Thursday, 27 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 54

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *ASMY I Sincerely dedicated this page to u may Allah help and guide u through the right path always....(Ameen)......*😍😍😍

{54}

   Ashraf ya fita daga gun taron rai a b'ace, Dan litti ya kalla wanda ke waje yace " muje inkaika b'angaren baki ka huta ina da gun zuwa."

  Duk da Dan litti bakinsa tam yake da tambaya ganin yanda Ashraf yai yasa ya kasa tambayarsa, nan Ashraf ya kaishi sannan ya aiko da kaya a kawo mai shi kuma yai waje a mota da gudu.

   Ta ina zai soma nemanta???
Yayi yawo iya yawo ga magrib ta kawo kai, gaba daya hankalinsa ya gama tashi, ina Nafinsansa?

  Little ce ta kirashi a waya wanda ita kanta ta kasa zama daidai saboda rashin Nafi, bayan Ashraf ya d'auka yace "ta dawo ne?" yai maganar cikin zumud'i.

  A hankali tace "a'a yaya."

  Yai tsaki sannan yace " to meye?"

  Cikin sanyin jiki tace " yaya ina tunanin gidan kawarta ta tafi."

Da sauri yace "kawa?dama tanada wata kawa ne?"

  Little tace "Ferry wannan kawartata ta makaranta, ai a nan kano suke."

  Ferry??? Tai saurin cewa kanwar Ya Nabil.

  Duk da yaji haushin inda akace take dan shi ya dauka saurayinta ne, amma yanzu ganin Nafi shine a gabansa yace "ina ne gidan?"

  Tace "wlh bansani ba amma bari na turo maka number ferryn."
Yace "turon to."
Ya kashe wayar tare da dafa sityarin mota yace " lalai Nafisa zan gamu dake."

  Little ce ta turo number da sauri yai dialing sai data kusa katsewa Ferry ta d'auka cikin salon iyayi tace " HELLO!"

  Ashraf yace "Farida ce?"
Tace "nice, wanene?"
"yayan Nafisa ne, tana nan kuwa?"

  Ta kalli Nafi da suke hira da Ummansu tace "tananan amma...."
Da sauri ya katseta yace " a wacce unguwa kuke?"

  "kabuga ta fada."
Nan tamai kwatance ya katse layin, tabi wayar da kallo tare da cewa " kai wannan guy din Feenan sai a slow."

Mikewa tai ta koma gunsu Nafi, Nafi kam Umma ta kalla tace " Umma ashe Baba acan yai aiki?"

  Umma tace " Nabil je ya fada miki ko?"
Daya dawo ai yacemin a gidan Marigayi Abbas kike.

  Nafi tai murmushi tace " ba yar gidan bace bafa."

  Umma ta kalleta a nutse tace "kiyi a hankali da wannan gidan."

  Kallan mamaki Nafi ta mata tace "Umma meya sa?"

  Umma ta girgiza kai sannan tace " nidai abinda zance miki kenan, har yau in na tuno da mutumin nan sai naji zuciyata ta karye."

  Nafi ta kalleta cikin damuwa tace "Umma wai wani abun ne ya faru da Marigayin?"

  Shiru Umma tai sannan ta mike tace "bari in je kitchen Babanku ya kusa dawowa."

  Nafi ta bita da kallo cikin kulawa.

  Tana fita Ferry ta kalleta tace "tashi kiyi wanka."

  Nafi tace "ke nifa yanzu zan tafi, duk kece kikasa nai dare haka."

  Ferry ta jata ta turata toilet, Nafi tai dariya dama batasan komawa, da saninta tai dare dan Umma ta hanata tafiya, wanka tai sannan tai alwalar magrib ta fito, wata had'adiyar doguwar riga taga Ferry ta fito dashi, ta mata kallan tambaya sannan tace "zance zaki ko?"

  Ferry ta matso tace "Feenah gwada rigarnan, Baba ne ya siyomin dayaje umara to kuma abin haushi tamin kadan."

  Nafi ta ture hannunta tace "naki na gwada din."

  Ferry tace "shikenan bari na fada ma umma ta saki ki gwada." jin haka yasa Nafi ta amsa sannan ta gwada.

  Ta mata daidai, gashi kamar dan ita akai doguwar rigar, light pink ce sai dai daga gaban rigar ta sama anye jere da manyan duwatsu har kusan cikinta, ta mata kyau sosai, rigar tanada mayafinta sai dai mayafin plain ne.

  Nan Ferry ta sata a gaban madubi tace yi kwalliya.

  Nafi tace "wai ina zamu?"
Ferry tai dariya tace "sirri ne."

  Kai Nafi ta girgiza sannan ta fara kwalliya, tayi kwalliya sosai, ta kuma yi kyau sosai, nan ta mike tai sallah, tana idarwa wayar Ferry nayin kuka, da sauri Ferry ta d'au wayar tai waje.

  Nafi ta tabe baki tace "ferry kenan uwar soyayya."

Shigowa Ferry tai rike da wani turare a hannunta mai masifar kamshi, sanyin kamshi gareshi, nan tazo ta fesa ma Nafi.

  Nafi tai dariya tace "lalai  to ke yaushe zaki shirya?"

  Tace kedai ki sauka kuyi sallama da Umma.

  Nafi tace "Au bari na mike na tafi, amma meye ma sani kwalliya haka?"

  Ferry tai dariya tace "sauko."

Nafi wacce batasan tafiya kuma bazata iya fad'aba ta mike a hankali suka sauko.

  Umma tama sallama nan umma ta bata ledar dauke da turare da kayan kwalliya.

Nafi tai godiya suka sauko.

  Ashraf yana tsaye a jikin mota sai ga motar mai gidan ta iso, ya tsaya kusa da Ashraf dan ganin waye a kofar gidansa.

  Ganin ya tsaya yasa Ashraf ya karasa tare da gaidashi, gaban Baba ne ya fadi ganin ko wanene, cikin sanyin murya yace "Me kakeyi anan?"

   Ashraf yai murmushi zai yi magana yaji Baba wanda ya dauka gunsa yazo yace " Ba Ashraf bane?"

  Kallan mamaki Ashraf yamai yace "nine...Amma???"

  Baba yace " me kake anan?"

  Ashraf ya kalleshi yace "a ina kasan ni amma?"

   Gaban Baba ne ya fadi ya dauka gunsa yazo ai, cikin dan rawar murya yace "na ganka a magazine ne."
Yana kainan ya ja motarsa yai cikin gida.

Kallan mamaki Ashraf ya bishi dashi, yanda ya kira sunansa da yanda yamai tambayar bai yi kama da wanda aka gani a magazine ba, kallan gate din gidan yai yana mamaki, fitowar yarinyarce yasa ya katse mai komai.

  Kallanta kawai yakeyi, tunda ta fito, ganin mutum a tsaye yasa ta tsaya  itama, ferry tace "muje mana sanyin ranki ne."

  Nafi ta kalleta tace "ya akai yasan gidan nan?"

  Ferry ta nuna kanta da hannu, tace "kina wasa dani ko?"

Nafi ta harareta, Ferry ta dafata sannan suka cigaba da tafiya, kallanta yake ya kasa d'auke idanunsa, yaushe na zama haka? Meyasa bana iya jure abinda zuciya ta take fadamin akan wannan yarinyar?"

  Nafi kam kasa kawai take kallo, har suka karaso kusa da gun, Nafi ta tsaya itama a hankali ta d'ago ta kalleshi, idanunsa na kanta tad'an shagwab'e fuska.

  Ferry ce ta katsesu dayin gyaran murya tace "yaya ni zan koma."

  Ashraf ya kalleta yace "Farida nagode kwarai amma dole na bada tukuici."

  Dariya tai tace " ba wani tukuici yaya indai ka kula damu to komai ya biya."

  Hannu yasa a aljihu, yaji ba komai, ba dai bai d'auko wallet dinsa ba?"

  Farida ya kalla wacce take mai dariya, Nafi ma dariyar ta guntse, Ashraf yace "karki damu zan kawo tukuicin daga baya."

  Tace "ba komai yaya."

  Nan ta dafa Nafi ta rada mata a kunne, "ki tabbatar kin gama kwace zuciyarshi a yau din nan."

Tana kaiwa nan ta juya ta tafi, kallan Nafi yai yace "muje ko?"

  Tad'an turo baki sannan ta karasa ta shiga ta zauna, ya shiga tare da maida kallansa kanta yace " bansan ina fadan da zan miki ya tafi ba."

  Ta kalleshi fuska a shagwab'e tace " me nai da za'amin fada?"

  Kasa jurewa yai ya jawota ya rungumeta, a hankali yace mata " Nafeesa ni kaina ina mamakin kaina."

  Itama a hankali tace "Name fa?"

Yace "nakasa controlling din kaina a kanki, ni na san ba haka nake ba, ban kuma san ya akai na koma hakan ba."

  Idanu ta lumshe sannan tace " nifa ba yau naso komawa ba."

D'agota yai yace " kinsan zunubin dake kan matar data fita ba sanin mijinta kuwa?"

  Kallansa tai tace " ni kam ban saba da zancen miji ba."

  Ya matso da bakinsa kuncinta yace " ya? Ko kinaso in tabbatar miki ne a yau d'in nan?"

Idanu ta zaro da sauri tace " a'a bance ba."

Yai murmushi sannan ya tada mota, hannunta ya kamo ya rike d'ayan kuna yana tuki dashi, kamshin turarensa ne ya hadu da nashi sai ya bada wani sansanyan dadi, ga Ac din daya kunna, Nafi kam har wani lumshe ido takeyi, a zuciyarta tace "Allah ka d'auki raina a lokacin da nake irin wannan farin cikin."

  Har suka isa gida hannunsu na cikin juna yai parking sannan ya kalleta yace " b'angarena zamuje."

Idanu ta zaro tace "muyi me?"

  Hannu yasa ya ja kumatunta kadan yace "uwar tsoro abu kawai zan baki."

  Tai murmushi batace komai ba.

  Ya fito sannan ta fito shima, yana gaba tana binsa har suka isa b'angarensa yace "ta zauna, sannan shi kuma ya shiga d'aki."

  Kayan jikinsa ya cire ya saka doguwar jalabiya.

  Itakam hotonsu wanda sukai da Anisa kawai take kallo, baki ta tabe, sam bataji zuwansa ba sai ganinsa tai ya zauna kusa da ita.

  Kallansa tai ta saki murmushi, shima maida mata yai sannan ya nuna mata cinyarsa yace "kwanta."

  Kallan tsoro tamai, ya kafeta da ido, a hankali ta kwanta a cinyarsa tare da lumshe idanta, ya zame d'an kwalin kanta sannan ya fara shafar kanta a hankali, idanunta a lumshe suke sai dai Allah ne kadai yasan me takeji a wannan lokacin.

  Ashraf fuskarta yake kallo yace " gobe zamuje musai waya, daga yanzu karki sake fita ba sanina, kinji?"

  Kai ta d'agamai fuskarta d'auke da murmushi.

  Idanu ta bud'e a hankali tace " na d'agama hankali da baka gan ni ba?"

  "Hmm, ban taba zatan zanji haka ba."
  Tai murmushi tace " I can't help dole ne in sake guduwa wani gun."

  Harararta yai ya had'e rai yace " in kika sake gwadawa zakiga b'acin raina da baki taba gani ba kuwa."

  Ta turo baki tace " sai in sake shirya yanda bazaka iya min fada ba."

  Hararata yai yace " ahh i am dead, abinda banaso ya afko a kaina."

  Tace "mekenan?"
Yai furzar da iska yace "bazan iya fada ba."

  Murmushi tai sannan ta kara lumshe ido, ji take lalai in abu ya rabasu da Ashraf lalai to kuwa ba tantama mutuwa zatai sai dai wani iko na Allah.

A hankali yakai bakinsa ya sumbashi goshinta, ta bud'e ido a hankali suka kura ma juna ido, idansa ne taga ya d'an canza kala, batasan ya akai ba taji tsoro karfa su wuce gona da iri, su biyi a bangare.

  Da sauri tace " Yaya."

A hankali yace "Uhmm."

Tace "Abba hatsarin mota yai ko?"

  Kallanta yai yace "eh."
Tace "kaima hatsari kai harkaje garin mu ko?"
Yace eh.
Tace " Motar Abba alokacin an duba meya jawo hatsarin?"

  Kallan ta yai gaba d'aya hankalinsa na kanta, idanunsa taga ya kada sosai, ta mike zaune, tace" yahkuri in na ba....."

  Jawota yai ya rungumeta tsam a jikinsa, yace " me kike tunani?"

  Kai ta girgiza alamar ba komai.

  Ya dago ya kalleta hannayensa na kan kafadarta, yace " Nasani Nafisa sai dai banasan ki cigaba da binciken abinda bai shafeki ba."

  Hawaye ne ya zubo mata na tsananin tausayin Ashraf, idanunta na kansa tace " Na dauka duk abinda ya shafeka ya shafeni?"

  Hannu yakai a hankali ya share mata hawayenta yace " ba haka nake nufi ba....."

  Tacigaba da zubar da hawaye tace " Y are u enduring everything by ur self? Can't u share it with me?"

  Kallanta kawai yakeyi, tacigaba da cewa " kwanaki kasheka ya Asim yaso yi, amma ba wanda ka fadama, abubuwa nawa ka sani wanda baka fadama kowa ba? Kana tunanin in kabar mutanen da sukeyin evil deeds saboda 'yan uwane kana tunanin zasu daina?"

  Yauce rana ta farko dayakeji har cikin jinin jikinsa lalai yarinyar nan ta damu dashi lalai tana sanshi saboda Allah, lalai zata iya komai domin shi.

  Jawota yai a hankali yakai bakinsa cikin nata...  Wata duniyar suka shiga kiss suke deeply wanda gaba d'ayansu wani feelings sukeji wanda su kadai ne sukasan abinda sukeji tundaga kansu har kafafuwansu.........

  Ni dai nace to fa ayi a hankali kar a gangara🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣.

  *#ASHRAFEENAH*
💞

1 comment:

  1. Salam'alaikum, hey pls kinada complete story din "Ni Da Prince" please?? Kindly reply asap, thank you ☺️❣️

    ReplyDelete