����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣2⃣
Habib na shiga mota ya kalli Seemah wacce take kallan waje, kanta ya shafa yace " me kike kallo?"
Juyowa tai ta kalleshi da raurau d'in idannunta, wanda kiris suke jira su fara zubar da hawaye, kai ta jijigamai kawai d'an tanaganin intai magana to lalai kuka ne zai biyo baya, sun fara tafiya ya kalleta yace mukaiki gida ko? Ni office zan koma? Kai kawai ta d'aga nan sukai hanyar gida.
A bakin gate suka sauketa har zata fita Habib yace Seemah ki kira Ammar ya dameni da waya, nan ma kai ta d'aga ta fito daga motar.
Tana shiga mai gadi ya bata key nan ta gane ba kowa a gidan karasawa tai ta bude ta shiga, direct d'akinta tai ta zuge jakarta ta ciro wayarta tana kunnata text d'in Ammar ne sukai ta shigowa murmushi tai tace " Allah sarki yayana."
Bayan tagama karantawa, ta danna numbersa, ringing d'aya ya d'aga yace " Haba Seemah, meyasa kike so ki wahalar da wannan yayan naki?"
Cikin sanyin murya tace " Sorry Special Broz wlh matsala aka samu na kashe wayata."
"Matsala? Kamar ta me kenan? Seemah gaskiya ni hankali ba akwance yake dake a kasar nan ba gaskiya zuwa zanyi ma taho tare."
Batasan sanda tai dariya ba tace " Karka damu yaya ba abinda ke damuna."
" duk mafarkin danake kina san kicemin a banza nake yinsu?" Ammar ya fad'a cikin kakkausar murya.
Mafarki?
Ammar yai ajiyar zuciya yace " ni kaina mamaki nake wlh kanwata tunda kika bar gida in na kwanta sai nayi mafarkin kina kuka."
Ido ta lumshe sannan tace " Ya Ammar gaskiya u are the best brother in d world."
Yace " Seemah fad'amin gaskiya meke damunki?"
Dariya tai tace yaya ba wanda ya kiraka? Yace eh menene? Kwafa tai tace share kawai yaya.
Sun dad'e suna hira kafin suyi sallama, murmushi tai tare da bude texts d'in Dad, tana gamawa taji text ya kara shigowa ganin No Name yasa tasan Jalal ne da sauri ta bud'e abin haushi text d'in yayi mantuwa ne daya mata jiya kenan.
Wayar ta cillar kan gado jin karar text ta karayi da sauri ta d'auka tare da addu'a a zuciya Allah yasa Jalal ne, tana bud'ewa kuwa taga No Name.
" Hope kun isa Lafiya, uhmmm actually bansan ya akema mace text ba, ko in ce bansan me akecewa ba yanzun ma bansan me zance miki ba."
Hannu tasa ta buga goshinta sannan ta rik'e kuncinta da hannuwa biyu tace " Oh ni Jalal to me kake nufi da ni? Ni zan koya maka ko me?" Wayarsa tai dialing, ringing 3 ya d'aga tace " let's meet."
Yace a ina? Tace zan fito da Bala zan jiraka kafin a karasa Company d'inku.
Suna sallama ta mik'e tare da canza kaya ta gyara fuskarta tayi kyau sosai, fitowa tai suka fita da Bala.
Suna zuwa wajen Company d'in tace Bala d'anyi oarking anan, nan suka tsaya tace ungo kud'i ka koma gida nizan karasa gun yaya, yace amma........katseshi tai cikin masifa tace banasan raahin mutunci aiki kakeyi ake biyanka baruwanka da harkokina.
Hakuri ya bata ya amshi kud'i ya tafi, tana ganin ya tafi ta dawo gaba tare da saurin zuge jakarta ta d'auko cassette d'in rannan na Kabhi Kushi Kabhi Gam, ta saka tare da mai flashing, jingina tai a jikin kujeta tare da lumshe ido.
Bata dad'e ba taji motsin bud'e kofar, idanunta a rufe amma kanshin turarensa yasa ta gane waye, murmushi ne ya bayyana a fuskarta, Jalal ya shiga ya zauna tare da kallanta, bacci take? Ya fad'a aransa tare da matsowa daf da fuskarta ya fara kallanta, bai tab'a kare mata kallo ba irin na yau, kallan fuskarta yake sosai, jiyai zuciyarshi ta fara bugawa da karfi, jiyai ance " Deen Wannan kallom fa? Sai ka gano munina?"
Tai maganar idanunta a rufe.
Saurin matsawa yai sannan ya tada mota yace " wa ya ce miki kallanki nake?" Idannu ta bud'e tace " me kakeyi to inba kallo na ba?"
Titi ya kalla tare da cewa, abu nake kallo a ta waje ta Inda kike.
Had'e rai tai tace dama nasani ai.
Murmushi yai sannan yace ina zamu wai? Tace nidai kawai muje guri quite muyi hira I am not feeling good.
Da mamaki ya juyo ya kalleta yace " The Great yarinyar ce yau take fad'an haka?"
Seemah ta kakaro yake tai sai da sukai tafiya nai nisa suka d'an fita daga gari ba wanda ya sake magana, jiyai tace " Narasa menene dalilin dayasa sukemin haka? Me nai musu? Meyasa duk inda aka fad'i sunana sai inga ancamzamin?"
Jalal dake jin maganganunta ya gangara kasan titi yai parking a gefen wani fili kana gani kasan filin ball ne, ya juyo ya kalleta yace " Ina kikaje aka canza miki?"
Tace gidan kakanina da gidan yayan Dad, Ita kanta mamakin kanta take, ta rasa me yasa take fad'amai sirin nake ranta.
Hannu yakara lankwasawa ya d'ana mata a goshinta, cikin shagwab'a ta rike gun tace " Haba Deen wannan fa wayan mugunta ne, d'azuma fa kamin haka."
Yace " duk sanda kikai lefi hukuncinki kenan, yanzu menene d'an an canza miki fuska? So kike duk inda kikaje a fara tsalle ana murnar ganinki?" Kai ta d'aga alamar eh yace " ahhh!!!! Baki sani ba ko haka halinsu yake basu da sakin fuska, d'an haka ki cire tunanin komai a ranki."
Kallansa tai cikin tsananin bege tace " Deen kayi tunanin tambayar da na maka na menene tsakanin mu?"
Kallanta yai sannan yai ajiyar zuciya ta kalleshi tare da kwantar da kanta a jikin kujera tace " Bansan meke damuna ba kwanan nan, in muna tare da kai zuciyata sai ta dunga bugawa da sauri."
Matsowa yai kusa da ita tare da rike hannunta yace " me kikeso in d'inga ce miki?" Kallansa tai tace " Meemah, inasan sunan d'an nafisanshi akan Seemah, murmushi Jalal yai ya kara rike hannunta yace " Meemah! Ajiyar zuciya tace tace Deen d'an sake fad'a please a hankali ya kara cewa Meemah, murmushi ta saki tace " kodai inje incema Dad asake yanka min wani ragon sunan ne?"
Cikin wata murya mai taushi taji yace Naso inje inyi tambaya akan abinda ke damuna, na in ina kusa dake sai ind'ingajin zuciyata na bugawa da sauri, sai dai yanzu danaji kema irin abin da nake ji kikeji, hakan ya nuna min ba wani abu bane ke damunmu illa san juna da mukeyi, shine yasa zuciyoyinmu ke bugawa a tare in muna tare."
Kallansa takeyi idannunta suka ciciko a hankali taji kwalla ta zubo mata, Jalal ya kalleta cikin mamaki duk ya rikice yace " Meemah wani abun ne? Ko na fad'i abinda ya b'ata miki rai ne?"
Bai farga ba yaji ta rungumeshi kam sannan tace " Bawai abinda kafad'a bane baimin ba, dad'in kalaman ne sukamin yawa."
Murmushi yai, baiyi maganaba d'agowa tai ta kalleshi tace " karfa kace bani da kamun kai d'an na taso a wata kasar."
Da mamaki ya kalleta yace da akai me? Tace eh mana kasan mu a al'adar mu ba'a rugumar mutum, amma mu acan im abin farin ciki ya samu mutum baya sannin sanda yake rungume me sashi farin cikin.
Sai yanzu ya fahimceta dariya yai yace " kinganmu a fili, me zai hana in fara koya miki mota?"
Dariya ce ta zo mata ta rufe bakinta da hannu tace " Deen kasan abinda zance maka kenan?"
Atare suka saki murmushi ya fito itama ta fito sukai canjin gun zama.
©
*THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
*AJA!*
*AJA!*
*FIGHTING! !!!*
��♀
No comments:
Post a Comment