Thursday, 13 July 2017

Zuciya.....Kowa da irin tasa 45

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *45*

  Ranta yakai koluluwa gun b'aci Ashraf bai tsamani ba kawai yaga ta bud'e motar ta fita, ga ruwa ake sosai, da sauri shima ya bud'e kofa ya fita, tafiya kawai take tsabar ruwa batama san ina take sa kafarta ba, Ashraf ya hanzarta ya riko hannunta.

   Kallansa tai sannan ta fizge hannunta da karfe ta nemi ci gaba da tafiya, hannayensa biyu yasa ya rike kafad'arta ya juyo da ita saitinsa yace " Nafisa!!" ya fad'a tare da jijiga mata kafad'a, Nafi ta shiga neman kwace jikinta ganin yanda ruwa ke dukansu gashi da alama taurin kai take nemanyi yasa kawai ya d'agata cak yai mota da ita ahakan ma saj wutsul wutsul take, ya bud'e mota ya sata sannan ya zaga  da sauri ya shiga tare da sama motar lock.

  Nafi ta juya kanta gefe, hannunta ya kamo yace " menene wai?kanki d'aya kuwa?"
  Ta kalleshi da idanunta da suka ciciko cikin wani irin murya ta kalleshi tare da cewa " yaya ni nace ka aureni?"
 Kallan mamaki ya mata, ta share hawayenta duk da tasan abanza dan kuwa hawayen sai ma kara zubowa takeyi, ta kalleshi sannan ta cigaba " Yaya ni bw mutum bace?dutse ce ni ko kuwa?"
 Kallanta kawai yake sam ya kasa magana, hawayen da takeyi da kalamanta sune kawai ke ratsa shi, ta kara share wasu kwallan sannan ta cigaba " ka tab'a ganin inda mace a ranar da aka daura mata aure miji yake mata zancen saki? Ka taba tunanin yanda wannan matar zataji duk da yarintar dake damunta a lokacin??"

   Ashraf jikinsa ya mutu sosai, Nafi ta sake goge kwallar sannan tace " ka bani takarda ta yanzu inaji shine kawai abinda ya kamata, a gun iyaye da mutanen garinmu ne kawai kake mijina waya san abinda ke tsakanin mu? Ni kaina mantawa nake da auren ka akaina, baka tunanin halin da zan fad'a idan na fara kula wani?ku kuwa ba zunubi na aikata ba in nai hakan?"

  Ashraf ya kara rike hannunta yace " Nafisa!"

  Hannunta ta kwace ta kalleshi cikin idanunta da suke zubo da kwalla tace " na gode sosai daka taimakeni, ka kula dani ka kuma sani a makaranta sai dai ina ganin lokaci yayi da nima nake bukatar zuciyata ta huta da kokwanton ni matar aurece ko bazawara ko kuwa budurwa?ka bani takardata gobe in koma mahaifata."

   Idanu Ashraf ya runtse sannan ya bud'esu a hankali ganin yanda take kuka bai san sanda ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, kokarin kwacewa ta shigayi sai dai ya riketa sosai ganin ta kasa kwacewa yasa ta rikeshi itama tare da cigaba da kuka, jikinsu ya jike shakaf.

  Kuka take sosai wanda ke taba duk wani lungu da sako na jikinsa, kanta ta kwantar a wuyansa a lokacin da ta fara tsagaitawa da kukan, jin jikinta yai ya fara d'aukan zafi ya daure ya d'agata sannan ya riko hannunta ya shiga hura hannunta da bakinsa yana murzasu, kallansa kawai takeyi tanajin wani irin sabon kaunarsa na ratsata, Why?? Meyasa ita da takesan ta daina sanshi amma takejin haka.

   Ya kalleta yace " zazzabi ke neman kamaki, me yasa bazaki min magana ba kika shiga ruwa?"

  Ta kifta ido sannan tace " yaya ka tab'a tunanin ya nakeji inkamin zancen saki bayan ban tabbatar da matsayin aurena ba ma? "
 
  Ashraf ya kalli yanda jikinta yai sharaf sannan ya kalli idanunta cikin dan fada fada yace " ina miki zancen jikinki kinamin zancen abinda ba shiba?"

   Idanu ta kafeshi dashi, ya kalleta shima, kallan juna suka shigayi dukansu wani abu na ratsasu, Nafi ta daure ta d'auke idanta ta juyar da kanta jikin window, Ashraf ya sa hannu ya rikota tare da jawota kusa dashi.

  Idanun Nafi ne suka fifito ya kalleta yace " kalleni.!
 A hankali ta d'ago tana kallanshi ta maida kanta kasa, jikinta ne ya mutu ganin ya sa kanta akan kafadarsa yace " ki zauna a haka na yan mintina."

   Why? Tafad'a a hankali yai gyaran murya yace " zai taimakawa jikinki dake neman kamuwa da zazzabi."
  Tai murmushi batace komai ba, ya sake gyaran murya yace " ba kuma cewa nai kiyi hakan ba da wani."
  Tace " me yasa? Naga taimako ne."
 Ya harareta yace " ni ai haryanzu akwai aurena akanki."
Tad'an tab'e baki tace " auren da ni kaina ban tabatar ba."
 
Me kikeso ki tabbatar? Idanu ta rufe kamar mai bacci dan batada amsa.
Ya kalleta sannan yai murmushi.

  Ganin ruwa ya fara d'aukewa yasa ya gyara mata kwanciya zuwa kujerarta duk da yasan ba Bacci take ba, sannan ya tada mota ya jata a hankali.

   Nafi kam juyawa tai tana murmushi lalai wannan rana ta shiga cikin tarihin rayuwarta ba wai cewa yai yana santa ba sai dai ta rasa dalilin farincikin nata.

  Sun isa gida sannan yai parking yasa hannu a wuyanta yaji dumin kadan ne sannan ya kalleta yace " mai baccin karya ki tashi ki shiga ciki ki dan zuba ruwan zafi a jikinki kisa kaya mai dan nauyi."

  Kai ta d'aga ba tare da ya juyo ba, sannan tai sumsum tai waje ya bita da murmushi.
 Yasa ankai mata kayanta sannan ya wuce b'angarensa yai wanka shima da ruwan zafi sannan yasa kaya ya kwanta akan gado tare da dora hannunsa akan goshinsa, meke damunshi? Me yasa yake abu kamar ba shi ba, me yasa yake yawan murmushi tare da yin abubuwan da bai saba ba in yana tare da yarinyar nan?

   Wata zuciyar tace badai kamuwa kafarayi da santa ba? Kai ya girgiza da sauri yace " No way, how can i...."

   Shiru yai yana tuno sanda ta kwanta ajikinsa tana kuka, murmushi ya saki tare da lumshe ido......

   Nafi kam haka taitayin komai cikin farin ciki har Little ta ke tambayarta yau meya same ta haka?Nafi kawai sai dai tai dariya..

  Washegari litinin da safe Ashraf ya shirya ya tafi gun aiki sabosa sunada Meeting yau ranace babba agunsa don project din da yai kusan wata 6 yana planning yau zaiyi presenting dinsa a gaban directors na company din.

  Karfe goma ne presentation din dan haka ya isa gun karfe 9 da kansa ya Shiga gyara gun har 10 tai, mamaki ne ya kashi ganin har 10 da rabi ba kowa a gun sai shi kad'ai nan ya fito ya fara dan zazagawa, wani member na team dinsa ya kira yace " ya dubamai ko ancanza lokaci ne."

  Yana nan a tsaye sai ga Mansir ya taho, ya karaso inda Ashraf yake yace " har an fara?"
  Ashraf yai kasa dakai cikin rashin jin dadi yace " ba wanda yazo shiyasa nake tunanin ko ancanza time ne."

  Kawubya d'an nuna rashin jin dadinsa a fili sannan ya d'aga waya ya kira Secretary dinsa, ko me ya cemai ya kashe tare da kallan Ashraf yace " Ashraf ance project dinka plagiarism ne."
 Cikin tsananin mamaki Ashraf yace " Ban gane ba?"
  Kawu yace haka aka sanar da directors din ciki kuwa harda members na team dinka sannan project din har anyi lunching dinsa ma a comapny din da muke rivals." yana kai nan yad'an bubuga kafadar Ashraf sannan ya juya ya tafi.

   Da kallo Ashraf ya bishi ya saki wani murmushin takaici a ransa yace " ko kuma ka d'auka ka basu ba? Kana tsoron hakan zai sa mutane suyi acknowledging dina."

  Ya runtse ido saboda wani takaici da ya kamashi, yai kwafa tare da zubar da takardun yai waje.

   Mota ya shiga ransa yakai kululuwar b'aci ya dage ya daki sityarin mota da hannunsa tare da kwantar da kanaa jikin kujera ya saki wani huccin takaici.

   Little ce ta kirashi sai data kusa katsewa ya d'aga sai dai muryar Nafi yaji tace " Yaya ina kwana?"
 Ya amsa a hankali, tace " driver din yazo zamu tafi gashi bakanan bare muyi sallama."
  Yace " da inzaki tafi makarantar sai kinyi sallama dani?"

  Mamaki ya kamata tace "Yaya gani nai...."
 Katse wayar yai sannan ya kasheta gaba d'aya ya runtse idansa da karfi zuciyarsa na kara tafasa.

  Nafi kam mamaki ne ya kamata, cikin takaici ta shirya da taso in sukai waya yace ta bari ba yau ba sai dai yanda ya amsa mata yasa taji batasan zaman gidan ma sam a wannan lokacin, ta kalli Little ta mika mata wayar Alamin sannan tace " ki bashi wayarsa kicemai na koma skul inda rabon mu sake had'uwa to inkuma babu Allah ya hada fuskokinmu a aljanna."

  Little ta kalleta fuska a hade tace " wai dan Allah bazaki hakura da tafiyar nan ba?"
  Nafi ta girgiza kai cikin takaici tace " karki damu little kwana nawa ne?"
 Little ta harareta sannan tace " wani irin sako ne wannan haka kikeso in fad'ama al'amin din?"
 Tace "eh, bari naje nama Mumy sallama."

  Sunyi sallama da Mumy, sannam ta shiga mota ranta duk ba dadi suka tafi.....

  *ILYSM MY FANS*

    *THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment