����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MOHD*
No. 1⃣0⃣
Can Jalal yace " me zaki siya wai? Dakika sani na taso?" Kallansa tai sannan tace " so nake nima na fara shiga irin ta kasata, d'an naga alama wasu kallan 'yar iska sukemin, wasu ma harda cewa......."
Kallanta dayai yasa ta kasa karasa maganar, baisan sanda ya saki wani murmushi ba, jitai zuciyarta ta buga, da sauri ta d'auke kanta tace " ehem, Jal me kakema dariya?"
Kallanta yakarayi da murmushi a fuskarsa yace " da alama kin k'ulaceni."
Baki ta turo ta d'an harareshi tace " ina tausaya yama matarka, zatai fama."
Jalal ya had'e rai yace " waya baki pass d'in hirar matata? Bayan b'an yarje miki ba?" Kallanshi tai cikin b'acin rai ta kafeshi da ido, wayarsa datake kara ya d'aga ganin ansa Zainab yasa ya d'aga da sauri.
Seemah da itama taga sunan jiki yasa ta juya kai jikin window da sauri ta had'iyi wani yawu tarasa dalilin ta najin ba dadi.
Jalal ya d'aga wayar tare da amsa sallamar da akamai, ya cigaba" Zainab ya akai? Jikin Zaheedan ne?"
Cikin sanyin muryarta ta amsa "a'a yaya k'ira nai inji jiya ya ka isa Abuja?" Yace " Lfy lau Alhamdulila, Abba fa?" Tace " ya fita d'azu." Jalal yace " keda ba kud'i kike dashi ba me makon kimin flashing?amma bari na kashe zan turo miki kati yanzu." Godiya tai sosai nan sukai sallama.
Seemah kam tanajinsu, da sauri ta juyo tace " kanada aure ne?" Jalal ya kalleta yace " meya dameki in inadashi ko bani dashi?" Itama ta had'e rai tace " me kuwa ya dameni, tausayin ta kawai nakeyi, kuma in kasan bata da kud'i a waya meyasa tun farko ka d'auka? Sai ka kashe sai ka k'irata kai kuma."
Jalal ya karasa gefen titi yai parking, yace " ina zan kaiki? Kim barni sai tafiya nake, kinzo kina shiga abinda bana tunanin ya shafeki."
Kallansa tai ta tab'e baki sannan tace " nasan garin ne? Ka kaini inda zan sai kayan kasar mu."
Girgiza kai Jalal yai yace " to ai banaji matata ce zatai fama dani, da alama kece za'ai fama dake." Cikin shagwab'a da b'acin rai tace " *YOU?*" Jalal yace " What? " juyawa tai kamar tai kuka, kara girgiza kai yai yace tab lalai.......
Wuse Zone ya wuce, ya shiga Bengari Street, a Sahad Store yai parkin, ta d'aga kai ta kalli store d'in, yace " sai kin fito, kuma karki kuskura ki shanyani a waje."
Kallansa tai ciki da mamaki tace "au ni kad'ai zan shiga?" Jalal yace " da ni ne mai siyan kayan? " leb'enta ta ciza idanta ya ciko tace " wai kai wani irin mutum ne? Yama za'ayi ka cusa mace cikin shagon da bata tab'a zuwa ba kuma ita kad'ai?"
Kallanta yai yace " a tunanina kawo ki kikace inyi bawai in rakaki siyayya ba?" A zuciye ta fito daga motar tare da rufo kofar da karfi, ta fara tafiya, murmushi yai sannan shima ya fito tare da rufe motar, a baya ya bita.
Seemah kam ran nan nata a had'e take tafiya tana shiga taja shopping cart tafara tafiya, jitai ance bana zakiyi ba, dasauri ta juya jin muryar Jalal cikin shagwab'a tace " Jal da saninka kenan?" Bai kulataba yafa tafiya, binshi tai tana tafe tana smiling, sunje wajen atamfofi dasu shadda da lesuka nan ta fara zab'a kallan Jalal tai dake tsaye yana danna waya, karasawa tai gunsa tace " Jal tayani zab'a." kallanta yai sannan ya cigaba da kallan wayarsa yace " ina duba time ne, minti 30 na baki ki gama zab'a minti 10 ki biya kud'i minti 5 mu koma mota minti 15 ta maidamu, so nake in koma office a cikin 1hr."
Kallan mamaki Seemah tamai a ranta tace harda wani lissafi? Hmm aikuwa zakaga 1hr.
Juyawa tai batare da ta kara magana ba, a hankali take duba kayan ta gama da kaya sannan ta kalleshi tace " inasan turaruka da kayan makeup,"
Agoggon hannunsa yaduba yace " kinfa cinye time d'inki anan." Tace "to ko in k'ira yaya ya nemarmin izinin wasu lokutan?"
Juyawa yai yace biyoni...
Nan ta fara binshi tana murmushin mugunta, juyawa tai taga yawanci maza ne ke jan cart d'in hakan yasa kawai tad'ansa kara kad'an tare da tsugunnawa, da sauri Jalal ya juyo yace lafiya? Kallansa tai tare da kallan kafarta data rik'e, ya kalleta yace bigewa kikai? Kai tad'aga tace " eh, sam bankula ba ina kallan wani abun na bige."
Jalal ya matso tare da cewa " ke da kika taso a England har akwai abinda zai sa ki kallansa har ki bige baki kula ba?"
Kasa tai da idanta, yace to tashi muje kima b'ata min tym, mik'ewa tai irin da kyar d'in nan yace muje to, har ya fara tafiya tace Jal? Cikin b'acin rai ya juyo da masifa yace " sunana wai kenan?" Kallansa tai ta kalli cart d'in tace " bazan iya ja ba."
Oh God!!!!! Jalal ya fad'a sannan ya karaso tare da ansa ya fara turawa, jitai dariya na neman ka mata haka ta d'aure tana d'an d'ingisa kafa, ta gama siyayyarta sai dai Jalal ya kullu sosai ganin a siyayya sai data kai 1hr, sunje gurin biyan kud'i ta mik'a Atm, Jalal kam kallan uban kayan data siya yake sai dai in ya tina yayanta waye sai yaga ba komai bane.
Sun fito Jalal rik'e da ledoji sukasa a booth, Jalal ya kalleta yace shiga muje, ga mamakinsa gani yai bata d'ingishi, kallanta yai harta shige mota inda ta zauna d'azu, a ranshi yace ni kikai fooling? Kwafa yai sannan ya shiga shima.
Baice mata komai ba sai dai fara tuk'i dayai, basuyi tafiya mai nisa ba yaga wani asibiti, gangarawa wa yai tare da yin parking a asibitin, Seemah da mamaki ta kalli asibitin tace" baka jin dad'i ne?" Murmushin mugunta yai yace muje, kallansa tai tace harda ni? Nifa banasan ko shiga asibiti.
Jalal yace " ni ce miki akai inasan shiga store?" Jin haka yasa ta bud'e motar a hankali ta fito.
Suna shiga akace sai sun sai kati, Jalal yace muna d'an sauri ne ba likita zamu gani ba allura kawai za'a mata ta tetanus, nan aka nuna masa inda nurses suke, ya kalleta tare da mata alama da hannu, suna shiga ya kalli nurses d'in yace " bata d'an ji dad'i bane, ba big'e da karfe ne shine nake tunanin ko da abinda za'a mata ko allura ne."
Seemah da sauri cikin tsoro ta kalleshi, ba abinda ta tsana irin allura, cikin in ina tace " ahh ah ba big'e wa nai ba takalminane yad'en bugeni kad'an."nurse d'in tace " matso mu duba" ai tanajin haka ta fara baya baya, Idanunta suka kad'a Jalal ta kalla tace " Jal mu tafi please." Ganin yanda idanta ya kad'a yasa ya kallesu yace " kuyi hakuri inajin ni na d'aukaka abin maybe ba serious bane.
Tanaganin haka Seemah tai waje da sauri, Jalal ya karaso ya bud'e mota tana shiga ta d'au waya ta k'ira Ammar, yad'aga tare da cewa " Seemah na ya kke? Yau naji dad'i ana kirana."
Kallan Jalal tai sannan ta sa hannu tasa wayar a hand's free tace " Yaya Ammar saura kad'an yau a min allura."
Daga can b'an garen cikin tashin hankali Ammar yace " Seemah waya isa yasa a miki allura bayan bakyaso? Me ma yasameki? Ya Habib ne?"
Kallan Jalal tai tace " bashi bane wani d'an gadara ne."
Ammar yace " Seemah anya ana kula dake yanda ya kamata kuwa? Anya bazanzo dakaina ba? Ko kuma ke ki dawo ba?"
Jalal ta kalla da ya kafe ta da wani mugun kallomaka, ta murgud'a mai baku tacigaba" karka damu yayana I will take care of myself. " tana kai nan ta kashe ta kalli Jalal tace "what? Ka kaini asibiti a min allura? Shiyasa na nuna maka matsayina, banaji yayuna in sukaji me kamin zasu kyaleka tun balle wanda mukai waya dashi yanzu.
Jalal ya kalleta yace " da alama baki daddara ba kenan, har ni zakima pretending? Kisani aiki?"
Dariya ne ya kamata auuuu yanzu tasan dalili, darita tasa sosai, Jalal ya saki baki yana kallanta, tad'an tsagaita tace "ohhhh dama haka ne?"
yace " Do u just laugh at me? "
Dariya tasakeyi tace " au sorry, amma yazanyi dariya kake bani."
Jalal ya furzar da wani iska yace " mene? Dariya nake baki? Nid'in?"
Had'iye dariya tai tace " ni ai ban gane saboda haka ka kaini asibiti ba ai, amma lalai u r really funny."
Jalal jiyai kamar yasa ihu, kamar shi acemai funny? Bai kulata ba da karfi ya fizgi motar suka hau titi, Seemah a ranta tace " zakasan ni ka kai asibiti, ka gano weakness d'ina d'aya nima na gano d'aya, bakasan ama dariya nikuma banasan allura."
© *NWA*
��♀
No comments:
Post a Comment