Friday, 21 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 51

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *51*

   Asim yana shiga bangaren Mahaifinsa yaga Mumy a zaune suna duba takardu, haushi da kishi ya kamashi ya karasa ciki a zuciye.
  Kawu ya kalleshi yace " Asim meye hakan zaka shigo ko sallama?"
 Asim ya harari inda Mumy take ya kalli mahaifinsa yace " in kuna tsoron Ashraf ni bana tsoronsa, sannan in ku bazaku iya komai ba akan halayensa ni zan gyara su."

  Kawu ya daka mai tsawa yace "Kai wani irin hauka kakeyi hakan? Zakazo ka dinga fadamin zancen banza ko ni din abokin ka ne?"

   Asim ya kafe Mumy da ido yace " gashi can dan da kuke ji dashi ya ajiye matarsa a titi ya zari karuwarsa sunyi gaba."

  Hankalin Mumy ne ya tashi ta kalleshi tace "Bangane karuwa ba?"

  Asim yai wata dariya yace " Au ke kika mahaifiyarsa bama kisa abinda d'anki yakeyi ba? Karuwarsa daya dauko daga wani kauyen nake nufi."

  Mikewa Mumy tai tace "Nafi?bangane abinda kake nu......"
 Bata karasa ba taji ana zage zage a waje, Asim ya juya yai waje, kawu yai wani murmushi ta gefe sannan ya mike yazo kusa da Mumy ya jawota jikinsa yace "Karki damu munfi kowa sannin Ashraf mun kuma san bazai aikata abinda suke fadaba, Anisa kawai suke tayawa kishi ba komai ba."

   Idanu Mumy ta runtse jin zage zagen da akeyi yayi yawa, nan suma suka fita, Umma ce taci damara ita da 'ya 'yanta maza, Anisa na tsaye sai matsar kwalla takeyi.

    Fada sosai ne ya kaure a waje banda zagi da cima Ashraf mutunci ba abinda sukeyi, mumy ganin bazata iya daure wa ba yasa tasa baki aikuwa kamar jira Umma take har cewa take zata daki Mumy kuma yau dole ne Ashraf ya saki 'yarta dan bazata yarda da cin mutuncinsa ba, sai dai zancen saki burga ce kawai takeyi dan tasan bazai yiwu ba.
 

   Little wacce hayaniya yasa ta fito tai tsiru tana jin su duk jikinta yai sanyi, bata taba ganin gidansu a haka ba.

   Suna tsakiyar zage zage sai ga motar Ashraf ta shigo gidan, nan fa kowa yabi motar da kallo dan ganin abinda sukaji, Ashraf kam tunda ya shigo yake mamakin taruwar ta menene, itakam Nafi kanta na kasa sam bata gansu ba, yana fitowa ya zaga inda Nafi take ya bud'e mata ta fito, kallan takaici tamai.

  Zata wuce taji kafarta ta hard'e ta kifo zata fad'i ta gaba, da sauri ya tareta, hannunsa yasa a kugunta d'aya kuma ya rike hannunta.

  Sallati suka saka, Umma ta shiga tafa hannu tana sallalami, Mumy ma idanu kawai ta rufe, kawu kuwa ko ajikinsa sai ma farinciki da yake.

  Nan Asim ya nufoshi a zuciye, Anisa kam zama tai a kasa ta kara sa wani sabon kukan.

  Itakam Nafi kallan Ashraf tai sannan a hankali ta zare jikinta ta kalleshi tace "Thanks."
  Bai amsa mata ba sai kallanta kawai da yakeyi, kai ta juyar gefe dan batasan kallan nan, Asim ta gani ya iso gun a zuciye ya dunkule hannu zai naushi Ashraf da sauri ta shiga gaban Ashraf ita naushin ya sameta, iya karfinsa ya sake wanda naushin sai daya sa tai baya.

  Ashraf ya razana da sauri ya tarota ya shiga kiranta, su Umma ne dukansu suka karaso gun suka cigaba da sallalami, Umma ta kallesu ya wani rungumota yana kiran sunanta.

 Tace "Lalai Ashraf bansan haka kake ba sai yau, to dama mahaifinka ya mutu kafin ka mallaki hankalin kanka, uwarka ta kasa hakura ta zauna tai tarbiyarka saboda bazata iya zama ba namiji ba ta auri kaninsa ta ma manta da danta, dama ina zakai hankali?"

  Ashraf ya d'ago ya kallesu dukansu, Mumy ya kalla wacce ke matsar kwalla a gefe, ransa ya kara b'aci ya kalli Nafi wacce bata farfado ba, sannan ya maida dubansa kan Umma yace " kun taremun jikin mota ina bukatar fita dan kaita Asibiti."

  Asim ya kara zuciya zai kara kai mai naushi wani kallo da Ashraf ya bugamai yasa ya tsaya, Ashraf ya nunashi da yatsa yace "Don't you dare think of something like this again, dan banaji zan yafema inka kuskura ka kara tunanin abu irin wannan, kasan ni kasan kuma abinda zan iya."

   Umma ta kutuntumo Ashar ta maka mai tacigaba " dan marasa tarbiya har mu zaka nunawa bariki? Daga kai har wannan tsinaniyar karuwar taka?jiki duk a kya mushe? Zaka wulakanta matarka ta suna akan wata can karuwa?"

   Ashraf ya kallesu, sannan yace " In kun gama zaku iya matsawa? inada gun zuwa na dauka na sanar daku."

  Kawu ya matso gunsa yace "Kai Ashraf bakada hankali ne? Akan me zaka dinga neman fita da yarinya bayan ka bar matarka ka dauketa kun tafi wani gun?"

  Ashraf ya kalleshi yace " Me kuke san ji daga gareni? Kafin ku tambayeni komai na dauka kowa a nan ya amince da abinda zuciyarsa ta fadamai?"

  Kawu ya hade rai yace " Ko ma menene dole ne gobe wannan yar kauyen mara asali ta koma kauyensu saboda yarinya guda d'aya bazai yiwu mu cigaba da samun sab'ani ba."

  Little ce ta mikamai ruwa a jarka data d'auko ya amsa sannan ya sa mata, numfashi taja sannan ta mike zaune, sai dai gefen fuskarta har ya tashi, Ashraf ya mike tsaye yace " who said that?"

  Kawu ransa ya b'aci yace "nine na fad'i haka kuma nine shugaba a gidan nan dolene ta koma kauyensu goben nan, bazan juri ganin tana neman lalata mana zumunci ba, yarinyar da ko asalinta bamu sani ba."

  Nafi kam yanzu ta fahimci da ita ake, jiki a sanyaye ta mike zata wuce, hannu Ashraf yasa ya riko nata hannun, cak ta tsaya sai gabanta kawai da yake fad'uwa, Ashraf ya kalli Kawu yace "Zumunci?wanne kenan? Banaji na sanshi, sannan maganar yarinya babu wanda ya isa ya sata ta tafi dan kuwa nine na kawota nine kuma nakeda hakkin sata ta tafi."

  Kallansa tai cikin takaici, tasani bazai iya cewa matarshi bace ita, yana gani yana kuma ji ana ce mata karuwa, hannunta ta fizge sannan ta kalli Kawu tace "Kawu kuyi hakuri zan tafi gobe in Allah ya kaimu."

  Tana fada ta juya, hannu yasa ya kara rikota nan ta shiga kokarin kwacewa, Mumy tace "Ashraf wai ke kakeyi hakan? Bazaka saketa ba?"

  Murmushi ya sakar musu yace " What should i do?"

  Kallansa sukai cikin alamar tambayar, yace " ya zanyi? Tunda Nafisa matata ce wacce na aura kafin Anisa, ya zanyi in ban rike hannun matata ba?"

    Gaba d'ayansu cak suka tsaya kamar abu mara motsi Nafi kam kallansa kawai take sai dai tsoro ya cika mata zuciya, a da tana so taji ya fada with full confidence akan ita matarsa ce to meyasa yanzu taji gaba d'aya ba haka ba?"

  Ashraf ya kalleta yai murmushi yace "muje ko?"
 Hannunta ya ja suka fara tafiya binsa kawai takeyi, sukam kowa ya kame ya kasa motsi, suna matsawa daga gunsu Nafi ta had'iyi wani abu tace "Yaya mai ka aikata?"

  Murmushi ya sakar mata yace "what? Are u scared?"

  Kallansa tai batace komai ba, har d'aki ya kaita yazaunar da ita tare da kallan inda aka nausheta yace "Me yasa kika taremin d'azu?"

  Kanta na kasa tace " nima ban sani ba."
 Yai murmushi yace " sanda naga kin taremin naushin da ya kamata ya sauka a jikina lokacin jinai komai ya daukemin a kuma wannan lokacin na gane meke damuna."

  Kallansa tai kallo mai alamar tambaya, kiss ya manna mata a kuncinta yace " Feena I think I Luv You."

    Kallansa tai gabanta ya tsananta fad'uwa baki ta shiga motsawa tana san tai magana ta kasa, Ashraf ya jawota jikinsa yana daga tsaye ita kuma tana zaune akan gado, yace " Be strong dan nasan akwai yaki babba a gabanmu, sai dai karki damu kowa zai gaji ya bari."

  Kai ta jinjina mai, yai murmushi sannan  ya saketa ya fita.

   Ko kallan inda suke baiyi ba yai b'angarensa.

  Anisa da gudu ta mike tai b'angaren Umma ta shige d'aki ta kulle, maganin Umma ta gani kawai ta debi guda 10, ta hau had'iya, kankace me jiri ya debeta ta fadi kasa ta suma, nan su Umma suka tadda ita a kwance, da gudu Asim ya d'auketa ya sata a mota sukai Asibiti.

 
  Nafi kam tana nan a zaune Little ta shigo da sauri bata mata magana ba kawai ta zari mayafi tai gaba, Nafi ta mike da sauri tace "Little ina zaki a daren nan?"

 Little bata tanka mata ba tai waje, jikin Nafi yai sanyi ta zauna a kasa ji take kamar tasa kuka, sallama taji ta mike ta leka, mai gadi ne ya miko mata leda yace " gashi inji yalabai."

 Yana bata ya juya ya tafi, bud'ewa tai taga magunguna, dana shafawa dana had'iya.

  Ta mike tai sallar isha'i sannan tasha, akan sallayar ta zauna kawai tana addu'oi Allah yasa komai yazo mata da sauki......

  Nima nace Amin.....

  Su Anisa kam dukansu har Mumy aka nufi asibiti, emergency akai da ita, likitoci suka dukufa akanta, sun dade kafin su gama aikinsu, suka kallesu suka ce " Kuna ina duk yawanku yarinya na neman kashe kanta?

   Umma ta harari Mumy tace "Likita masifa ce ta taso mana, bamu fargaba ta shiga d'aki."

  Yai dan hucci sannan yace "She is no longer in danger amma sai kun jira zuwa anjima kafin ta farfado."

  Yana kaiwa nan yai waje, Umma ta kalli Mumy tace " Lalai danki dan masifa ne, bala'i ne kuma annoba ne."

  Mumy cikin takaicin kalaman Umma tace " Malama kisan abinda zaki dinga gada nasan yayi laifi amma ko kadan bai cancanci kalamai irin wannan ba daga bakinki ba, dama kowa na gidan."


*#ASHRAFEENAH TEAM*
*1LOVE💞*

No comments:

Post a Comment