Sunday, 11 December 2016

JALALUDEEN 4

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ
     ๐Ÿพ *Jร…ฤนร€ฤนร™ฤŽฤšฤšร‘*๐Ÿพ
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ









Na *AYUSHER MOHD*







4โƒฃ



Har suka isa Company d'in ba wanda yama wani magana a cikinsu, haushi duk ya cika Jalal aikuwa da yazo taka burki da karfi ya taka har sai dayasa Seema ta bugi kujarar gaba, cikin b'acin rai ta d'ago tare da dafa gun kamar tai kuka dan taji zafi.

  Jalal ya juyo yace " Sorry bankula bane."

   Ta tuna itama haka tace data mai tsiya a airport wato ramawa yai ko me? Juyawa tai ta kalli Company d'in, babban ne sosai duk an bishi da glass lekawa tai taga kamar mutane sun taro daga bakin kofar, ido ta kura nan ta hango yayanta, wani murmushin dad'i ta saki tanaso taga ana ji da ita, wannan tarbar da aka mata yasa taji zafin goshin ya tafi, kallan Jalal tai dake miko mata key, yace " gashi kyaba yayanki."

   Ta kalleshi tace " bud'emin kofa."
  Jalal ya kalleta cikin rashin fahimta yace " what did you just say? "
  Ta murgud'a baki tace " bakaga an taro ana jirana ba? Ko so kake ka b'atama yaya na rai?"

   Jalal yad'an yi wani dariya dakanaji kasan ta bakin ciki ce, yace " Servant d'inki ne ni?"
   Zatai magana taga an bud'e mata kofa, cikin mamaki ta kalli waje, wani saurayi ne yace " Welcome Madam"

  A hankali ta zuro takalminta mai mugun tsini sannan ta fito, sai dataje tsakiya yanda jalal zai jita haka kuma mutanen dake jiranta zasu jita, ta juyo cikin wani rainin hankali takalli jalal dake tsaye jikin mota, tace " Mr Pride d'an Allah jakata na manta nan kawomin."

   Jalal ya kalleta tare da nuna kansa da hannu yace " Me?"
  Ta d'aga kai tace" Sorry."


   Wanda ya bud'e mata kofa yace " bari na anso miki madam.
Seemah tace " barshi shi nakeso ya kawomin."
Tana kainan ta cigaba da tafiya.

  Jalal ya furzar da wata iska cikin takaici ya bud'e boot ya d'auko trolly d'in.

  Seemah ta karasa gunsu yaya tana tafe tana murmushi, Habib na gani ta kusa zuwa ya karasa tare da rike hannuwanta duka biyu, tab'e baki tai tace "yaya haka ake oyoyon?"

  Yace " Sorry Seemah ta bakiga da mutane bane? Kuma kinsan a kasa na suke kar su rainani."
Tace " nagane, oh ni yaya ashe zanganka?"
Dariya yai yace "mu wuce office d'ina muyi murnar ganin juna, ko?" Cikin zumud'i ta d'aga kai, nan suka fara tafiya, nan ta waiga ko zataga d'an rainin hankalin nan,  sai dai ga mamakinta duk inda ta duba bayannan mamaki ya kamata, ina yaje? Jakarta ta hango a hanyar shiga,  wato har ya ajiye ya tafi? Lebenta tad'an ciza tare dayin kwafa a hankali.

  Sun isa mutane na ta gaisheta tana amsawa, farinciki ya cikata tanasan kulawa, har suka isa office d'in kowa ya gansu sai ya gaidasu, suna isa suka rungume juna, ta rik'e hannun Habib tace " Yaya I really miss you. "
  Yace "nima kanwata, ni kad'ai nasan dad'in danakeji na ganinki."
  Dariya tai tace " yaya sai yau nazo mahaifata, bakaji dad'in da nakeji ba dan ma d'an......." sai kuma tai shiro.
Habib yai dariya yace" badai daga isowar kanwata har an samu rikaken dazai b'ata mata rai ba? "
Ta turo baki tace " sosai ma kuwa yaya, kuma nad'au alwashin sai ya tsugunna ya nemi yafiyar abubuwan dayamin."
  Dariya sosai Habib yai yace " namanta ashefa Seemah aka tab'o wacce bata hakuri in aka mata abu."
 Tai dariya itama tace " yaya dad'i nakeji sosai."
Sun dad'e suna hira, har waya sukai dasu dad yakara tunamai ya kular masa da Seemah, suna gama waya Habib yace " kai dad ma sai a hankali, tun kafin kizo yake tunamin in kula dake."
    Dariya tai tace " ai nasani dad duk yafi sona akanku, bayasan abu ya tab'ani."

 Habib yace "muma duk muna sanki sosai, yanzu dai dolene in samarmiki wanda zai dunga kula dake a duk harkokin da zakiyi a nan kasar, amma kamar mutane nawa kikeso?"

  Shiru tai can wani abu ya fad'o mata wani mik'ewa tai tare dayin tsalle, tace " kaii!!!!! Amma naji dad'i."
Kallanta Habib yai tare da tambayarta mene? Ta tsugunna agabanshi tace " yaya wani abu nakesan kataimakamin dashi."

 Yace menene wannan? Seemah ta saki murmushi tace " akwai wanda nakesan yazama driver na kuma bodyguard d'ina."
Habib ya kalleta da mamaki yace " au yanzu daga shigowar ki gari har kinsan wani da kikeson ya kula dake?"
  Tace " sosai kuwa yaya, kuma shid'in nan nakeso yad'inga min aiki."

  Habib yace "ba matsala in dai har ba ma'aikaci bane."

 Cikin shagwab'a tace " nidai ko ma'aikacin ne shi nakeso Yaya, in yaso sai a tsayar dashi in na koma sai ya koma aikinsan tunda ba dad'ewa zanyi ba."
Habib yace " dole a miki duk abinda kikeso Princess. "



  Wani murmushi tasaki, harta hango tana sashi aiki yana mata....hahhh lalai zataci dariya.


***************************


  Jalal kam yana kai jakarnan ya wuce department d'insu yanashiga, ya zauna a kujerarsa cikin b'acin rai, shugabansu nagun aiki ya shigo tare da cewa " Jalal bakai nagani yanzu ba? Rik'e da jakar kanwar Chairman? "

   Wani takaici ya kamashi ya kasa magana, shugaban yasake cewa " kai amma kaji dad'i gwara daka kama kafarta, d'an ancemana Chairman d'in Company d'inan nasan kanwar nan tasa, kasani ko tamaka hanya ka zama mai office d'in kanka ba irin wannan ba na kusan mutane biyar?"

  Jalal ya mik'e cikin tsananin bakin ciki da sauri yai waje tare da bugo kofar office d'in da karfi.

   kama kafa? Kamar shi? Da iliminsa da komai? Ajiyar zuciya yai tare da kiran Abbansa, bayan sun gaisa ya tambayi jikin kanwar sa, Abba yace " jiki nanan yanda yake."
  Sun d'anyi hira kafin suyi Sallama.






By *Ayusher Mohd*
ยฉ *NWA*

No comments:

Post a Comment