����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MOHD*
No. 1⃣1⃣
Bai sake kulata ba har suka isa gida, mai gadi ya bud'e gate kallanta yai yace " a nan za'a bar motar?" Kai ta d'aga hakan yasa ya shiga da motar, yai parking, kallansa tai tace " mezance? Godiya zanyi ko me?"
Jalal yad'an matso kusa da ita sosai, ya kai bakinshi kefen kunnenta a hankali yace " ki rik'e godiyar ki ko rashin ta, ki kama hanya ki kwashi kayanki d'an banaji ko tsinke zan d'aukar miki." Juyo da fuskarta tai ta kalleshi sai kuma ta saki murmushi tace " na hutasheka ko ka manta munada masu gadi da masu aiki a gidan, kai dai nake tunani ko kanada kud'in da zai maidakai."
Tana kainan ta juya da niyyar bud'e kofa, hannunta Jalal ya fizgo ta koma ta zauna tare da juyowa, Jalal yace " me kika ce?" Seemah tad'anyi shiru kawai tana kallanshi, fuskarnan tasa a had'e haka kawai sai taji ba dad'i rau rau tai da ido tace " Jal jiya ka banni da yunwa da wahala yau kuma hannuna kakesan b'alawa? Da alama yau ne rana ta karshe dazan yi amfani da hannun, oh ni Allah sarki ni."
Yanda tai maganar ne yasa Jalal ya saki hannunta da sauri yace "haka ake b'alla hannu a garin ku?"
Hannunta ta kalla tare da langwab'ewa tace " shikenan hannuna....." da sauri Jalal yad'an tab'a hannu kara tasa kad'an tace " Jal hannuna......" rud'ewa yai sosai yace menene? Da gaske ciwo yake?
Dariya sosak Seemah tasa tace " amma kanada saurin shiga." Kallanta yai shima baisan sanda yasa dariya ba, yace amma wlh yarinyar......bakinshi tai saurin toshewa da hannunta tace " basai ka karasa ba."
Hannu yasa ya ture hannunta sannan yakara yin dariya tare da girgiza kai....kallansa kawai Seemah take ta karkatar dakai tana murmushi.
Jalal ya kalleta sannan yace " Na tafi." Ya fad'a tare da bud'e kofa, itama da sauri ta bud'e kofar ta d'aura kanta a saman mota tace " Sai yaushe kuma?" Tsayawa yai tare da juyowa ya kalleta yace " Saurayin ki ne ni da zaki tambayeni sai yaushe?" Da sauri ta d'auke kanta sannan tai d'an juya kai tace " ce maka akai haka nake nufi?" Murmushi yai yace " bari na turo miki mai gadin dan da alama baisan kinada kaya ba."
Yana kainan ya cigaba da tafiya, Seemah ta bi bayanshi da kallo har ya fita, a jiyar zuciya tai tare da cewa " not bad."
Mai gadi ne ya karaso tare da kwasar kayan, Seemah tai ciki da sauri, jin gidan shiru yasa tai d'akinta.
A kwance ta taradda Aisha da alama waya take kallanta tai taga yanda ta wani shige bargo tana wani kashe murya, Seemah tai tsaki sannan ta yau gado ta kwanta tare da rik'e wayata da alama game takeyi.
Aisha ce ta taso tazo kusa da ita bayan ta gama wayar tad'an tab'ata, Seemah ta mik'e tare da kallanta tace "lafiya?"
"Seemah d'an Allah inada tambaya, misali saurayinka kullum badai shi ya k'iraka ba sai dai kai ka k'irashi sannan wani sa'in in ka k'irashi ma sai yace yana wani aikin ne zai k'iraka, kuma fa bazai k'iraba, dan Allah me hakan yake nufi?"
Seemah ta mik'e zaune ta kalleta tace " me kuwa yake nufi, banda ke kike sansa ba shi yake sanki ba? Sannan alamace ta yana buk'atar ki barshi ya huta."
Ta mik'e tare da d'aukan towel sai datakai wajen toilet ta juyo ta kalli Aisha tace " narasa meyasa mata bakwa sanin 'yancin kanku, har akwai namijim daya isa ink'irashi ya dizgani haka? Ba'a haifeshi ba." Tana kainan ta bud'e kofar toilet ta shiga.
Aisha ta bita da kallo idanta kamar tai kuka tace " mene? Alamace ta me...? " sai kuma tai kwafa tace " Allah ya nunamin sanda soyayya zata rufe miki ido...
Seemah kam wanka take amma tana mita a ranta.....
■■■■■■■■■■■■■■■■■■■
Da daddare suna zaune dukansu a falo a na hira Seemah na kusa dasu Ra'is tana koya musu homework, Habib ya kalli Seemah yace " D'azu ba dai abinda ya faru ko?" Tace name fa?
Yace" da kuka fita siyayya, naga kamar guy d'in nan basan zuwa yake ba."
Murmushi ta saki tace " Auu wannan? Ya kula dani yanda ya kamata kuwa, yaya a haka ne zaka ganshi kamar mara kirki amma a zahiri he is not a bad guy."
Habib da mamaki ya kalleta yace " ya akai kika sani? Bayan a tunanina yau ce had'uwar ku ta biyu?"
Da sauri tai kasa da kai tace " hmm kawai nima yau d'in ne naga kamar......."
Farida ce ta katseta tace " kodai kanwata ta fara san wa..........
Cikin wani irin tsawa Habib yace " banasan haka Farida, ke meyasa sai ana maganar mutunci sai ki d'inga fad'o abinda ba'a tambayeki ba?"
Cikin sanyi jiki Seemah ta kalli Habib sannan ta kalli Farida, mik'ewa tai taja su Ra'isa sukabar falon....
Tana kaisu d'aki ta koma d'akinsu ta kwanta sai dai ta kasa bacci sam, fuskar Jalal take hangowa, nan yana dariya, can yana murmushi, can kuma ya had'e rai......ajiyar zuciya tai ta saki murmushi.......
♧♧♧♧♧♧♧♧♧
Washe gari da safe Habib ya mata waya yace ta shirya zasuje gaida kakaninsu, murna sosai Seemah tai, Farida da kanta tazo ta duba had'ad'un kaya a cikin na Aisha ta zab'ar mata wata atamface da aka mata d'inki zamani riga da siket ne yau ce rana ta farko da ta tab'a saka kayan hausawa, sai dai kayan sun karb'eta sosai, Aisha ta zauna ta d'aura mata d'ankwalli, Seemah tayu kyau sosai ita kanta dad'i takeji inta kalli kanta, tarasa dalilin dayasa Jalal ya fad'o mata, tunaninta d'aya inya ganta mezaice?
Sun fito Habib sai wasa ta yakeyi suka shiga mota, nan suka fara tafiya zuwa Suleja inda iyayen Dad ke zaune.
Suna tafi suna hira har suka isa sunyi parking a daidai gate d'in wani karamin gida flat house mai kyau, Habib ya kalleta yace muje ko? Kallansa tai tace " Yaya why am I feeling so nervous? " hannunta ya rike yace " keda zakiga kakaninki mai zai saki jin haka?"
Murmushi tai sannan ta saki ajiyar zuciya tare da fitowa daga motar.
Habib na gaba tana binshi a baya, suna knocking akazo aka bud'e, wani almajiri ne ya gaidasu sannan Habib yatambayeshi ina hajiya? Yaron yace tana d'aki, nan sukai hanyar d'akin.
Sallama yai, wata datijiwace ta fito fuska a sake tana cewa maraba da babban jika na, dariya yai yace " ya akai kika gani muryata? Kafin ki fito?"
Fuskar nan cike da fara' a takalleshi tace " haba Mai gidan ya za'ai in kasa gane ka?" Idanunta ne suka kai kan Seemah kallanta takeyi taki d'auke ido, cikin rawar murya Seemah tace "ina kwana Hajiya?"
Batare data amsa ba ta kalli Habib tace ku shigo ciki, amma ban gane waccen d'in ba, nan suka shiga suna zama Mai gidanta ya shigo cikin murna yana cewa yau munada baki ashe? Lale da zuwan mai sunana.
Ciki ya shiga shima tare da zama kusa da Habib, Seemah kam jikinta rawa yakeyi ganin hajiya ta kafeta da ido, Habib ne ya rik'e hannunta yace " Hajiya Seemah ce, Auta sai yau Allah yai zuwanta."
Ba Hajiya ba hatta Alhaji gani yai sun had'e rai sunyi dif, a hankali Seemah tace " ina kwanan ku?" Sai dai abinda ya basu mamaki ba wanda ya amsa, Habib cike da mamaki yace " Hajiya gaisheku take fa? Baku gane ta bane?" Fuskar nan ba a sake ba, kawo yace " lafiya ya kika baro yan gidan?"
A hankali tace lafiya.
Sunyi shiru dukansu, Habib na mamakin wannan al'amari shikam bai fahimci wannan abun ba, itakam Seemah kasa tai kawai da kanta idanta kawai ya ciciko da hawaye.
© *NWA*
��♀
No comments:
Post a Comment