Friday, 16 December 2016

JALALUDEEN 15

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 1⃣5⃣

 
*_Washegari_*
  Habib ya nutsu a office yana aiki, wayar Dad ce ta shigo da sauri ya d'auka tare da gaidashi, Dad yace " kunje Sulejan?"
  Munje d'azu Habib yai maganar cikin damuwa, cikin tsananin tsoron abunda zai faru Dad yace "ba dai abinda ya faru a can d'in ko?"

  Habib najin haka yace " Dad ka fad'amin gaskiya kama su Hajiya laifine? Ko Seemah ce ta musu?" Jikin Dad yai sanyi abinda yake tsoro kenan shiyasa ya hanata zuwa kasar cikin sanyin murya yace " zanzo nan da 2wks amma karka fad'ama Seemah zanzo inje Sulejan sannan sai mu dawo da ita.

  Kafin Habib ya kara wata maganar Dad ya katse layin, da mamaki yabi wayar da kallo, meke nan?

    Seemah kam tun safe take a kwance akan gado ta kasa tashi, tanaji Aisha ta tafi skul, Aunty Farida ma tace zata fita daga nan zata duba ko an gama d'inkinta, itakam tana cikin bargo banda san ganin Jalal ba abinda ke damunta, ganin abin bazai cinyeba yasa ta mik'e da sauri ta fad'a toilet tai wanka, kayan Aisha ta duba ta d'auko wani had'aden material dinkin yayi kyau sosai ta saka sannan ta d'aura d'ankwali simple taduba mayafin daya shiga da kayan tasa ta fito, a waje taga Bala suna hira da nai gadi tace " Bala kaini gun Yaya."
  Nan suka mik'e suka fito, Suna isa ta kalli Bala tace ka hau taxi ka koma gida kabani key d'in akwai wanda zai maidani." Da mamaki ya kalleta alamun tsoro ya bayyana a fuskarsa yace " Hajiya ai......" katseshi tai dacewa kuma karka fad'awa kowa inda nake zan koma gida da wuri.
  Ta amshi key d'in tare da mik'amai 500naira tai ciki.

  Inda suka had'u jiya tai tana shiga elevator ta d'aga waya tama Jalal text " Rooftop. "
  Jalal dake zaune suna meeting na sabon project d'in da zasuyi jin karar text yasa ya d'aga waya yana gama karantawa ya d'ago suka cigaba da meeting d'insu.

   Seemah kam ganin har minti 10 bai zoba yasa ta kara mai text tace "inajira fa."  Jalal ya karanta text d'in suka cigaba da meeting sai dai wannan karan sam hankalinshi yarabu kashi biyu, yanzu ne yagane waye ke jiransa, manager ya kalleshi yace " Jalal kanaji kuwa naji kayi shiru bayan kaike bayani tundazo."

  Kallansa yai yace sry mu cigaba, nan suka cigaba sai dai yanzun ma yana yi yana kallan wayarsa, ganin hankalinsa ya ki kwanciya yasa ya kalli Manager yace " please ina zuwa."
Yana fad'ar haka yai waje da sauri, ido suka bishi dashi suna mamakin yau Jalal ne ke neman excuse ana meeting?

  

  Jalal kam da sauri shima ya nemi elevator ya hau yana tsayawa ya fito da sauri tare da karasawa kusa da kofar, sai dayad'an tsaya kad'an kafin ya bud'e kofar a hankali, sai dai yaga wayam ba kowa, cike da mamakin ko harta tafi, ya shiga ciki yana fubawa, a zaune ya ganta akan d'an karamin baranda d'in da akai agun ta sa kanta a cinya, ji take kamar tasa ihu, kamar ita ace tazo neman Jalal amma ya shareta?

  Kallanta Jalal yai tare da jingina da bango idanunsa na kanta, Shi kansa baisan tunanin me yakeyi ba, Seemah kam ganin ba ha za  yasa ta mik'e da niyyar tafiya tana d'agowa tayi arba da kafar mutum daga d'an nesa kad'an da ita kallansa tafara daga kafa ahankali takai kan fuskarsa zuciyarta nata harbawa, tana kallan kwayar idanunsa ta lumshe ido ya d'auka ko shirmen da takeyi ne na ganinsa, karkatar da kai Jalal yai tare da cewa " kin k'irani kuma bakice komai ba."
   Idanu ta zaro a ranta tace dama shine? Hancinta tad'an ja da hannu kamar me mura tad'an juya kai tace ka ga dama kazo? Dana d'auka bazaka zo ba ai.

   Kai Jalal yad'an jinjina yace " alright tinda bakiso nazo ba bari na juya." Ya fad'a tare da yin kamar zai tafi, da sauri tace  " ina kuma zaka?" Juyowa yai tare da had'e rai yace " inda na baro mana."

  Cikin wani salo da ita kanta bata san ta iya ba tace " karka tafi plz."

  Kallanta yai cike da mamaki me take nufi? Karasowa yai kusa da ita sannan ya zauna kusa da ita kad'an yace " me kike nufi da kar in tafi?"

  Kallansa tai sannan ta juya ta kalli gabanta tace " banda abokin hira so nake muyi hira da kai."

  Murmushi ya saki yace " ni abokin hirar ki ne? Ko kim manta ke kikace ba'a iya hira dani?"
  Baki tad'an turo tace " ai dagaskene wani sa'in ko wace magana zaka fad'a sai ka fad'i wacce zata kona ran mutum. "

  Yace " Ahhh tunda haka ne mai kuma zai sa a nemi yin hira dani?"

Ta kalleshi tace wannan kuma ai........sai kuma tai shiru, fuskarsa ya karkato inda take yace " wannan kuma me?"
  Da sauri tasa hannu ta rife fuskar ta tace " yaushe kake tafiya gun matarka?"

  Dariya yad'anyi kad'an yace " me kika gani?"

  Ta sauke hannunta tare da cewa " nasan dai kamar ba a nan suke ba ko? Amma ka dad'e dayin auren ne?"

  Ajiyar zuciya Jalal yai  yace" banajin yazama dole in sanar dake sirri na."

  Hararsa tai cikin jin haushi tace " rike zancenka banamaso." Tafad'a tare da juya baya tacigaba" laifinane ma dana kawo kaina."
   Mik'ewa yai yace " bari in tafi naga kamar fad'a kike ji, bana tunanin da bakina na tab'a ce miki inada aure." Ya juya ya fara tafiya da sauri ta mik'e tasha gabansa tace " me kace? Banji da kyau ba."

   Jalal ya kalleta yace " amma ke yarinyace sosai ko?"
  Tace " me ka gani?" Yace " me kika gani kika ce inada aure? Bayan bana tunanin na tab'a fad'amiki hakan da kaina?

  Ta harde hannu tace hmm ni bansan ya ake gane mai aure ba sannan naga bakafi sa'an yaya Ammar ba to naji a Nigeria da wuri akema mutum aure shiyasa nai tunanin haka.

  Dariya yad'anyi kad'an hakwaransa suka fito yace " a da kenan ko? Mu ma yanzu ba kowa bane ke aure da wuri."

   Murmushi ta saki ganin ta kasa rufe baki yasa Jalal yace " menene na farin ciki d'an banida aure?" Juya mai baya tai takarayin murmushi itakanta takasa controlling d'in kanta Jalal ya dawo ta gabanta tare da matso da fuskarsa saitin idanunta ta zaro ido tare da d'anyi baya ya kara kallanta sannan ya d'aga yad'an kalli kefen fuskarta yace " Don't tell me you. ..?"
   Da sauri cikin rawar baki tace " tell you what?" Duk ta rikece ya kara kallanta tare da kankance ido yace " anya?"
   Seemah ta kara had'iyar yawo ta girgiza kai tace " anya me? Me kake sakawa a ranka wai?"

  Jalal ya nuna ta da yatsa sannan yace " u? Sannan ya nuna kansa yace me?"

  Seemah ta shiga hura iska tace " bafa haka bane kadaina wannan tunanin."

" u look suspicious, badai abinda nake tunani gaskiga bane?"

Saurin juyawa tai tare da tsugun nawa ta toshe kunnenta da hannuwanta biyu, Jalal yai murmushi sannan ya tsuguna kusa da ita yace " a bar maganar nima naga kamar it doesn't make sense."
  D'agowa tai tace " ko? Ka gani kaima ko?"

Ya d'aga kai alamar eh yace " bari na koma office."

   Seemah ta kalleshi tace " zuwa naifa in ka gama abinda kake ka kaini inga gari." Kallan daya mata ne yasa tace " Please." Murmushi yai yace " shikenan bari inje in dawo ki jirani a nan.

   Itama murmushi tai tace to.

  Mik'ewa yai ya fito, sai dai har ya isa office murmushi bai bar fuskarsa ba.



© *NWA*

��‍♀

3 comments:

  1. It's my 1st time reading JALAL..and am enjoying it yeah! Ve read ur recent 'labari'"ZUCIYA"-it was awsome..keep the good work!

    ReplyDelete