๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ *Jร
ฤนรฤนรฤฤฤร*๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Na *Ayusher Mohd*
No 7โฃ
Seemah dake zaune a mota ta bishi da harara. Jalal kam yana ganin motar har tazo kusa dasu ta tsaya, Sagir da sauri ya bud'e motar yazo gun Jalal yace " Jalal tana ina?" Kallansa yai sannan ya kalli motar hakan ya sa Sagir yagane tana motar kenan, da sauri yakarasa motar ya bud'e baya tare da kallanta, ba tantama itace da sauri ya gaida ita, ita kanta kallansa take da mamaki ta amsa tare da tambayar " kai ma accomplice ne?"
Da sauri Sagir yace " a'a Ranki ya dad'e, yanzu ya k'irani na taho, amma ya akai haka?"
Kallansa tai sannan tace " kai waye da zakamin wannan tambayar?" Sagir yace " baki gane ni ba? Secretary d'in yallab'ai ne."
Kallansa tai tare da kauda kai gefe tace " maidani gida."
Da sauri Sagir yace " to ranki ya dad'e yanzu ma kuwa."
Fitowa tai nan taga Jalal a tsaye, ta harareshi tare da kauda kai gefe, Sagir ya kalli Jalal yace mutafi.
Jalal ya kalleshi yace ina? Sagir yace gida mana.
Kallan Seemah yai yace " so kake laifina ya shafeka? Na tab'a 'yar gwal kana tunanin zan bari laifina ya sha feka?"
Sagir yace to yaza'ayi Jalal?
A ranta ta na nata sunan *JALAL* *JALAL* *JALAL*
Jala yace " manka za muyi sharing a motar in yaso sai in maidata da kaina."
Sagir yai shiru amma shikam yasan tabbas da matsala, in har Habib yagansu bayaji Jalal zai tsira da aikinsa.
Seemah ta kalleshi tace " nidai ka barni na tafi, banasan tafiya da kai sai dai in kuma wani abun kake shirin yi min."
Jala ya watsa mata wani kallo yace " ni na ba kaina makulin motarki? Ko kuwa kidnapping d'inki nai? A iya sanina ke da kanki kika shiga mota kika kuma bani makulli, so I don't think kinada hujjar da zaki yanke hukunci akan wannan maganar."
Seemah wani kululun bak'inciki ya kamata ta bugamai wani kallo, wani k'arin bak'incikin kuma ko kallanta baiyi ba magana ma yake da Sagir, jitai kamar tasa ihu d'an bakin ciki.
Shikam sun sa tiyo sun d'an zuk'i man motar Sagir suna gamawa Jalal ya kalli Seemah yace wuce muje ko? Takalleshi tace "in naki shiga fa?" Jalal ya kalleta yace "ko zaki gwada ne kiga abinda zai biyo baya?"
Sagir ya kalli Jalal yace "Jalal ka d'inga hakuri d'an Allah."
Sannan ya kalli Seemah yace " kiyi hakuri ranki ya dad'e haka yake hakuri muke dashi muma."
Jalal ya kalleshi yace " Sagir banaso karkasa yarinya karama ta rainani." Yanakainan ya juya sai dayaje wajen motar yace kizo mu tafi dare na yi.
Sagir ya kalleta yace " kiyi hakuri Madam haka yake, a hak bazaki gane ba amma Jalal mutum ne nagari sosai." Kallansa tai ta tab'a baki wayaga na gari, ju yawatai itama takarasa motar, ta bud'e ta shiga baya.
Jalal ya tada mota ya hau kan titi, sunyi nisa sosai ba wanda yace komai, can Seemah ta d'aure tace " dama d'an kawai ka ci mutuncina ka jani a motar? Ko d'an na cemaka driver?" Jalal yai shiru can yace " tambaya kike?"
Haushi ya kamata tace " ba tambaya nake ba, ina dai tausaya maka ne na shirin dakai ya ruguje."
" Bana tunanin yarinya dake harkin kai matsayin dazaki rugujemin shirina." Ya fad'a yana kallan titi.
Tad'an matso da kanta jikin kujera sannan tace "ina tausaya maka abin da zai faru dakai." Jalal yad' an waigo kad'an yace " bana tunanin kinkai shekaru 20 in case in ma kinkai bana tunanin kin wuce, kinga kuwa baki kai lokacin tausaya ma wani ba sai dai ke atausaya miki."
Turo baki tai kamar tai kuka cikin shagwab'a tace " Wlh kacigaba da abinda kakemin, karkuma kai tunanin tsoro nake ji."
Baisan sanda yad'anyi murmushi ba yace " da alama ke mammah girl ce."
Tanajin haka tai shiru, idanunta suka cika da kwalla, Jalal jin shiru yasa ya cigaba da tuk'insa, anfi minti 5 da maganar jiyai tace " Banda mahaifiya ai, ban ma santa ba zance." Itakanta batasan meyasata fad'amai ba d'an a zahiri ko 'yan skul d'insu basu sani ba.
Shiru yai jikinsa yai sanyi, tausayinta yakamashi da kuma maganar dayai, ya rasa mai zaici, shikanshi mamakin kanshi yai dayaji yace " Bakomai ita dama rayuwa haka take, mutum baya samin komai, Allah yajikanta."
Kallansa tai idanunta taf da kwalla, sun shiga garin Abuja ya kalleta ta madubi yace " kinsan gidan?" tace " bazan gane ba gaskiya ban tab'a zuwa kasar nan ba sai jiya."
Juya kai yai yace " bana tunanin na tambayeki ko kin tab'a zuwa."
Tace " What? Kai wai wani irin mutum ne da ba'a iya maganar mutunci dashi?."
Jalal bai amsa mata ba ya d'aga waya ya kira Sagir nan yamai kwatance, sun kusa isa gidan Jalal ya kalleta ta madubi a ranshi yace da alama bata tab'a shan wahala irin ta yau ba, dan yaga harta fuskarta ta canza.
Ajiyar zuciya yai, shi kanshi yasan yayi laifi, Seemah ce ta katseshi da cewa dafatan ka fahimci kwatancen na gaji da wannan zirga_zirgan.
Jalal ya kalleta yace " to ko ke zaki zo ki jamu?" Tace ni driver ce? In fact ni ko mota ban tab'a tunanin koya ba."
Jalal yace " karki kuskura kisa a ranki wai d'an na ja ki a mota kina baya yana nufin nid'in driver d'inkine, sai dai hakan na nufin banasan zama guri d'aya......."
Katseshi tai tare da murgud'a baki tace " whatever banasan jin komai nidai ka kaini gida."
Jalal yad'anyi murmushi daga gefe sannan yai kwana, suna zuwa kofar gidan yai parking tare da juyowa ya mik'a mata key, ta amsa tare da kallan gidan, jitai yace " badai bakisan inda kika kwana ba?" Hararsa tai tare da d'an murgud'a baki kad'an tace " ce maka akai ban gane ba?"
Kofa ya bud'e batare da ya amsa mata ba ya juya ya fara tafiya, da sauri ta fito tare da cewa *JAL* cike da mamaki ya juyo jal? Meke nan? Daga inda yake yace " Jal? Da wa kike?"
Cikin wata murya tace " bazan iya fad'an sunan duka ba yamin yawa."
Murmushi yai kad'an yace " waya fad'a miki sunana? Kuma ni sunana in baza'a fad'a duka ba banaji zan iya amsawa."
Tad'an tab'e baki tace " ka ce baka da kud'i dame zaka karasa gida to?"
Yace " Don't tell me u are worried about me? "
Tace " wa? Ni? Allah ya sauwake."
Juyawa yai yacigaba da tafiya kawai yasamu kansa da murmushi.
Itama murmushin tai sannan tai knocking. ........
โงโงโงโงโงโงโงโงโง
Habib kam yakasa zaune ya kasa tsaye ko ruwa ya kasa sha masifa kuwa farida harta gaji itada Aisha, kowa yai jugum banda waya ba abinda yakeyi.
Mai gadi na bud'ewa cikin mamaki ya kalleta yace " kamar Hajiya ko?"
Seemah tace nice, nan ya bud'e mata yana cewa ina kika shiga Hajiya sai cigiyarki ake.
Bata amsa mai ba tai cikin gida, tana shiga ta murd'a kofar a hankali, tare da turawa, dukansu sun kurama kofar ido suna san suga wanene, ga mamakinsu Seemah ce ta shigo, da gudu Habib ya karasa cikin tsananin mamaki, yana zuwa ya rungumeta, ya shiga tambayarta Seemah ina kika shiga? Kinsan yanayin da kika sani? D'agowa yai ya kalleta yaganta tana lumshe ido, yace Seema are u alright?
Kafin ya kara cewa wani abun yaga tayi baya luuu ta fad'i.
Farida ta taho da gudu nan suka shiga jijigata, Habib yace a k'ira likita.
Sun kaita d'akin sun kwantar, Aisha taji wayar Seemah na kara, karasawa tai ta d'au wayar gani tai ansa *Special Bros* d'agawa tai jitai ance "Seemah na wato kinzo gun yaya kin manta dani ko?"
Aisha a hankali tace ba ita bace, Ammar da mamaki yace " waye? Ina Seeman?"
Aisha tace "hmm ta shiga toilet zan fad'a mata inta fito."
Yace alright yana kai nan ya kashe wayar.
Aisha tabi wayar da kallo ba shakka anaji da yarinyarnan kod'an yanda taga yaya Habib yayi.
By *AYUSHER MOHD*
ยฉ *NWA*
No comments:
Post a Comment