*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
_Godiya gareku 'yan Nice Hausa Novel musamman hajiya admin Aisha Sabi'u Mohd....ILYSM😍_
{ *50*}
Nafi kam a falo ta zauna ta dafa kanta itakam Allah ya yaye mata wannan abun dan bata ganin akwai riba a cikin wannan san da takema Ashraf.
Kwanciya tai daga nan bacci yai gaba da ita akan kujerar.
Sai la'asar ta tashi tana shiga taga Little ma bacci take nan tai sallah sannan ta tasheta itama tai, kitchen ta nufa dan kara samun fasaha akan girki.
Sai 6 ta fito tana shiga bayan sunyi magrib aka aiko wai ana sallama da ita, mamaki ya kamata ta tsare Little da ido, Little tace " ba Alamin bane Allah dan shi baima san kin dawo ba."
Nafi tace "to waye??"
Little tai murmushi tace "ki shirya sai ki dubo mana."
Harararta Nafi tai tace "wani shiri kuma? Bansan waye ba kawai sai in hau kwalliya sai kace mai neman saurayi?"
Little ta sa dariya tace " to da mecece?ai duk budurwa nema take har sai ta samu tsayaye."
Nafi ta tabe baki ta zari mayafi tai gaba Little na tsokanarta.
Waje ta fita mota d'aya ce a gun hakan yasa ta tsaya daga dan nesa tana tunanin karasawa, fitowa yai tare da zama a saman motar yace "My Feena ko sai na zo da kaina?"
Jin muryar Nabil yasa tai murmushi sannan ta karasa, kallansa tai cikin zolaya tace " da alama rashina ya hanaka sukuni?"
Ya dafa kai yace "Feenah taba kiji inaji zazzabi ne ke neman kamani saboda missng dinki."
Tai dariya tace "Ya Nabil to ya? Nayi mamakin ganinka a daren nan."
Ya kalli agogo yace " ko isha'i batai ba shine dare?"
Tai dariya sannan tace "Ina Aminiya?"
"Tana gida nima wucewa nazo yi nace bari na tsaya mu gaisa."
Murmushi ta sakeyi tace "aikam na gode."
Ya kalli gidan yace "dama a gidan Marigayi Abbas kike?"
Kallan mamaki tamai tace "kasanshi ne?"
Dariya yai yace "ina fa mutumin daya rasu kafin muyi wayau."
Tace "then?"
Yace " A company dinsa dai Dad yai aiki."
Cikin mamaki tace haba?
Ya daga mata kai sannan yace "Amma tun bayan rasuwarsa shima ya ajiye aikin."
Nafi tace "me yasa?"
Iska ya dan tara a bakinsa sannan ya furzar yace "bansan dalili ba."
Kallo ta tsareshi dashi tace " Kace wallahi."
Yai murmushi yace " me nene matsayinki a gidan?"
Ta kalli gidan sannan tace "nima bansani ba ganinan ne dai kawai."
Dariya yasa yace "ban gane ba."
Tace Wallahi dagaske."
Kallan mamaki ya mata yace " kiyi a hankali to da irin wannan gidan manakisa da sharrinsu yawa gareshi, dan mutuwar Abbas din........"
Bakinsa ya guntse jin yana shirin yin baran barama, Nafi ta kalleshi fuska dauke da mamaki tace " Me? Akwai sa hannu ko me?"
Juyar dakai yai yace " Hmm yaushe zakizo gida?"
Tace "Ya Nabil?"
Kallan gate yai yace "ga wani can ya fito da mota."
Nafi ta kalli gun, motar Ashraf ce idanunta ta kaida kan Nabil tace " Ya Nabil dan Allah me ka sani??"
Kifta ido yai yace "bazai miki fada ba?"
Hade rai tai tace " akan me kenan?"
Zaiyi magana yaga an dallesu da fitilar mota wanda sai da Nafi ta juya, ta tabbata so yake yaga waye, shiyasa tana juyawa ta maida kanta gun Nabil.
Ashraf kam wanda suka fito shida Anisa.
Ya tsaida mota batare da ya kashe fitilar ba, Anisa ta kalleshi ya had'e rai tare da kafe Nafi da ido, mamaki ya kamata.
Shikam Nabil kallan Nafi yai yace " Feenah da alama ke ake jira kar inja a miki fada bari na tafi."
Da sauri tace a'a yaya taimakamin karka tafi please.
Yace "Ba kya tsoro?"
Kallansa tai fuska dauke da murmushi tace " mu shiga motarka mudanyi gaba please, sannan banaji zan barka ka tafi baka karasa fadar abinda zaka fada dazu ba."
Kallan mamaki ya mata, ta shagwabe fuska tace "please "
Sauka yai sannan ya zagaya ya bud'e mata mota ta shiga sannan shima ya shiga tare da tada mota.
Anisa ta kalli Ashraf tace "wai me mukeyi anan ne?"
Bai ma san tanayi ba dan wani irin abu ne ya tasomai yana ganin sun hau kan titi ai kuwa shima ya taho da gudu da mota ya sha gabansu saura kiris motoci biyun su bigi juna, Nafi kam da Anisa duk sun runtse ido kowa na tsoron abinda zai faru shikanshi Nabil ya tsorata, Ashraf a zuciye ya kashe mota sannan ya fito ko kofa bai rufe ba yazo Kofar da Nafi take ya bud'e da karfinsa.
D'agowa tai cikin tsoro tana kallan idanunsa da suka kada sukai ja sai hucci kawai da yakeyi, hannu yasa ya fizgota da karfi, Anisa ganin haka yasa ta fito tare da shan gabansu tace "Ya Ashraf me kakeyi hakan? Ina zaka bayan kasan unguwa zamu?"
Kallanta yai cikin idanunsa da sukai ja bai bata amsa ba kawai ya zagaya ta gefe ya sa Nafi a bayan motarsa ya shiga ba tare da ya kuma kallan Anisa ba yai reverse sannan ya ja motar a zuciye.
Nabil kam wannan abu ya d'aure mai kai shima a hankali yaja tasa motar yai gaba yabar Anisa wacce ta tsaya kamar gunki.
Ta dade agun kafin ta koma gida, gun Umma ta nufa tai sa'a Asim nanan nan ta zayyane musu abinda akai tare da fashewa da wani irin kuka.
Umma ta mike tsaye tace " Asim dole ne musan abinyi dan nikam na gaji da wulakancin wannan dan marasa tarbiyar."
Asim a zuciye yai waje ya nufi bangaren mahaifinsa......
Shikam Ashraf gudu kawau yakeyi, Nafi kam tayi shiru a baya sai dai har yanzu tsoron abinda Ashraf yai takeyi, gashi sai gudu yakeyi ga dare.
Addu'a kawai take a ranta, can karshen titin Naibawa ya tsaya, wajen fly over sannan yai parking ya fito tare da bud'e kofar Nafi.
Ta kalleshi cikin tsoro.
"Fito!"
Abinda taji yace kenan, ta danne tsoro sannan tace "in fito inyi me??"
"What?" ya fada yana kara kallanta.
Ta murguda bakinta tace " Haka kawai ka jawoni ka kawoni nan sannan in fito inyi me?"
Kallan mamaki ya mata tai saurin kallan gefe, shiga yai kusa da ita tai saurin matsawa tare da harde hannayenta ta maida kallanta gefe.
"Waye waccan d'in?"
Tace wa kenan?
"tambaya ma kike? Wanda yake neman sa ki a mota ku tafi wani guri a daren nan."
Baki ta turo tace "Wani ne."
Yace "wani? Bakida hankaline bakisan mutum ba kike neman shga motarsa? In ya lalataki fa?"
Dariyar da ta nemi taho mata ta guntse tace " to meye a ciki? Tunda so na yake?"
Me? Bakida hankali ne?" ya fada a zuciye, ta kalleshi tace " ni so nake ma in aureshi dan na gaji da zama a inda na sona ake ba."
" who said that?" shikansa baisan sanda ya fadi hakan ba.
Kallan sa tai fuskarta da alamar tambaya, ya juya kai sannan yace " karki kuskura inkara ganinki da wani namijin balle har ki samu mai dariya ko shiga motarsa."
Tace" Akan me?"
Yace " Tambaya ma kike? So kike wani abu ya sameki ace nine?"
Haushi ya kamata ba haka taso ji ba, ta juya kanta tace " bazan iya rabuwa da shi ba."
Hannu yasa ya rike kafadarta da karfi tare da juyo da ita saitinsa, yace " ni kike fadawa haka?"
Baki ta turo batace komai ba, kallanta ya tsaya yi, batai auni ba taji bakinta cikin nasa, nan ta fara kokarin kwacewa sai dai ya riketa da kyau tun tana kokarin kwacewa har tai la'asar....Wani sakon ni suke ba juna wanda su kadai suka san ma'a narsa, sun dade sosai a haka sannan a hankali suka saki juna, idanuwansu dake lumshe suka bud'e a hankali.
Idanunta suka ciciko cikin sanyin murya tace " Yaya why are u doing this to me?"
Jawota yai jikinsa ya rungume ta yace " Nafeesa ni kaina bansan me nakeyi ba."
Tace " ba so na kake ba me yasa kakeyin hakan to?"
Ya kara kankameta yace " Na rasa me ke damuna, ni kaina abin na damuna."
Ta dago da jikinta tace " karka sake tabani har sai ka san abinda ke damunka."
Kallan mamaki ya mata yace " Ke halal dina ce bawai haram dina ba."
Wani murmushin takaici tai tace " Halal? Since when did i became your halal?"
Yace " What?"
Ta rufe ido sannan ta bud'e tace " Halal din da ba wanda ya sani? Halal din da ni kaina ban san halal bane? Halal din da kake tsoron kar mutane su sani? Halal din da kai kanka baka tabbatar dashi ba?"
Kallanta yai sai dai kalamanta sunsa jikinsa yai sanyi, ta sake murmushin takaici tace " ko ma meke damunka nidai karka kara tabani sai ka tabbatar dashi sannan sai na yarda da hakan."
Tana kai nan ta juya kanta tare da share kwallar da ta zubo mata.
Jiki a sanyaye ya bud'e motar yai waje ya koma mazauninsa ya zauna a hankali ya tashi motar sukai gaba.
Yana kallanta ta madubi jefi jefi tana share hawayenta, ya sani sarai shine silar kukan ta, me yasa yake zama dalilin hawayen ta? Why did he always cause her pain?"
Jiyai gaba daya jikinsa yai sanyi jiyake kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta, bayaso ko kadan yaga tana kuka dan har zuciyarshi abin ke tabawa.......
*#ASHRAFEENAH TEAM*
No comments:
Post a Comment