����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
No. 3⃣0⃣
Dad zaune kusa da Abba dayazo ganin gida, Dad ya kalli Abba yace "Yaya haryanzu banji kace komai ba?"
Abba ya kalleshi fuska a had'e yace " Meyasa baka fahimta ne Isma'il? Taya zaka had'a jininka dana....."
Dad ya katseshi dacewa" Haba Yaya meyasa bakwa fahimta ne, Seemah 'yatace akoda yaushe, duk da a baya nima nayi tunanin kaita gidan marayu, amma daga baya na gane haka Allah ya kaddaramin, kuma inaji a jikina Seemah Amanace Allah yabani."
Abba ya kalleshi cike da tausayi yace " Nafahimci abinda kake nufi amma kai kana tunani su Hajiya zasu yadda da wannan fatawar taka?"
Dad yace " nasani yaya shiyasa nake rokon ka daka taimakamin, Yaya banaso wani abu da zai d'aga ha kalin Seemah."
Cikin takaicin hali irin na kaninsa Abba ya m'ike yace " Seemah Seemah Seemah!!! Haba nagaji da yanda ka damu da yarinyar, anya ma kana kaunar 'ya'yanka kamar yanda kake santa? Ko dai akwai wani abu dabaka sanar dani ba? Bana tunanin akwai mutum irinka a duniya, mahaifiyar yarinyar nan tajaza maka masifar da bazaka tab'a iya wanketa ba amma kai kamar mara tunani."
Hawaye ne suka taru a idan Dad ya mik'e shima ya kalli yayan nasa yace " Yaya alokacin kunki fuskarta ne amma ni kad'ai nasan halin datake ciki."
Cikin takaici Abba yace " Nikarka karamin zancen wata mata can da banasan in tunama nasan ta, sannan ni haryau ban yarda ma........"
Cikin zafin Rai Dad yace " haba yaya! D'an Allah karka kara furtamin kalaman nan."
Abba a zuciye ya bar gidan, Dad ya zube a kasa kawaa yasa kuka kamar karamin yaro, gyambun dake birne a zuciyar sa ya famu, kuka yake sosai bai masan sanda Habib ya shigoba, dayake Abba a bud'e yabar kofar, Habib ya tsaya a bakin kofar yana kallan mahaifinsa jiyai kawai jikinsa ya d'ebi rawa baisan sanda shima hawaye suka fara zubomai ba, kallan mahaifinsa yake cikin wani yanayi mai wahalar fahimta, meyasamu dad? Me akamai? D'an da alama kukan daga zuciya yake fitowa bawai ciwo yaji ba ko rashin lafiya bane.
Habib a hankali ya karaso kusa da Dad ya rungumeshi ta baya baice komai ba sai kuka shima da yakeyi, A hankali Dad ya fara kokarin saita kansa, ya juyo da fuskarsa kan Habib, baice mai komai ba Habib ya rungumeshi yace " Dad menene yakecin zuciyarka haka? Menene ke damunka da har zakai irin wannan kukan? Dad ni babban d'ankane kuma Abokinka ko kamanta haka kake cemin in ina cikin damuwa?"
Dad ya kalleshi kawai girgiza mai kai yake, Habib ya kakaro wani murmushi yace shikenan Dad na d'auka munyi shakuwar dazamu d'inga raba matsalolinmu.
Mik'ewa yai ya fita Dad ya bishi da kallo cikin tausayi sai dai yana tsoron furtama Habib maganar.
Jalal kam ganin zaman da yake ya isheshi yasa ya mik'e da sauri yai waje shima, ya fara neman Zainab, yana tunanin ita kad'ai ta rage masa a mafita yasani inya sanar da ita abinda ke ransa zata goyamai baya.
Sai dai duk yanda yaso nemanta bai sameta ba, haka ya gaji ya koma gida, yana shiga ya ganta a tsakar gida tana shara, cike da mamaki ya karasa gunta yace " Zainab inasan magana dake."
Jiyai Umma tace " bazata ba, Jalal yaushe ka zama haka? Nasani sarai abinda kake tunani."
Jalal yace " haba Umma meyasa bazaki fahimceni ba?"
Zainab ta d'ago fuskarta duk ta b'aci da kwalla, ta kalli Jalal shikin bakin ciki tace " Yaya yaushe ka zama haka? A da na d'auka kai mutum ne mai tsananin girmama iyayensa, menene dalilin dayasa ka canza? Nice bakasan aure? Saboda ni kake wannan abun?"
Jalal ya had'e rai wani kallo ya buga mata yace "in ima magana da Umma karki kuskura ki kara katseni." ajiyar zuciya tai idanunta suka kara zubar da kwalla tace " Umma d'an Allah kubar shi ya auri wacce yakeso." Tana kainan tai d'aki da gudu ta rufo kofar, kallo Jalal ya bita dashi, Umma tace " Jalal ka bani mamaki." Itama ta juya ciki.
Iska ya furzar daga bakinsa wayarsa ce tai kara ya cirota daga aljihu, ganin Sagir yasa ya d'aga wayar Sagir yace " Jalal kana ina? Kazo Habib na nemanka."
Jalal yace " bangane yana nemana ba? Yau asabar ban fahimci dalilin dazaisa a nemi ni ba bayan ina hutun weekend. "
Sagir yace " to d'an ka'ida amma please kazo yanasan ganinka wajen 5 yace it's urgent."
Harzai musa sai kuma yai tunanin da alama maganar bata aiki bace mayb tsakaninsa ne da Seemah, da sauri yacema Sagir okay zanzo.
Yana katse wayar ya shiga d'akin Umma, a zaune ya ganta ta baza tagumi, ya karasa kusa da ita ya zauna ya kalleta yace " Umma?" Juyo da fuskarta tai ta kalleshi, yacigaba" Umma ko nace dole sai na auri Seemah baza ki amince dani ba?"
Tace kwarai, yai ajiyar zuciya yace " ko nace Seemah ce jigon rayuwata bazan iya rayuwa ba sai da ita bazaki amince ba?"
Kallansa tai da mamaki tace " Jalal!! "
Yace " ko nace in ba da itaba bana tunanin zan iya zama da wata a matsayin matata bazaki amince ba."
Kallansa take cike da kulawa tace " Jalal yaushe ka fara soyayya haka? Ban tab'a tunanin zaka so mace haka ba? JALAL meya sameka? Baka tunanin sun maka asiri?"
Mik'ewa yai ya juya mata baya yace " nikaina bansan ya akai na zama haka ba Umma, bansan yaushe zuciyata tai rauni akan mace haka ba, in tana dariya sai insamu kaina cikin farinciki, in tana bakin ciki sai inji nafita damuwa, in taji ciwo jinshi nake kamar a jikina, in ina tare da ita jinake kamar kar mu rabu, Umma bansan meke damuna ba."
Idanun Umma ne suka cika da kwalla, ta kalleshi cikin tsananin tausayi, lalai ta fahimci halin da d'anta yake ciki amma ya zatai da Zainab? Mik'ewa tai ta dawo ta gabansa tace " nafahimceka kwarai Jalal sai dai Jalal abinda baka sani ba shine, rayuwar aure ba soyayya ake nema ba kawai.
Kai ya girgiza yace " Umma ban damu da wad'an nan ba."
Shiru tai jikinta duk yai sanyi, Jalal ya kalleta yace zan koma Abuja yanzu ana nemana zanzo wani satin, Umma d'an Allah kitaimaken kishawomin kan Abba.
Takalleshi tace daga zuwa? Yace eh oganmu ke nemana, tace to Allah ya kiyaye.
Direct tasha ya nufa ya shiga mota, tunani yakeyi ta ina zai fara shawo kan lamarin.
A company d'insu ya sauka, office d'in Habib ya wuce, ba kowa saboda yau weekend, knocking d'in kofar yai daga ciki akace ya shigo, shiga yai da Sallama, Habib ya bashi izini zama, shikam yana tunanin harda maganar san Jalal da Seemah take yasa Dad cikin wannan halin dukda baisan takamaimai dalili ba sai dai shikanshi bazai yarda da wannan soyayyar ba.
Zama Jalal yai sannan Habib ya mik'amai hannu, sun gaisa Jalal yace " akace kana nemana?"
Habib ya kalleshi tare da ajiye takardun hannunsa, yace " kasan kanwata?" Kai Jalal ya d'aga, Habib yace " akwai wani abu a tsakaninku ne?"
Cikin rashin fahimta Jalal yace " kamar me fa?" Habib yace " kamar abinda ke tsakanin mace budurwa da namiji."
Jalal yai murmushi sannan yace " eh, we like each other. "
Habib ya tattara hankalinsa kan Jalal sannan ya zaro envelope ya tura masa abansa, Jalal ya kalleshi da rashin fahimta yace na meye? Habib yace ka bud'e, Jalal ya zaro abinda ke ciki check ne na million 3, cikin tsananin mamaki da tambaya ya kalli Habib yace na meye? Yai maganar tare da ajiye envelope d'in.
Habib yace " wannan kud'in ina tunanin ya isheka ka fara business d'an haka inaso kabar garin nan kaje wani gun ka fara kasuwancinka."
Jalal ya kalleshi yace "bangane in fara kasuwanci ba? Kuma kai a matsayin me kake a guna da zaka bani kud'i ka kuma umarceni akan wasu sharad'u dabata shafi aiki ba?"
Habib yaji zafin kalamansa amma ya daure yace " ina nufin ka rabu da Seemah, kai kanka kasan tafi karfinka, ko kana tunanin kanada abinda zaka kula da ita ne?"
Jalal ya saki wani murmushi yace "Ahhhh dalilin kenan? Sai dai yaza'ayi yaya Habib bana tunanin zanyi accepting wannan offer taka."
Yana kai nan ya mik'e cikin tsananin b'acin rai, zai iya jurar komai amma ya tsani amaidace gara wanda za'a iya siya da kud'i.
Habib shima ya mik'e zaiyi magana kawai sukaga an turo kofar, Seemah ce da Ammar suna dariya, dariyar ta tatsaya ne sanda taga Jalal, da mamaki ta kalleshi tace " My Deen me kake a nan? Ba kace kana birnin gwari ba?"
Idanunsa ta kalla ba shakka ransa a b'ace yake matuka, Jalal ya kalleta sannan ya kalli Ammar ya juya ya kalli Habib yace na wuce, ta kusa da su yazo ya wuce bai kula Seemah ba, Ammar ya bishi da kallo haka kawai yaji bayasan guy d'in.
Seemah kam kallan Habib tai tace " yaya lafiya?" Bai amsa mata ba kawai ta juya tai waje da gudu, Ammar na k'iranta amma inaaa, da kyar ta tadda Jalal yana jiran elevator da sauri tasha gabansa tana hakki, tace " Deen menene? Yanaganka haka? Kana ganina baka min magana ba."
Kallanta yai sannan yace " haka kuke dama masu kud'i? Komai bakwa iya solving d'insa sai da kud'i? What do u people think of me? Kije ki sanar dasu halaye na."
Gaba d'aya Seemah takasa fahimtarsa, bai jira amsarta ba yana ganin Elevator ya tsaya ya danna ya shiga ya barta a tsaya tana maimaita kalamansa.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*