Monday, 17 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 47

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *47*

      Su Nafi manya anyi hutun first term da kyar ta yarda tabi su Ferry gida tai hutu, sunyi waec sunyi neco.
Yau sun tashi suna ta shirye shiryen graduation ceremony da za'a musu.

   Zuwan Little biyu d'aya da Mumy d'aya kuma itada driver tana zuwa kawoma Nafi provision.

   Sun tashi a gida ita kadai zataso dan Mumy tanada biki, hakan yasa ta kira Habib ta fad'amai da sauri ya amsa akan zaizo dan kuwa shima yana san ganin Nafi.

  Bayan Habib yazo ne ya karasa gun abokinsa wato Ashraf nan ya sanar dashi inda zasu, shiru Ashraf yai yana tunani tabbas yanajin rashin yarinyar nan har cikin jikinsa, amma zuwansa bazai kawo masa raini ba kuwa??"

  Habib ya dafashi yace " mutumin mu mun wuce."
Da sauri yaji Ashraf yace " Nima zani dan ina ganin bai kamata har ta gama skul banje ba."
Habib yai dariya yace " ashe kasan abinda ya dace, na tabbata da Little ce acan da kaje yafi a irga."

  Ashraf bai amsa mai ba ya tashi ya shiga d'aki, bayan ya shirya ya fito, kallan d'aki Anisa yai wanda ya tabbata bacci take har lokacin aya zari key yai waje.

  Sun tsaya gun ajiye motoci Ashraf yace "ku tafi da motar ku dan ni tawa tafiyar daban sannan banaji zanyi hour d'aya ma acan.

  Sun fito suka fara tafiya, Habib na gaba shi yana baya, a hankali yake tuki yana tunanin me zai ce mata in sun had'u? Wata zuciyar tace " Sannu? Congrat? Hi? 'yan Mata? 'yan makaranta?"

  Kansa ya shafa yace " ke zai sa in fara mata magana? Ita zata gaida ni ai nasan ni kuma sai na amsa."
Yai murmushi ganin komai yazo da sauki.

  Har suka isa yana ta 'yan tunane tunanensa.

  A makaranta kuwa lokacin har an fara programs, su Nafi anshirya cikin kayan 'yan mata atamfa da siket ansha d'auri zasuyi drama ne itace lead, alokacin dasu Ashraf da habib suka iso, daidai nan an fara gabatar da drama din kenan.

   Nafi sam bata kula sun iso ba ta zake sosai tana gudanar da scene dinta na star din cikin dramar, kowa ya nutsu yana kallo Nafi sai burge mutane takeyi da turanci ga iya acting, bawai dan tafi kowa bane aka sata a'a sai dan yanayin yarinyar yanayin Nafine.

   Su Little sai fara'a akeyi, Habib kam kallan Nafi kawai yake yana tsananin mamakin yarinyar da batai primary ba itace take turanci haka??

   Shi kuwa gogan ya kafe kaf, shi bawai turancin bane yafi tada mai hankali ba, yanda ta girma ne yafi bashi mamaki, bawai wani kiba tai ba sai dai cikar mace kam Nafi tayishi a wannan lokacin, ta kara gogewa.

   Sam ya sha'afa cikin tunanin yarinyar jiyai Little na tab'ashi, ya kalleta fuskan nan a d'aure.
  Little tace " Yaya kaga Feena? Dan Allah bata burgeba?"
Ya harareta sannan yace  " ina wani abun birgewa ta fito kandar kandar ko mayafi?"

  Ya fad'a tare da juya kai, Little ta d'an turo baki sannan ta kalli inda Nafi take.
     An gama drama Nafi tun anayi ta hangosu, aikam ana gamawa ta taho gunsu, little ta rike hannunta cikin tsananin farin cikin ganin junansu, Nafi tace " Little!"

   Little ta saki murmushi tare da kara rike hannun Nafi tace " Yar Uwa Congrats."
Nafi tai murmushi sannan ta kalli Habib tace "Ya Habib."
Habib yai murmushi cikin kulawa yace " Princess Congrats tun dazu naketa kallanki sai birgeni kike sake yi."

   Nafi ta maida kallanta kan Ashraf wanda shima kallanta yake tun da tazo gun, kallan sa kawai tai tace " yaya sannu." tana fada ta maida kallanta kan Little.

  Kallan mamaki ya bita dashi, is that all? Abinda ya fad'a kenan a ransa Cikin mamaki, yaya sannu? Ya kara kallanta gani yai sam ma hankalinta baya kansa ransa yakai kololuwar baci.

  Nafi kam hannun Little taja tace " ya Habib muna zuwa."
Sukai gaba, kallo Ashraf ya bita dashi.

  Sukam gun su Ferry suka nufa nan suka cigaba da hira ita kuma Nafi taje ta canza kaya zuwa kayan makaranta tare da sa graduation gown dinta.

  An gama taro suka fito tare da su Habib jikin wata bishiya suka zauna babbar sallaya irin manyan nan suka shimfida suka zauna, Ashraf da Habib kuma suka zauna a kan wani benci dake gun.

  Ashraf ya d'au waya yana dannawa sai dai jefi jefi yana kallan Nafi, haushi duk ya isheshi ganin yanda sam ta d'auke kai daga kansa ko gaidashi batai ba balle ma yasa ran zasu danyi magana.

  Had'e ransa yai tamau ya rike wayarsa kawai yana dannawa, Su Ferry ne suka iso suka.
Nafi ta kallesu tace " wannan  Yayana ne Ya Habib." ta fada tare da nuna Habib, yai murmushi.
Su Ferry suka gaisheshi, ta kalli Ashraf tace " wannan ma yayanane sunanshi Ya Ashraf." tafad'a tare da nuna Ashraf, Ashraf ya sake hade fuska wato shi da Habib duk matsayinsu d'aya take nufi ko me? Yayana? Ya Habib? Ya Ashraf?"

  Wani mugun kallo ya bita dashi, Nafi kam d'auke kai tai tare da kallan Ferry.
  Yana kallo suka zauna suna hira sam ma ko kallan inda yake batayi.

  Ashraf kam ya cika fam ko hira da Habib yake neman jansa dashi ya kasa biyemai.

  Suna nan a zaune suna hira sai ga wani saurayi nan ya iso kana ganinsa kasan yayan Ferry ne dan suna kama sosai, yana isowa ya kalli Nafi sannan yasa hannu a saitin inda zuciyarsa take yace " Feenah zuciyata za za za......"
Yai kamar irin numfashin na neman yankewa, Ferry da Nafi sukai dariya, Nafi tace " Ya Nabil zaka fara ko?"
Little ta kallesu tace au wasa yake?"

  Nabil yai murmushi sannan ya kalli Little yace " Yar uwar mu."
Little ta zaro ido dan mamaki, yacigaba " ke yar uwar Feena ce kinga kuwa yar uwa tace."
Habib yai dariya yace " Lalai guy din nan kana da abin dariya."

Nabil ya cigana da magana yana kallan Little yace " Little in baki taimaken ba kinsa kanwarki ta soni ba inaji zakuzo jana'iza ta."

  Nafi da Ferry suka sake dariya, Ashraf ransa ya kara b'aci a zuciye ya mike ya karasa gun motarsa ya shiga, kansa ya kwantar akan kujera zuciyarsa duk ta gama kuluwa haka take ma maza dariya?"
Kallan gun yai ya d'auka zai ga tana ko kallan inda yake sai dai abin haushi hira suke cikin annashuwa da Nabil.
Motarsa ya tada, Nafi ta kalli gun da sauri zuciyarta duk ta fara sanyi anya kuwa wannan hanyar itace? Ferry ce ta mintsineta a cinya wanda hakan yasa ta daina kallan motar sai dai zuciyarta duk ta karaya.

  Little ce ta kalli Habib tace " Ya Habib ina yaya zaije?"
  Habib ya girgiza kai sannan yace "wlh bansani ba nima."
Ashraf har ya fara tafiya yaga bazai iya jurewa ba a zuciye ya fito inda suke hannu yasa ya fizgo Nafi dake zaune suna barkwanci da Nabil.
  Nafi ta kalleshi, fuskar sa a had'e yace " mike."

A hankali ta mike, yai gaba ta bi bayansa, jikin mota ta tsaya, ya kalleta yace " shiga."

  Fuska itama ta had'e tace " ina?"
Yace " za ki shiga ko na shigar dake da kaina?

  Kallan mutanen gun tai ta had'e rai sannan ta shiga fuska a hade.
Shima ya shiga, glass din motar ya zuge, ya maida kallansa kanta yace " i am a joke?"

  Ta kalleshi itama tace " me nai kuma?"

  Me kikai?tambaya ta ma kike?

  Ta turo baki tace " to ni menai? Ka fad'amin"

  Ashraf ya kura mata ido cikin takaici yace " kinasan kice min bakisan me kika min ba? Sannan ko kunya ma ki fito gaban maza kadar kadar ko mayafi wai ke a dole kina drama ko?"

  Nafi bata amsa ba sai baki data turo ya kara cewa " shi kuma wancan waye? Meye hadinki dashi zaki zauna kina washe mai baki?"

  Nafi ta kalleshi sannan tace " Mun saba dashi ne fa."
What?kun saba? Meye shi a gunki?"
Nafi ta juya kai tare da yin dan yin kunkuni, yace "me kike cewa?"
Kallansa tai tace "jirana akeyi nabar mutane."
Zai sake magana yaga ta bud'e kofa kallan mamaki ya bita dashi......

  A zuciye yaja motarsa da gudu yai waje, Nafi tabi bayan motar da kallo jikinta duk yai sanyi, idanunta suka ciciko, Ferry ce ta matso ta dafata suka kalli juna sukai murmushi.


  *THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment