*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*40*
Nafi ta mike a zabure tace " Haka suka ce? Wow! Lalai na jinjina ma matar Yaya." ta fad'a tare da tafa hannunta.
Little tai dan dariya tace " hmm dan ma Ya Ashraf suka samu? "
Nafi ta koma ta zauna tare da jan tsaki tace " Ni fa gani nake Yaya nada zafi amma baya iya wani abun kuzo mu gani. "
Little tai murmushi tace " Nafi bakisan halin Yaya bane, yanada masifar zuciya da taurin kai abu d'aya ne yake hanashi yin komai a gidan nan. "
Da mamaki Nafi ta kalli Little tace " me kenan? "
"Mumy. " Little ta fad'a fuskarta d'auke da damuwa, sannan tacigaba "Nafi yau zan fad'a miki tarihin gidan nan. "
Da jin haka Nafi ta gyara zama cikin zukud'in san taji meke faruwa.
*TUNA BAYA.*
" Kakan Ashraf wato Sale ya kasance mutumin wani kauye ne dake garin Kila a karkashin jahar Jigawa, ya taso cikin wahala kasancewar mahaifinsa bashida hali sannan shi kad'ai ne namiji kuma babba agun mahaifinsa.
Wahala kam na rayuwa ya shata, dan mahaifinsa ba cikaken lafiya gareshi ba, duk wani arzikin gona iin ya samu akan kannensa da iyayensa yake tafiya, hatta kayan da yake sawa sun jeme saboda tsabar wahala.
Sam bai taba tunanin aure ba ganin nauyin dake gabansa sun mai yawa, har Allah ya kawo kanwar mahaifiyarsa ita da 'yarta sukazo hutu gidan.
Tunda Sale ya ganta yaji ya kamu da santa sai dai ganin ita daga birni take yasa ya kunshe abinda ke ransa.
Fanna wanda take 'yar kanwa ce ga mahaifiyar Sale a garin maiduguri suke, yarinya ce wacce ba ruwanta , tunda tazo gidan ta lura Sale kaya d'aya yake maimaitawa sannan sam ta kula baya zaka kullum aiki yakeyi.
Ranar yazo fita ta d'au mayafinta tace " zata rakashi. "
Ba musu suka fita tare, wannan fitar itace mafarin soyayya mai karfi data kullu a tsakaninsu, iyayenta sunyi takaici sun kuma so hanata wannan auren ganin ba komai Sale ke da shi ba.
Fanna ta dage wanda hakan ya kaisu ga aure.
Nan aka gyara mata b'angare anan cikin gida aka mata jere.
Shekararsu d'aya da aure Allah ya azurtata da d'a namiji sai dai tana haifarsa Allah ya karb'i ranta.
Aka sama yaron Abbas, Sale yayi kuka sam rayuwarsa ta canza kullum yana tare da d'ansa ko gona zaiji haka yake d'aukansa sutafi.
Gulmar da ake a kauyen ne yasa mahaifin sa ya d'aura mai aure da Ruma 'yar gidan babban wansu.
Ruma na san Sale sosai sai dai shi d'ansa ne kawai a ransa, wanda hakan ne yasa Ruma ta d'au soyayya itama tasama Abbas.
Ganin yanda takesan d'ansa ne yasa shima ya fara kulata har Allah ya bata ciki ta haifi namiji itama shine aka samai Mansir.
Sun taso cikin kulawar iyaye sai dai kowa yasan sanda Sale yakema Abbas wanda sam baya iya b'oye hakan koda kuwa a gaban waye.
Abbas na shekara 8, shikuma Mansir na shekara 5 Allah yama Sale rasuwa.
Wannan mutuwa ta girgiza kowa, iyayen Fanna sukazo akan a basu Abbas ya zauna a gunsu.
Sai dai Abbas ya tubure akan baza'a rabashi da kaninsa ba, hakanan dole suka had'a da Mansir suka taho maiduguru.
A can kuwa kowa yafi nuna kulawa da damuwarsa akan Abbas, dan yana isa garin aka sashi a makaranta, Abbas na kokarin ganin duk abinda aka mai an ma Mansir sai dai duk yanda yaso abu ya faskara.
Makarantar kud'i aka sashi aka sa Mansir ta government, sannan kafin asai ma mansir kaya d'aya to Abbas ya tara 5 dan 'yan uwa ma na aikomai, wani sa'in haka zai dau saban kayansa yaba kaninsa.
Haka suka taso cikin wannan rayuwa, Mansir yana tsananin kishin kauna da Abbas yake samu ta ko ina, a haka har Abbas ya gams karatunsa ya tafi Buk a kano.
Mansir kuma yana aji biyar.
Mansir tun yana Js1 ya fara san wata yarinya wacce akama mahaifinta transfer daga kano zuwa maiduguri.
Yana tsananin santa sai dai ganin yarinyar bata Shiga harkar kowa yasa ya kasa sanar mata, har shima ya gama secondary ya fara poly dake nan garin Maiduguri.
A kullum ya taso daga makaranta sai ya biya ta islamiyar su yarinyar wato Ruma, haka zai tabin bayanta har sai sunje gida ba tare da saninta ba.
Kwatsam wani hutu Abbas yazo gida lokacin yana level 4 yaga Ruma, ba tare da gazawa ba yaje gidansu ya sanar da ita soyayarsa, cikin sa'a ta amsa masa, bai sanar da kowa ba saboda Ruma tace bataso a sani saboda mahaifinta yace karatu kawai yakeso.
Soyayya mai zafin gaske ce ta shiga tsakanin masoyan biyu, a lokacin da Abbas ya sanar da Mansir akwai wacce yake so shima Mansir din yacemai akwai wacce yakeso sai dai shi kunyar sanar da ita yake.
Abbas yai dariya sannan yace " Kanina ai yanzu da zafi zafi ake bugan kirji karka kuskura ka jinkirta soyayyarks kar a maka shigo shigo.... "
Wannan kalamai na yayansa sun karfafamai gwiwa bayan Abbas yabar gida Mansir ya bugi kirji yaje gidan su Ruma.
Sun gaisa kafin cikin fara'a zai fara koro mata abinda ke ransa ta katseshi da cewa " Mansir ko? Kanin Abbas. "
Mansir ya washa baki yace " Eh nine.
Ruma ta d'anyi kasa dakai sannan tace "Ai koka yai? "
Cikin mamaki Mansir yace "a'a. "
Ta d'ago sannan tace " ba wani nan, yace bazai fad'ama kowa muna soyayya ba amma wai bazai min alkawarin kin fadama ba. "
Gaba Mansir ne ya fad'i yace " Kinsan yaya ai. "
Tai murmushi tace " Yana sanka dayawa komai sai ya ambaceka. "
Mansir kam jiyai kafafuwansa suna neman Kasa d'aukansa hakan yasa yace mata kansa na ciwo ya tafi.
Mansir ya rame, sam karatun ma ya kasayi, a lokacin ne Abbas ya gama nashi karatun, yama Mansir fada sosai ganin takardunsa ba abin arziki, duk yanda yai akan ya sanar dashi matsalarsa ya ki.
Hakan yasa ya zauna da kansa yake koyamai karatu.
Sai dai abin mamaki ya kula yanzu sam Mansir baya yarda suyi wata magana mai tsawo.
Hankalin Abbas ya tashi, yana tsakiyar wannan kangi mahaifin Ruma aka maidashi kano, sannan mahaifinta yace ta fito da miji.
Ruma kam kai tsaye ta gabatar da Abbas, nan aka kai kud'i tare da sa rana."
Little tai ajiyar zuciya tare da kallan Nafi wacce tai shiru tana sauraranta, tace " Kinsan su waye mutanen nan uku?
Nafi tace " Abbas mahaifin Yaya, Mansir kuma Abban ki ko? "
Little ta d'aga kai sannan tace " Ruma fa? "
Idanu Nafi ta zaro cikin shakkun abinda yazo ranta tace " Don't tell me???"
Kai Little ta d'aga tace " Yes! Mumy ce. "
Nafi ta zaro ido sosai cikin mamaki, Little tai yake sannan tace " wannan shine mafarin komai dake faruwa. "
Nafi kam baki ta saki tana mamaki wannan sarkakiyar.....
Little ta nisa sannan ta cigaba..............
*THE INNOCENT TEAM*
Wow what a nice story, pls continue.
ReplyDeleteThanks. We always appreciate your efforts.
ReplyDeletePls aturo mana karaken ni da Prince, da Ilham Pleeeeeease
ReplyDelete