Tuesday, 25 July 2017

Zuciya...Kowa da irin tasa 53

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *53*

  *Wannan shafin naki ne Billy Galadanci*......😍😍😍

    Idanu Ashraf ya zaro cikin mamaki ya nunashi yace "Dan Littin Gayu?"

Keya d'an Litti ya sosa yace " Ashaf nine dai kam." yai maganar yana washe  baki.

  Dariya sukama juna ganin za'a bada hannu yasa Ashraf yace, shiga muje.

    Da sauri dan litti ya shige bakin nan yaki rufuwa.

  Gefen titi suka gangara Ashraf yai parking tare da kallan guy din wanda sai washema Ashraf baki yake, Ashraf yai murmushi yace "Dan Littin Gayu."

  Dan Litti yai dariya yace "inafa gayu? Gayun daya kusan kaini prison."

  Ashraf bai san sanda dariya ta kwacemai ba yace " Ah haba? Ni ai bantaba tsammanin ganinka a nan ba."

  Nan D'an litti ya shiga bashi labarin zuwansu da su Datti da kulleshin da akai, da zamansa a kachako, har zuwa komawarsa kauyensu da abinda Datti yai.

  Ashraf yai murmushi yace " Gaskiya kasha wahala gun nemana, ko da yake alheri ya zamarma tunda gashi nan ai ka canza."

  Dan litti yai dariya, Ashraf ya cigaba " Shi kuma wannan mahaifin Nafin....."
Sai kuma yai shiru.

Dan litti yace " Ai datti ni har yau Allah bai hadani da mutum irinsa ba."

   Shiru Ashraf yai, tausayin Nafi na kara ratsashi.

  Ya juyo ya kalli Dan Litti yace " yanzu ina zaka?"

  Dan Litti yace "mun shigo kano ne dama kawai yawo, nida abokaina."

  Ashraf yai murmushi yace " Dan Litti kenan, kace yanzu an daina sakar mana turanci."

  Kansa ya kara sosa wa yace " inafa?inasanyi ina tsoron abinda zai jamin."

  Sukai dariya a tare, Ashraf yace "ba matsala mu tafi gidan mu."

  Dadi ya kama Dan Litti shi dama burinsa ya gansa da Ashaf.

     Nafi kam yau gidan duk ya isheta, ga Little bata kulata ba tai wanka tai tafiyarta makaranta, gashi bata isa ko fita tai ba, yunwa ma takeji amma saboda gudun rigima ta kasa fita.

Mikewa tai ta shirya ta duba jakarta taga d'ari biyar ta fito ta hau adaidaita tamai kwatancen gidansu Ferry.

   Tai sa'a suna nan aikam suna haduwa hira ta barke, anan taci abinci suka cigaba da hirarsu.

   Duk yanda sukai akan ta fada musu meya sameta a fuska taki fada cewa kawai tai faduwa tai, sai dai su sunsan ba faduwa bace Sai dai ba yanda zasuyi.

*********

  Ashraf sun isa gida yai parking din motarsa sannan ya kalli Dan litti wanda ya saki baki, hanci, ido duk yana kallab tangamemen gidan dai bai taba gani ba a tsawon rayuwarsa.

  Ashraf ya sa hannu ya zunguroshi, Dan Litti yai firgigitbya kalleshi.

  Fito mu shiga ko?"

   A hankali Ashraf ya fito sai kara kallan gidan yakeyi, Ashraf yai gaba, nan yabi bayansa yana tafe yana kalle kalle.

  Bangaren Ashraf suka nufa, bayan ya bud'e ya kalli Dan Litti yace 'shiga muje ko?"

  Kai dan litti ya girgiza yace "a'a kadai fara shiga."

  Ashraf yai murmushi sannan ya shiga, nan Dan Litti ya dan dosana kafarsa a hankali sannan ya shiga, kallan Ashraf yai yace " Ashaf lalai kana bawa gayu kunya, wannan duk haduwarsu suka ganka ko motarka ko gidanka ai dole su shiga hankalinsu kunya ta kamasu."

  Ashraf bai san Sanda dariya ta zo mai ba yace " Lalai Dan Litti, kai dai baka rabuwa da shirme, shigo insa a kawo ma abinci."

  Nan ya zauna a tare da kara kallan falon, Ashraf kuma yai ciki.

  Dariya kawai dan litti ya shiha yi ba kakautawa wanda yasa Ashraf ya fito da sauri, a kasa yaganshi yana dariya, cikin mamaki yace " ya akai?"

  Dan litti ba tare da ya daina dariya ba yace "lalai Datti zai ci Kw*******"

  Ya karasa yana dariya, kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, bayan dan litti ya gama dariyarsa ne idanunsa suka fada kan hoton Ashraf da Anisa, nan yace "KAI! Kai jama'a." da karfi yai maganar wanda yasa Ashraf ya sake fitowa ya kalleshi yace " ya akai?"

  Dan litti yace " Tab, Ashaf amma wannan matar taka tayi, da alama wannan yarinya mai wanke wanke ta koma, yo dama ina kai ina ita?."

  Ashraf ya dan daure fuska zaiyi magana yaji Dan litti ya sake cewa " lalai Datti zai suma duk randa ya shigo gidan nan." ya kara kwashewa da dariya.

  Kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, waya ya daga ya kira Little yace " ki sa Nafisa ta kawo min abinci."

  Little wacce tun dazu take neman Nafi tace "yaya wlh nima nemanta nakeyi."

  Cikin rashin fahimta yace "kamar ya kenan?"

   Tace "wlh na dawo daga makaranta naga batannan."

  Cikin fada yace "to ija taje?"

  A tsorace Little tace "wlh bansani ba yaya "

  Tsaki yaja sannan ya kashe wayar, ya zauna a bakin gado, haushinsa da takaicinsa d'aya da ko waya bai sai mata ba, ya rufe ido cikin takaicin kansa yace " why?"

  Yanzu tayaya zai soma nemanta?to inama ta sani da zata? Kansa ya dafe cikin takaici.

  Yana fitowa sai ga Little ta shigo da tire ta kalli dan litti mamaki ya kamata bayan Habib ba wanda yaya yake kawowa bangarensa,ina kuma ya samo wannan?"

  Ashraf ne ya katseta da cewa " ko wa ya dawo?"
Kai ta daga alamar eh, fuskan nan tasa a daure yace " ki buga taro."

  Ta amsa da to sannan ta fita, kallan Dan Litti yai yace " zo ka ci abinci Gayu."

  Nan ya kaishi dinning ya turamai tiren gabansa sannan shi ya fita.

  Tunda ake taro agidan yauce rana ta farko da Ashraf ya fara zuwa gun taron da wuri, zuwa yai ya zauna fuskarsa a murtuke.

  A hankali kowa ya fara shigowa duk wanda ya shigo sai yayi mamakin zuwan Ashraf da wuri.

  Bayan kowa ya hallara ne Ashraf ya mike yace " bayan fitata waye ya kira matata Nafisa?"

   Cikin mamaki kowa ya kalleshi, Kawu yace " dalilin taramun da kai kenan?"

Ashraf yadan motsa baki sannan yai murmushi yace " matata bayan fitatavna tabbata wani ya kirata, in kuwa ba'a kirata ba anje har inda take anci zarafinta, dan a yanzu haka bata gidan nan, ban kuma san inda ta shiga ba."

  Umma tace " to menene namu a ciki? Banaji wannan damuwar mu ce, kila ta tafi yawon karuwancinta ne."

  Ashraf yq shafa goshinsa yace " menene naku a ciki? Ina tunatarwa ne da in ban ganta ba ni kaina bansan me zan aikata ba."

   Asim ya mike rai a bace yace " kai! Kayi kadan ka taramu akan wata banzar yarinyar da mu bamu san matsayinta ma a gunka ba, wanda babu shaidar ita matarka ce."

  Ashraf yadan yi murmuhsin da har hakoransa suka fito yace " Little kiramin bakon nan."

  Nan ta mike tai waje, Ashraf ya cigaba " wlh in har wani abu ya samu Nafisa bani da guarantee din abinda zan iya aikatawa."

  Mumy ta kalleshi zatai magana kawu yai saurin cewa "nina kiranta bayan ni kuma banaji akwai wanda ya kirata, inka tashi hukuncin sai kamin, tunda yanzu idanka ya rufe akan karamar yarinya sam baka tunanin kowa."
  

   Ashraf ya kalleshi sai dai baiyi magana ba, ya gane Mumy ce ta kirata kenan, tunda yasan ai kawu suna tare gun aiki.

  Kallan Mumy ya shigayi, ta had'e fuska tace "eh nice na kirata, Ashraf wai meke damunka ne kwana biyi?"

  Idanunsa ne suka fara canza kala, a hankali ya ke fitar da wani hucci dan kar a gane ransa yakai kololuwa gun tashi.

  Shigowar Dan Litti ne ya taimakeshi da yayi barna dan tibiren dake gabansa mai dauke da cups na tangaran kawai yake kallo.

  Dan litti ya tsaya daga nesa cikin tsoro ganin duk an zubomai ido, kuma kallan tsana ake mai.

  Ashraf ya kalleshi yace " karka damu mutumina gani nan anan."

  Kallan Ashraf yai sannan hankalinsa yadan kwanta, Ashraf ya kalli Kawu yace "to ga shaida na nan na sanda aka daura auren, banaji daga wannan shaidar kuma kuna bukatar wata."

  Kawu ya Mike ya kalli Dan Litti yace " daga ina kake?"

  Dan litti yace " kauyen gwaram."

  Kawu yace " menene hadinka da Nafisa?"

  Kauyensu na kusa da tamu."

  Menene ita kuma tsakaninta da Ashraf?
Matarsa ce.

   Wannan kalma ta rikita kowa, Ashraf yama Dan litti alama akan ya koma.

  Yana fita Ashraf yace " zan nemo matata da kaina, sai dai bazan yafema wanda ya kuskura ya kara shiga harkarta ba."

  Yana kai nan yai waje......

_Ina mika ta'aziyata ga Aisha Y. Kura na rashin mahaifinta datai, Allah ubangiji ya jikansa, yasa aljanna ce makomarsa ya kuma kai haske kabarinsa (Ameen)_

*#ASHRAFEENAH TEAM*

No comments:

Post a Comment