����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣8⃣
Suna isa gida ta wuce da gudu d'akinsu tana zuwa ta fad'a gado ta cigaba da kukanta, Jalal kam sai kiranta yake a waya bata d'agaba, sam hankalinsa ya gaza kwanciya, Habib ma d'aki ya wuce ya zauna a bakin gado, ya rasa meke faruwa, da sauri ya d'au waya ya k'ira Sagir bayan sun gaisa ya tambayeshi ya labarin abokin ka kuwa? Sagir yace wa fa?
" Jalal mana, ni a wani gari yake ne?"
Sagir yai shiru yana mamakin tambayoyi sai can yace " a birnin gwari yake, yaron nan yallabai abin tausayi ne."
Habib yace " ayya iyayensa acan suke kenan?"
Sagir yace " eh nidai ban tab'a zuwa ba amma nasan talakawane sannan yana da kanwa da take kwance ba lafiya, yallabai yaron nan tare mukai makarantar jami'a ma tausaya mai kwarai, ga karatu ga sana'oi dayake saboda harkar makarantarsa dakuma iyayensa."
Habib yai ajiyar zuciya lalai Seemah batada hankali, amma a fili yace " na tausaya mai, iyayensa basa wani aiki kenan."
Sagir yace " gaskiya banaji, d'an inaji kamar mahaifinsa harkar ko gona yakeyi ne, bandai san takamaimai me yakeyi ba."
Habib yace " okay Allah ya rufa asiri, sai da safe." Yana kainan ya katse layin tareda rik'e kai, lalai Seemah yarinta na damunta, ai ko Dad bai hanaba shi bazai bari ta aure wani Jalal ba.
Seemah kam ganin kukan ya isheta yasa ta mik'e zaune tare da d'auko waya d'an ta fad'ama ya Ammar, ganin missed calls d'in Jalal ne yasa ta saki wani murmushi sannan ta mai text, tana gun ya Habib ne suna hira.
Jalal na ganin text d'in yai ajiyar zuciya tare da kwanciya.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Duk yanda Dad yaso hankalimsa ya kwanta yai bacci abin ya gaggara sai juyi yakeyi, tunaninsa d'aya yazaiyi ya warware wannan al'amarin ba tare da Seemah tasha wahala ba? D'an bazai yadda da auranta da wani bare ba, kar azo maganar aure abinda yake a b'oye ya fito fili.
*Washegari*
Da wuri Jalal ya shirya ya nufi tasha, yai sa'a yana zuwa ya samu motar dazata birnin/gwari, nan ya shiga suka d'au hanya........
Seemah kam ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan data sha jiya, zama tai a kan gado, tana tunanin matakin daya kamata ta d'auka, Ammar da Junaid su kad'ai suka rage mata, da gudu Ra'isa ta shigo d'akin tace mata "Aunty kizo Uncle Ammar yazo." Cikin mamaki had'i da farinciki ta kalli Ra'isa, tace " Ra'isa dagaske kike? Ya Ammar d'inna ne yazo?" Kai ta d'aga mata, sam ta manta rigar bacci ce a jikinta da gudu ta diro daga kan gado tai falo tana zuwa ta kalli Ammar dake tsaye, ai da gudu ta fad'a kansa duk yanda yaso ya d'aure amma ina sai da suka fad'i kasa, Farida ta girgiza kai, wannan dab'iar fa? Seemah kam d'agowa tai ta kalli Ammar tace " Yaya sorry na yadda kai, amma yaya ya akai haka?"
Ammar yai murmushi sannan ya kalleta sai yanzu yaga kayan baccin dake jikinta, shara shara ne ana hango half-vest d'in data sa, yace " d'aga ni to, d'an naga alama neman karya wannan yayan naki kike."
Tai dariya tare da d'agashi tace " yaya tsaya d'an mintsineni a fuskata kad'an, so nake inji ko mafarki nake."
Dariya sosai tai sannan ya matso ya kama kumatunta da karfi sai datai kara, yace " ya? Yanzu kin gane?" Kara shigewa jikinsa tai sannan tace "yaya kamar kasan ina tsananin nemanka." Yai ajiyar zuciya tare da kallan gefe yace " yazanyi da kanwata? Ai in tana nemana dole jikina ya bani."
Ta zaro ido tace " dagaske kake yaya? Saboda haka kazo?"
Dariya yai har da zama akan kujera yace " lalai kanwata bata girma ba haryanzu zolayar ki nake."
Turo baki tai tare da harararsa sannan tace yaya bari nai sauri nai wanka zamuyi magana.
Ya d'aga kai, ta juya da sauri, Ammar ya bita da kallo fuskarsa d'auke da murmushi, wani sanyi ke ratsashi dayaga Seemah.
Jalal an isa gida lafiya a waje ya tadda Zainab tana wanke-wanke, kallanta yai cike da tausayi tana ganinsa ta mik'e da sauri tare da gyara hijab d'in dake jikinta, yana mamaki shidai ko a d'akinta take tanaji da hijab take zama, bai tab'a ganinta ba hijab ba, katseshi tai cikin murna tace " yaya? Kaine? Sannu da zuwa."
Murmushi yai yace " aiki kike?" Tai kasa da kai ya kalleta yace " sannu zainab, ana sanyi kina wanke-wanke a wajen nan?"
Ta kasa kawai dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta, umma ce ta fito tace " kaima dai ka mata fad'a Jalal, duk yanda nai da yarinyarnan tabarni nai amma bata yarda sam hanani komai takeyi."
Tausayinta ya kara kamashi, jiyai tace " Umma ina zan bari kiyi aiki? Bayan kema hutu kike bukata? Kullum kina gun Zaheeda kina kula da ita."
Umma tai dariya tace Jalal kajita ko? Jalal kam kallanta yake cike da tausayi, Zainab ta d'ago ta kalleshi ganin yana kallanta yasa tai saurin yin kasa da ido, tace " yaya ka shiga ciki sanyi akeyi." Kallanta yai ko rigar sanyi babu a jikinta sai hijab amma wai shida yake sanye da jacket tama cemai ana sanyi, matsowa yai kusa da ita yazare Jacket d'in ya mik'e mata yace " kisa" ta amsa tana kallansa, Umma ta saki murmushin farin ciki ya sani ko Jalal baisan Zainab bazai wulakantata ba, Jala kam yama gani ta amsa ya matsu kusa da Umma yace Umma mushiga, nan sukai ciki.
Kusa da Zaheeda ya zauna idannunsa sunyi jaa, itama idanunta na kansa, sai dai kana ganin alamun fuskarta kasan tana farincikin ganinsa, murmushi ya k'akaro tare da shafa kanta yace My Zahee kinyi missing d'ina ko? Idannu ta lumshe alamar eh, ya had'iye wani abu sannan ya juyo ya kalli Umma yace Umma ina kwana? Tace lafiya lau Jalaludeen, ya aikin?
Yace Alhamdulila, Umma ya jikin Zahee? Takalli Zaheeda tace gatannan dai jiya iyau, sai dai kwanan nan jikin baya wannan tashin.
Jalal ya kalle Zahee yace " Abba fa?"
Tace " yafita wai akwai wani mutumi dake neman masu mai lambu, shine sukaje shida Sani, Jalal ya gyad'a kai, yace " amma Umma kema ya kamata kid'inga hanashi wannan sana'ar da ba amfani take mai ba."
Umma tai shiru tace " kaima kasani bayasan zama guri d'ayan nan."
Jalal ya runtse ido yace " amma Umma kima ganin yanda kafarsa d'aya take? A dalilin me zai d'inga zuwa yanama wasu aiki bayan shi kanshi yana neman hutu? Sannan inya gama kwata kwata nawa suke bashi? Ya wuce dubu 1 ko 2?"
Umma tai shiru, Jalal yacigaba " Umma please ki taimaken ki hana Abba wannan yawon, in kuma lalai sai yayi sana'a ne, to ina ganin in na d'au albashi wannan watan mufara gina karamin shago a wajen gida inyaso in muka gama sai muji me yakesan ya zuba."
Umma ta kalleshi tace ka manta yace " bayasan kasuwanci?"
Cikin zafin rai da takaici Jalal yace " Umma wai menene dalilin dazaisa yak'i kasuwanci? Bayan muna halin rashi ne?"
Umma ya share kwallar data zubo mata tace " Jalal wani babban al'amari ya faru a shagon mahaifinka ne a shekaru masu yawa da suka wuce, 'yan garin nan suka sama shagon wuta, basu san me ya faruba bakuma su duba halin da maishagon yake ciki na bakin cikin abinda ya faru a shagonsa ba."
Jalal ya mik'e cikin b'acin rai yace" nasan wannan Umma, duk dabansan abinda ya faruba amma nasan wannan nasan kuma akan abunda ya farune kafarsa d'aya ta zama haka, sai dai tunda kinki sanar dani abinda ya faru bansan me zance ba"
Yai ajiyar zuciya yace" amma kome ya faru bakya ganin shekaru masu yawa sun wuce da za'a ajiye wannan al'amari?"
Umma ta kara share hawayenta tace " Jalal d'an Allah karkama mahaifinka zancen kasuwanci, ba'abinda ya tsana irinshi."
Jalal ya kalli Zaheeda da yaga hawaye na zuba ta gefen idanunta, sama ya kalla d'an boye hawayesa, ya tsugunna kusa da ita ya saki dariya" ha ha ha Zahee karki damu hira kawai muke da Umma ba wani abu bane kinji."
Umma ta kalleshi cikin tsananin tausayi, ganin yanda yake neman faranta ran kanwarsa yasa taji zaman yana neman ya gagareta, da sauri ta mik'e tai waje, Zainab da ta taho kawomai kunu da kosai, duk taji abinda sukai, ita kanta hawaye take sosai, ajiye kwanon tai ganin Umma ta fito, har zata bita taga kamar be dace ba, nata hawayen ta goge sannan ta shiga d'akin da fara'a, tace " Yaya kanaba Zahee labari ne?"
Ya juyo ya kalleta yace " sannu zainab. " ta zauna a d'aya gefen Zahee itama tana bata labari.
■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■
Seemah da sauri ta wanka ta zura kaya ta fito, akan dinning ta sami Ammar da ya Habib, taje kusa da Ammar ta zauna ta gaida Habib, Habib yace " baxan amsa ba tunda dai baki zauna kusa dani ba."
Ta kalli Ammar tace " Sorry Ya Habib naga tsohuwar zuma, kasan tafi zaki."
Ammar yasa dariya yace " Yaya sai dai kai hakuri kasan ni special ne."
Habib ya girgiza kai yace " lalai Seemah ni zaki ma haka ko? Shikenan nima zan rama."
Ta kalli Ammar tace " ya Ammar I miss you alot."
Ya shafa gefen fuskarta yace " ban yarda ba, bayan banga kin rame ba sai kiba danaga kinyi?"
Zaro ido tai ta kalli Habib tace " Ya Habib da gaske ban rame ba?"
Habib ya harareta yace " sai kiba dakikai kamar me...."
Ahhhhh ya zanyi? Ta mik'e ta shiga zirya tace ya Ammar ya zanyi? Kasan fa banasan nai k'iba? Noo bazanyi breakfast ba, ta kalli farida datai sakwalo tana kallanta, taje ta rik'e hannunta tace " Aunty azumi zan fara."
Habib da Ammar kam banda dariya ba abinda sukeyi.........
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
��♀
Tnx a lot
ReplyDeleteAgain....
ReplyDelete