๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ *Jร
ฤนรฤนรฤฤฤร*๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Na *AYUSHER MOHD*
NO 9โฃ
Waya ta d'aga ta k'ira Ammar yana d'agawa cikin shagwab'a tace "yaya!!!!"
Cikin rud'ewa ya tambayeta " Seemah menene? Waya tab'amin ke?"
Takara shagwab'ewa tace " yaya an wulakantani yau."
" waya isa ya wulakanta min ke kanwata? Banaji an haifeshi, kinaso yayanki yazo yad'au hukunci?"
Ammar yai maganar cikin b'acin rai.
Seemah tasa dariya tace " Kai yaya ni kainan inajin dad'in kasancewa kanwarka, amma a yau inaji amai uzuri amma in har ya sake zan fad'ama kad'au min mataki."
Shima dariyar yai yace " kin hucce?" D'aga kai tai kamar yana ganinta tace " sosai ma." Hira sukai tayi sai dayaga ta ware sosai sannan sukai sallama.
Murmushi tabi wayar dashi sannan ta koma ta zauna a kan kujera.
Seemah kwafa tai sannan ta leko ta k'ira Sagir, tace zo kasamin number office d'insu abokinka, ta fad'a tana nuna landline na office d'in, Sagir ya karaso ya nuna mata tace tnx, yana fita ta kira number.
Manager d'insu ya d'aga tare da tambaya, Seemah tace " daga office d'in chairman ne, inaso a turomin Jalal yanzun nan." Tana kainan ta kashe.
Cike da mamaki manager d'in yabi wayar da kallo, Jalal?
Jalal kam ya dad'e agun kafin ya d'aure ya sauko, sai dai yana zuwa office d'insu Manager d'in yace " kaikuma ina ka shiga?" Jalal yace na d'an fita ne,
"Kayi sauri ana nemanka a office d'in Chairman." Manager d'in yai maganar yana kallansa.
Gaban Jalal ne ya fad'i sai dai bai bari Manager d'in ya gane ba kawai ya juya ya fita, yana zuwa ya bude kofar tare da kallan Sagir, yace " Ana k'irana ko?" Sagir yace bari in sanar sai ka shiga.
Nan ya mik'e daga mazauninshi yai knocking office d'in, Seemah ta bada izini ya shiga ya sanar mata yazo, tace ya shigo, nan ya juya ya fita.
Kallan Jalal yai yace " ka shiga."
A hankali Jalal ya karasa yai knocking ta bashi izini ya shiga da sallama, Seemah na tsaye jikin window tana kallan waje kallanta yai da mamaki yace " ke kika kirani?" Juyowa tai tare da yin murmushi tace " ayya shikenan ma je ka." Jalal da mamaki ya kalleta bangane ba.
Kallansa tai tace " nace ka tafi na fasa." Cikin b'acin rai ya fito tare da bugo kofar da karfi, ko Sagir bai kallaba ya juya ya fita, yana koma wa office d'insu ya sake had'uwa da Manager a kofar office d'in yace " Jalal kayi sauri Madam tace ka koma."
Jalal ya kalleshi yace " daga gunta fa nake tace in komo." Yace " kayi hakuri ka koma tace lalai kaje yanzu."
Jalal cikin mugun takaici ya koma, yana zuwa ko Sagir bai jira ya neman mai izini ba ya bud'e kofar ya shiga, tana tsaye jikin fridge d'in office d'in tana shan ruwa, ta juyo tace ka koma na fasa, Jalal ya kalleta wani takaici ya kamashi karasawa kusa da ita tare da fizge jarkar ya ajiye sannan cikin b'acin rai ya kalleta yace " am I a joke?"
Kallansa tai tace " bakaga ruwa nake sha ba?"
Jalal ya nunata da yatsa ya kara matsowa kusa da ita yace " bazan d'auki wannan rainin hankalin ba d'an haka don't you dare repeat that to me." Yana gamawa ya juya zai fita.
Hannunshi ta kamo tace " ka manta ni kanwar mai Company d'in ce?"
Yace " if u need respect then act right." Sannan ya juyo yace " Sakeni in tafi ko?"
Tace " waya baka damar tafiya?" Tafad'a tana hararsa.
Ya juya tare da fizge hannunsa sannan yace " ni naba kaina."
Yana kainan ya fita da sauri, kallansa tai da mamaki sai ta sami kanta da sakin wani sansanyar murmushi, sai kuma can tace "Not Bad."
Nikam Ayusher nace mefa?
Jalal ya fito cikin takaici ya karasa office d'insu sai da abinda yakara d'aure mai kai Manager ya kara gani a tsaye a kofar, yace lafiya? Manager yace " ance in kaika da kaina, d'an haka wuce muje." Jalal ya kalleshi yace ina?
Hannunsa manager d'in ya kama suka fara tafiya, Jalal ya kwace hannunsa yace itace dai? A hankali Manager ya d'aga kansa alamar eh, Jalal yace zanje da kaina, nan ya fara tafiya yagama shirya yawan rashin mutuncin dazai kwara mata.
Da karfi ya bud'e kofar ko sallama baiyi ba, sai dai me? Habib ya gani zaune a kujerar sa Seemah na tsaye tana waya jikinsa ne yai sanyi a hankali yace "am sorry."
Habib ya kalli Seemah dake ta shagwab'a a waya, Jalal kam takaicin yanda take shagwab'a yakeyi amma da alama ko saurayinta ne, sai dai jin tace " Dad sai anjima." Yasa ya d'ago, Dad?
Maganar Habib ce ta katseshi dayace " Seemah wannan ne?"
Seemah ta kalli Jalal tace eh yaya please.
Habib ya kalleshi yace " d'an Allah so nake ka taimakamin, kanwata ce kesan zuwa yin shopping to nikuma inada aikin yi shine tace tanaso kad'an kaita."
Jalal da mamaki ya kalli Seemah ya mata kallan jiya baki daddara ba ko? Baki ta murgud'amai tace " ni yaya dama shi ka bani a matsayin driver na." Wani kallo da Jalal ya watsa mata ba ita ba har Habib sai dayasha jinin jikinsa, ganin yanda ya kafeta da ido yasa ta had'iyi wani yawo tace" Wasa nakeyi maida wukar."
Habib ya d'an kakaro dariya yace " karka damu akwaita da tsokana, she is just joking."
Sai a lokacin Jalal yad'auke idanunsa, sannan yace " yau ne kad'ai zan kaita ko?"
Habib ya d'aga kai yace yau ne kad'ai, in ka kaita ka karasa da ita gida, Jalal yace to sannan ya kalleta yace " muje ko Madam?"
Seemah ta anshi key sannan ta fito.
Sunje shiga mota Seemah harta bud'e baya Jalal ya sa hannu ya fizgota ya sata a gaba sannan ya rufe shima ya shiga, kallansa tai tace " meye hakan kuma?"
Jalal yace tambaya kike? Batace komak ba kawai ta juya kanta tana kallan window, Jalal ya tada mota sun d'an fara tafiya tace " wato bazaka bani hakuri ba ko?"
Jalal ya kalleta yace " laifin menai dazan baki hakuri? Bakya tunanin ke zaki bani?"
Juyowa tai tace " kamanta me kamin ne?"
Jalal ya saki murmushi yace " au duk wannan abun da kikemin so kike in baki hakuri?"
Ta d'an turo baki tace " eh mana, kuma inaso kabani yanzu."
Jalal yace " lalai kin da aiki a gabanki."
Tace sai in taka burk'i yanzu, ko in bud'e kofar motar, uhmmm ko insa ihu in ma sharri.
Ga mamakinta dariya taga Jalal yasa abinda bata tab'a gani ba, dariya sosai yai, sannan ya kalleta yace ko zaki gwada?
Ganin yanda take kallansa yace " kallan fa?"
Ta kifta ido tace " dama kana dariya?" Da sauri ya had'e rai yace " baki gani daidai bane, ba dariya nai ba."
Seemah tai murmushi tace "yau naga side d'inka kala kala, d'azu ka makamin kallo kamar zaka dakeni yanzu kuma dariya?"
Jalal ya had'e rai ya cigaba da tuk'insa, Seemah ma shiru tai sai dai murmushi bai bar fuskarta ba......
ยฉ *NWA*
๐โโ
No comments:
Post a Comment