsaye tace " Ya Asim me na maka kake shirin duka na?"
Ya sake zabura yace " tambaya ta ma kike?"
Tace " Kanwarka itace zata gyara rayuwar auranta ni banga me nai ba balle insan dalilin dukan nan."
Asim yai wata dariyar takaici yace " Umma dama na fad'a muku yarinyar nan karuwar Ashraf ce inba haka ba har takai matsayin da zata dinga magana haka?"
Nafi ta kalleshi cikin wani mugun tsana tace " karuwa?"
Asim ya matso yace "me? Ba haka bane?"
Idanun Nafi ne suka fara neman kawo kwalla ta d'aga kanta sama tare da maidasu sannan ta kalli Anisa wacce itama Nafi take kallo cikin tsananin kishi, har zatai magana kawai tai waje a zuciye.
Anisa ta kalli Umma kamar karamar yarinya zatai magana Umma tace " Ai na fad'a miki ki cire Ashraf a ranki yanzu ai kingani yanzu."
Anisa ta kalli Asim, ya karaso gunta ya zauna tare da ce mata sau nawa kikasan ina kamasu tare? Shiyasa kikaga sam banasan Ashraf dalili kuwa shine nasan komai, ai kina kallo dai bata musa ba."
Anisa ta fashe da wani irin kukan takaici, lalai Ashraf ita zai ma haka? Asim yace " kada ki kuskura ki nunamai kinsani ki cigaba da nunamai yanda kike sanshi har sai mun samu abinda mukeso."
Anisa kam kuka take sosai.
Nafi kam tana fita taja can gefe ta takure ita kad'ai ta saki wani kukan takaici, karuwa?? Lalai mutanen nan makiyan Ashraf ne na gaske, shi me ya kaishi auren 'yarsu?? Me yasa duk da yasan basa sanshi suna neman kasheshi amma bai kai kararsu ba ko wani abun?
Kuka take sosai taga an dalleta da fitilar mota, a hankali ta d'ago jajjayen idanunta, ganin wacece yasa aka rage hasken fitilar.
Nafi ta dan karkata ta kalli motar, motar Ashraf ce hakan yasa jiki a sanyaye ta mike ta karaso jikin motar inda yake.
Ashraf ya sauke glass d'in motar.
Me kike anan?
Ta kalleshi da idanunta tace " Yaya gobe nake tunanin komawa skul saboda inyi karatu kafin a dawo, kasan yanzu S3 zamu shiga."
Kallan idanunta yai ba tantama yasa kuka tai yace " Wani abun aka miki?"
Kai ta girgiza alamar a'a ya juya kai yace " amma me kike anan? Ba dai jirana kike ba?"
Ta d'an bata fuska tace " ni a suwa? Akan me zan jiraka?"
Yai ajiyar zuciya yace " good daya kasance ba haka ba."
Nafi tad'an juya kai sannan tace " Amma yaya daga ina kake a daren nan?"
Yace " Ko Mumy inta ganni na dawo a wannan time din banaji zatamin wannan tambayar."
Baki ta d'an turo batace komai ba.
Ya kalleta yace " ki wuce ki kwanta gobe kizo da safe muyi maganar makarantar."
Ta jinjijina kai alamar to, sannan ta juya.
Kallanta ya tsaya yi baisan sanda ya saki murmushi ba can yace " me aka mata? Wata zuciyar tace kasan su ai."
Tsaki yaja sannan yai 'yar kwafa.
B'angarensa ya nufa yana shiga ya shirya tare da kwanciya ya d'auko diary din Abbansa shafin tsakiya ya bud'e.
" Ashraf ban taba tunanin abinda naji da kunena ba har kuma a wannan lokacin ina fatan abinda naji ya zama karya ba gaskiya ba, don't ever trust anyone except ur self."
Ajiyar zuciya yai yace " Abba me kaji? Me yasa baka rubuta ba?"
Idanu ya lumshe zuciyarsa na zafi, a haka bacci yai gaba dashi.......
*Fatan Alkairi gareku Masoyana, Allah ubangiji ya barmu tare (Ameen)*
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment