Sunday, 11 December 2016

JALALUDEEN 3

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
  🐾 *JALALUDEEN*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾







Na *AYUSHER MOHD*








NO 3⃣








    A hankali Jalal ya mik'e ganin minti 30 d'in tayi, tsaki ya sakeyi yace amma Sagir ya ci mutuncina.

    Kallan 'yan uwansa nagun aiki yai yad'an sosq k'eya yace " zan d'an fita gun wani friend d'ina."

  Sukace sai ya dawo, waje yai yana cewa haka kawai da mutuncina an sani karya, makulli ya amsa tare da tambayar security d'in ina motar take? Nan ya nuna mai, ya kalli motar tayi kyau sosai, bud'ewa yai ya shiga tare da jaa....

   Ya isa airport sa alokacin yashiga tunanin wai ma yazaiyi yasan itace? Zuwa zaiyi yai ta tambayar mutane Seema ko me? Shiru yai can yace " Seemah? Amma sunan kamar ba na kasar nan ba, yai kama dana india, to amma Sagir yace wai kanwa" yai shiru a ranshi yace da alama Sagir d'in bai fahimta bane.


    Ya dad'e a zaune baiga jirgi ya sauka ba, haushi ya isheshi ya kalli agoggo kusan mintinsa 30 kenan da zauwa, haushi ya isheshi ya mik'e zaiyi hanyar waje, karar jirgin dake alamar sauka ne yasa ya koma ya zauna.

    Kallan mutane ya shigayi wad'anda sukazo d'aukar 'yan uwansu, to shi wai ya zaiyi ya ganeta? Ganin mutane sun fara tahowa yasa wata idea tazo mai, juyawa yai yaga wasu rik'e da manyan abu d'auke da sunayen wad'anda sukazo tarba, a ranshi yace nima bari nai haka.

   Jakarsa ya bud'e ya d'auko littafin rubutunsa, ya gutsuro takarda karama, tare da rubuta Seemah da biro a jiki.
A zahiri in ba kazo kusa ba bazaka tab'a ganin me aka rubuta ba.

Nikam dariya ne ya rufeni ganin wata 'yar takarda d'auke da sunan Seemah gashi sai kunyar rike takardar yake da kyar ya d'aure ganin zai b'atama kansa lokaci yasa ya d'an rike da hannun hagu.

    'Yan jirgi sun fara fitowa,  Seemah kam duk ta gaji a jirgi ta fito sanye da glass ta cire rigar sanyin datasa ta jacket ta rik'e a hannunta, ga takalmin da tasa mai masifar tsinine, rigar jikinta takai gwiwarta sai wando pencil dake jikinta, tasha jambaki pink, gaskiya tayi kyau sai dai tunda ba al'adarmu bace hakan yasa kowa take kallanta, itakam ko ajikinta.

  Raba ido kawai take taga an rubuta Seemah a katon symbol wanda zai d'au hankalin mutane, sai dai duk wanda ta leka sai taga ba sunanta, mamaki ya kamata nan tace ko dai yaya yana kunyar rubutawa ne? Nan ta shiga duba mutane ko zata ganshi, mamaki ne ya kamata ganin har ta iso gun da mutane ke tsaye suna jira bataga yayanta ba.


  Jalal kam ya baza ido sai neman ba india yakeyi, sai dai turawa kad'an da suka fito.

   Seemah da sauri ta kunna wayarta, sakon yaya ne ya shigo na zai shiga meeting amma ya turo a d'auketa, haushi ya kamata tace " akwai meeting d'in daya fini mahimmanci ne?...."
Maganarta ce ta katse ganin wata 'yar karamar takarda wani saurayi sanye da coat yana rik'e dashi, dariya ne yazo mata tace " lalai wasu basuda mutunci, yanzu wannan 'yar iskar takardar da ita za'a tarbi mutum? Da alama dai mutumin nan ko bashi da mutunci ko kuma mammako ne ya mai yawa.

   Hartazo kusa dashi tana d'an duba mutane, to ta ina zata gane d'an aiken? Ga wayar yaya a kashe, idanta ne yakai kan rubutun dake jikin 'yar takardar, in batai kuskure ba *SEEMAH* taga an rubuta, wani kululun bakin cikine ya ziyarceta, badai ita Seeman ba d'an itakam tasan tafi karfin wannan takardar.

    Karasawa tai kusa dashi, daidai nan shikuma wani Sagir ya kirashi, Jalal ya d'aga cikin kunnar rai yace " Sagir me kad'aukeni? Tun d'azu ka aikoni d'auko wata banza itakuma tana neman b'atamin lokaci, ce maka akai banda aikin, yi ko me?"

   Sagir yace " Sorry Jalal yanzun ma ba gama meeting d'in mukai ba, Chairman ne ya kalleni, hakan yasa na gane so yake yaji maganar kanwarsa, dagani yanaji da ita."

 Cikim zafinrai Jalal yace" me yadameni da wani ji da ita dayake? In hakane ya bar meeting d'in yad'aukota mana, ni mubar wannan maganar, india ce kome? Naji kace Seemah?"

   Seemah dake tsaye tana jinsa bakin ciki yazo mata wuya, ita ake ciwa mutunci?

   Haushi ya kamata ta juya ta kara juyawa nan taga wani rike da d'an karamin cup da alama ko lemo ko ruwa ko tea yake sha, ajiye trolly d'inta tai ta karasa gun mutumin, addu'ar ta d'aya Allah yasa tea ne mai zafi.

   Tana isa gunsa tace sannu bawan Allah, ya kalleta ganin shigarta yasa yad'an had'iyi yawo, yace " mekikeso madan?"

  Murmushi tai tace " please abinda kake sha nake so, "
Da sauri ya mik'a mata cup d'in ta kalli ciki, tea ne mai madara yaji milo sai dai abin haushi ba zafi sai dumi dai kawai, godiya tai ta juya tai gaba shikuma ya bita da kallo.


   Seemah na isa kusa da mutumin, sai ta juya kai kamar bashi take kallo ba, shi kuma ya zak'e sai fad'a yake a waya sam bai kula da itaba, Seemah na matsowa ta saita takalminta ta takamai kafa da karfi, zai juyo ta kwaramai ruwan tea a cikin kayansa wajen farin coat d'in na ciki cikin tsananin mamaki Jalal ya d'ago d'an ganin wace 'yar duniyar ce wannan? Yana d'agowa Seema ta kwad'amai jacket d'inta, da karfi ya zare jacket d'in takard'ar hannunsa ta fad'i.
 Cikin wani irin takaici yace " wani irin hauka ne wannan?"
   Kallansa tai shima ya kalleta, tab'e baki tai tace " Sorry ban kula ba."
Tafad'a tare da juyawa, da karfi Jalal ya d'amko hannunta ta tsaya tare da d'an kara d'an taji zafin damkar, ta juyo tace " Malam wani irin rainin hankali ne wannan? Sakeni ko?"

   Jalal yai wani mugun Murmushi yace " me da me kika ce?  Bakiga ke abinda kika min ba?" Ya fad'a yana kallan kayan jikinsa ga kafarsa dake zafi.

  Tace "sake ni ko? Kai meye dalilinka na tsaya a hanya? Ko nan gidanku ne dazaka tsaya kana gulmar mutane a waya. "

   Jalal yazabura yace " Gulma? Ke tsaya in ma gulmar ce meye naki a ciki? Ohh shine kikamin haka da sanin ki kenan ko me?"

   Seemah ta kalleshi tace sakeni ko? Jalal ya zare hannunshi tare da cewa " tambayar ki nake? Meke damunki? Kuma a wani dalilin zaki min haka? Banasan rainin hankali kuma akanki bazan jura ba, kawai kiyi godiya d'aya ke macece dabadan haka ba I don't know what will happen. "


   Seemah ta makamai harara tace " ka kuma d'auko jakar ka taho mu tafi."

   Jalal kam ranshi ya kai matuka gun b'aci yace " what?"

  Seema tace "kanaso in kara fad'ane? Ko ba Seemah kazo d'aukaba?"

 Jalal yai wani murmushi yanzu ya gane wai itace  yace " ko ita nazo d'auka bata isa tasani ind'aukar mata jaka ba, d'an banaji nid'in mai aikinta ne." Yafad'a tare dayin gaba yace " kibiyoni zan jiraki a mota."


   Seemah ta bishi da kallo tare da d'anyin kara tace " wannan wani irin mutum ne? Wayyo bakin ciki zai kasheni."
Yazatai? Haka taja jakarta, yana tsaye jikin mota takarasa fuskarnan a had'e duk da da glass a idanta.


  Jalal  ya shiga mota, itama ta karasa ta shiga baya ta zauna, lalai ba shakka sai ta gyarama mutumin nan zama, shi harya isa? Shid'in wa?

   Tafiya suka fara bamaima kowa magana, shi haushinshi ma maidashi driver datai, Seemah kam waka tasa a wayarta ta kuma kuri volume, Jalal ya juyo tare da ciro earphone ya cilla mata yace " malama yi amfani da wannan banaso a cika min kunne."

   Cillamai a binsa tai tace " sai kuma naga kamar ba a kanka nake ba, sannan ta kalli motar ganin abin bit da ta ba yaya habib a jikin madubin gabar motar yasa tace "sai kuma naga motar yayanace bana tunanin kanada iko da ita."

   Jalal yai tsaki  tare da juyawa, yanaji bai tab'a ganin mace 'yar rainin hankali irin wannan ba.

   Seemah ta kauda kai a ranta tace wannan wani irjn mutum ne? Da alama kuma ba wani kud'i gareshi ba ganin coat d'in jikinsa bamai tsada bace.

  Yana talaka shine zai raina mata hankali? Tafi karfin a wulakanta, ita datakesan taga kowa na mutuntata yana santa shine yau zata had'u da wannan wanda ko kwayar mutinci bataji yanada shi.





By *Ayusher Mohd*
© *NWA*

No comments:

Post a Comment