Sunday, 11 December 2016

JALALUDEEN 1

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
     🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾





Na *AYUSHER MOHD✍🏻*


Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai.
Yanda zan fara rubutun nan lafiya, ina rokon Allah dayasa in gamashi lafiya, sannan abinda ke ciki na kuskuren Allah ya yafe mana, wanda muka fad'a daidai kuma Allah ubangiji yasa masu karatu su amfana dashi(Ameen).



Ina godiya ga masoyana akan kullawar da kuke nunamin.
Hope zaku biyoni danjin wannan labarin............luv u all😘



Episode 1⃣




Wani irin ihu ta sake mai tsananin kara, duk mutanen dake cikin gidan sai da hankalinsu ya tashi, mazan dake zaune a dinning suna breakfast suka kalli juna sai kuma suka mik'e da gudu sukai sama, masu aikin gidan suma duk suka hau gudu sai rige rigen hawa beni akeyi, mutum d'ayace bata ko d'aga kafar taba bare insa ran zatasa gudu kamar kowa, tsaki ma naga taja ta wuce d'akinta.


Sukam duk sun isa kofar d'akin da ake ihun suka shiga knocking jin kofar a kulle, babban cikinsu wanda ina tunanin ma mahaifinsune ya matso jikin kofar yace "my swthrt open the door please. "

Daga cikin d'akin cikin wata murya mai sanyi akace " Dad kaga fuskata kuwa? Banasan ganin kowa."
Kallan juna sukai shida mazan dake gun guda 2 sukai murmushi, wanda takira da dad d'in ya kalli wasu turawa dake sanye dakayan aiki kana ganinsu kasan masu aikine garin irin kayansu, ya musu alama da kai yace "Spare key."
Cikin sauri sukace "ok Sir."
Suka juya.


   Basu dad'e ba sai gasu sun dawo, dasauri suka mik'a makullin.

     D'an saurayin cikinsu ne wanda da alama shine karami ya amsa tare da bud'ewa, suka d'uru cikin d'akin dukansu, azaune suka ganta a kasa ta rufe fuskarta ta hannunta biyu.


  Dad yai murmushi ya karasa kusa da ita yace " My Swthrt meke ya faruwa? Bazaki bud'e ido ki kalli fuskar Dad d'in naki ba?."


   Cikin shagwab'a ta sauke hannun tare da bare baki tasa kuka tace " Dad kalli fuskar Princess d'inkafa?"

Dariya suka kunshe dukansu, d'ayan namijin yace " Wai! Wai! Wai! Seemah kin ganki kuwa? gaskiya na tausaya miki." Yafad'a tare da kunshe dariyarsa.

Seemah ta kalleshi tace " Yaya Janaid da gaske?" Takalli dad takara sa kuka tace " Dad dama na fad'a maka shi yasa banso kuka ganni ba."


   Dariya karamin yai yace " Ohhhh ni yazanyi? Kanwata takasa girma," ya fad'a tare ta tab'a kasan id'anta ya lakutu bakin abu, yace  " wannan ba Mascara bane Seemah? "

   Sai alokacin ta kalleshi tace " do u think so?"
Ya d'aga mata kai alamar eh,ta kalli masu aikin tare da mik'ewa taje kusa dasu, ta tsaya a kusa da d'aya tace "Anna mascarar dana sa jiyace tamin haka?"

 Anna tace "Sorry Madam it's my fault."

   Seemah takarasa jikin madubi ta kalli kanta kamar wata aljana da sauri ta rufe fuska takalli karamin saurayin tace " Ya Ammar to ya akai hakan ta faru dani? Jini fa? Zai fita ma kuwa?"

   Dariya sukai su dukansu, dad ya kamota ya zaunar a bakin gado, yace "Anna zo ki gyara mata fuska. "
Dasauri tace "ok sir"

   Ammar yace "amma meyasa kika kwana da kwalliya?bana hana ba?"
Ta turo baki tace "laifin Anna ne kullum in nai bacci ita take zuwa ta gogemin, amma shine jiya bata gogemin ba."

    Junaid yai dariya yace "da alama da asuba dakikai alwala duk ya zazzago miki, ke kuma shugabar bacci baki kulaba ki ka kwanta bacci."
   Tace" I think so yaya."
Dariya sukai dukansu.

   Dad ya mik'e ya kalleta yace " Swthrt zamuyi late bari mu fita."
   Tai murmushi tace "nima inada lectures yanzu zan shirya."
Shafa mata kai yai yace "yauwa baby na."

Suna fita Anna tashigo ta goge mata fuska sannan Seemah ta shiga wanka.



Su dad na sauka kasa suka taradda matar d'azu ta fito daga d'akinta, ran dad ya b'aci ya kalleta cikin b'acin rai kafin yai magana su Ammar suka ja jakarsu sukai waje gun mota, ya kalleta, itama tsoron mai zaice take.
    Ta d'aure tace "bakuyi breakfast d'in ba? na shiga toilet ne sai yanzu na fito."


   Dad ya maka mata hararra yace " Yanzu in wani abu serious ne yasamu Seemah sai ki wuce toilet?" Ta d'aure tace " it's a relief ai tunda ba serious bane."

   Yace " oh da kikai kamar baki sani ba? Kin kyauta." Ya fad'a tare da yin kwafa ya wuce waje.

   Tabishi da kallo tace  yau koma me za'amin na tab'o 'yar gwal? Sun bar yarinya duk tagama sangarcewa, datayi magana sai yacemata kar ta manta aurantama dayai saboda Seemah ne, tsaki tai ta wuce kitchen.



Seemah na fitowa daga wanka ta kure disco tana rawa tanasa kaya, Anna na tayata shiryawa, riga da wando tasa sanna  ta zura suwaita doguwa a sama tasa karamin nayafi ta yane kanta, ta fito tare da d'aukan karamar jakarta.


  A hankali ta sauko kasa ta kalli dinning kamar yanda masu aiki aka umarcesu, sun jera mata nata kayan abincin, ta karasa dinning ta bubud'e kwannukan, ta kalli matar dake zaune itama tana nata breakfast d'in tace " Small Mom banajin zan iya cin abinci, in dad ya kira ya tambaya please kicemai na ci."bata jira amsar taba tai waje, tana gyad'a kai.

   Haushi yakamata tace "Small mom? Da haka ki kirani da sunana mana Sadiya"

    Seemah na fita ta taradda driver ya gama goge mota yana tsaye yana jiranta, ta kalleshi tace " da wace mota zamu? "
   Dasauri ya nuna mata wanda yake tsaye, tsaki tai tace "ni bana santa kujerar cikinta basu da laushi sosai, muje a waccen." Tafad'a tare da nuna wata.

    Da sauri yace to madam.

Kallan garin tai tace " it's snowing."

   Takarasa ta shiga mota suka fita daga gidan.

Garin England yau sun tashi ana ruwan kankara sai dai sukam mazauna garin sun saba da wannan rayuwa, hada_hadar su kawai sukeyi, nikam banda rawar sanyi ba abinda nakeyi, nace kaii! Ina zan iya rayuwa a nan? Seemah na kallah dako ajikinta, nace uhmm keda aka haifeki anan dama.......wayarta ce takatseni datai kara, da sauri Seemah tad'aga ganin sunan dake jiki Big Bros.
 
  Cikin shagwab'a tace " Yaya Habib."
   Yace " Princess dafatan kin tashi lafiya?" Tace "lafiya lau Bros bayan kak'i zuwa?"
Ya kalli matarsa dake kusa dashi yace "Ai zuwa zai ban wahala yanzu d'an company d'in dad na bukatata sosai."
   Seemah Tace " dama za'a barni inzo im ganka, If you think it yaya ban tab'a zuwan garin iyayena ba, gashi kai yanzu ka koma can, sannan su Ya Junaid da Ammar suna zuwa duk bayan 5 month haka ma Dad amma ni bandani."

    Habib yai murmushi yace "gaskiya kam, kunyi hutun skul?"
Cikin zumud'i tace "yau zamu gama exams, kasan kuma inmun gama shikenan an gama zuwa sai an dawo."
Yace "Good, zan ma Dad magana yabarki kizo ko 1 month ne kimana."

   Dakarfi tace " *YESSSS* Kai Bros shiyasa nake sanka sosai."
Nan sukai sallama akan sai ya tambayi dad.

  *************************
Seemah cikin farin ciki ta isa makaranta, ra k'osa taga ya Nigeria take, suna isa ta sauka daga motar tare da shiga cikin skul d'in, tana taka kafa zata ciga class d'insu taji ansa ihu ana fesa mata spray, mamaki ya kamata ta kallesu zatai magana taga abokinta Alex yazo kusa da ita yayi knell down tare da miko mata flower, yace " Seemah will you date me?"
  Ihu yan class d'in suka sa suna tafi suna cewa " ACCEPT IT!!!!!!"
  Kallan Alex tai cikin mamaki tace " Alex what's going on? "

    Ya kara m'iko mata flower yace " Seemah please accept my love."
   Kallansa ta sake yi ta d'an tab'e baki tace " Alex will you stop all this drama?"

   Alex ya mik'e tare da cewa " Seemah!!!"
  Hararsa tai sannan tace " do I look easy to u? Meyasa kowa yake neman raina min hankali? Rannan Abokin ka yazo min da zancen yana sona, yau kuma kai? Am I a toy to u? "
   Alex zai yi magana ta amshi flower hannunsa ta kalli wata  mate d'insu datake sanshi, kowa na skul d'in ya sani har shi Alex d'in ta ajiye mata flower a gabanta sannan ta kalleshi ta wuce ta zauna, Alex ya bita da kallo, abokanansa sukace kaima kasani ai yarinyar nan datakejin kanta kamar 'yar gidan sarauniyar England itace zata so ka? Get a hold of yourself buddy!!!.......



 
   Tana zama waya ta d'aga tama Ammar text, tana ajiye wayar ya kira, yace " Princess ya akai? Ki kace wani ya miki proposing?"

   Tace " eh mana yaya wai kuma ka san wa? Alex fa?"
   Dariya yasa yace " yanzu ya akai?" Tace " ya akai kuwa? I reject him kaima kasani yaya Alex is not my type."

Dariya Ammar yai tace " nifa yaya wanda zan aura dole ne sai ya cika abubuwa guda 5, na farko kyau, na biyu ya d'inga bani respect, na uku bai isa yamin abinda zai b'atamin raiba, na hud'u ya zama mai kud'i d'an ni ban taso a babu ba, na biyar in har nace kaza to lalai sai an min."
  Ammar yasa dariya sosai yace " anya kuwa zaki samu duka?" Tace "umm wait an see yaya I will definitely find him."

    Ammar yace kai amma na kosa inganshi.
Dariya itama tai tace "yaya plz kasa baki a barni naje Nigeria. "
Yace "ok ba matsala, ai kin kai 20yrs ya kamata dad ya barki."
Tace tnx Yaya

   Ammar yace "ki share kiyi exams d'inki a nutse."
 Murmushi tai tace "ok tnx Oppa".

 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡

   Zaune yake a gaban mahaifiyarsa ga kanwarsa dake kwance bata da lafiya, tun tana 'yar shekara 10 ciwo ya kamata, take a kwance har yau Allah bai bata damar mik'ewa ba, komai yi mata ake.
   Goge mata bakinta yai da miyau yake zuba, ya kalli umma yace " umma ina tunanin tau zan koma."
  Tace " Jalal in ka tafi wannan karan ka d'inga bari sai sati bibiyu, daga Abuja zuwa binin_gwari da nisa."

   Murmushi yai yace" zan duba, amma Abba fa? Naga har zan tafi bai dawoba."
   Tace "yaje kai Zainab kauye ne gun iyayenta, ta damu tanasan zuwa," tai shiru can tace jalal nikam har yanzu baka duba maganar dana cema ba? Na auren Zainab?  Kaga 'yar uwace gata ba ruwanta."

   Jalal ya mik'e tare da cewa " Umma bari na wuce, zan kiraki a waya."
Takalleshi tare da cewa "to Allah ya kiyaye hanya."


*Jalaludeen* kenan talakawa ne sosai sai dai mutum ne shi da bayasan a rainashi dan bashi da hali, kuma baya tab'a kaskantar da kanshi akan wani mai hali, baya d'aukar raini, ba kuma ya so a rainashi.


**************************


Seemah na gama exams da sauri ta shige mota dan batasan su had'u da Alex tana shiga, ta kira yaya Habib, yai murmurshi yace " lalai na yadda kanwar nan tawa ta kosa tazo ta ganni"

   Seemah tace " yaya ya kukai da dad?" Yace "ya ce ba matsala indai zan kula dake."

Ihu tasa tace" wow yaya amma nifa tunda na gama exam so nake a satin nan, in fact gobe ko jibi na k'osa inganka."
  Habib yace " bakomai zan duba flight na kusa nima na k'osa inga my kanwa."








By *Ayusher Mohd*
@ *NWA*

No comments:

Post a Comment