🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
No6⃣
Seemah duk tagama rud'ewa kafin a isa birnin/gwari har ta gaji da kuka tayi shiru, sai ajiyar zuciya take, jalal kam na isa lungun gidansu yai parking d'an mota bata shiga gun, ya juyo ya kalli Seemah kwarai tabashi tausayi, shikanshi baisan meyasa yamata haka ba, daurewa yai yace " Kid'an jirani kad'an."
Kafin tai magana ya fita tare da kulle motar tsoro yakara kamata mr zai jeyi? Jijiga kofar tashiga yi sai dai yariga ya kulleta.
Jalal kam da sauri ya karasa gida, Umma na zaune a barandar tayi shiru tare da zuba tagumi, Sallamar dataji ne yasa ta mik'e, Jalal ya shiga da sauru tare da rik'e hannunta yace " Umma ya jikin Zaheedan? Umma ta kalleshi tace " Jalal menene hakan? Ya akai ka tahu yay bayan kasan yau kanada aiki?wama yafad'ama bata da lafiya?"
Jalal bai maganaba kawai yazare hannunsa daga gun Umma yai hanyar d'akin kanwarsa, a kwance yaganta yanda dai take, ajiyar zuciya yai sannan ya rike hannunta idansa taf kwalla, bacci takeyi hakan yasa bayan yagama mata add'ua ya fito daga d'akin, Umma ya kalla yace " meya sameta umma? "
Umma ta kalleshi cike da tausayi tace " Jalal bafa wani abu bane, kawai d'azu ne ta shiga yin jijjiga, sai kuma kumfa data d'inga fitowa daga bakinta, amma ana kiran likita ya dubata, yace bakomai yana mata allura kuwa tadaina."
Ajiyar zuciya yai ya kallin hanyar toilet jin motsi, Zainab ce d'aure da zane sai hijab datasa da alama daga wanka take, kallanta yai, itama da sauri ta gaidashi, ya amsa sannan ya juyo ya kalli umma yace " zan wuce inada abinyi, sannan kicema Abba zan turo kud'in."
Umma ta kalleshi tace " to Jalal Allah ya tsare." Juyawa yai da sauri Zainab tace " yaya?" Juyowa yai batare da ya sake rai ba, tad'an matso, ganin haka yasa umma tai ciki.
Kanta a kasa cikin nutsuwa da hankali tace " Kayi hakuri yaya laifinane." Yace namefa?
Tad'ago a hankali tace " natasoka na fad'amaka Zaheeda batada lafiya."
Fuska yad'an saki kad'an yace " nagode sosai kuma inaso in wani abun ya faru ki d'inga fad'amin kamar yanda kikai yau."
Kai tad'aga tare da cewa " Allah ya tsare.
Juyawa yai yai waje da sauri ya koma mota, ga mamakinsa mutane ya gani a gun, cikin sauri ya karasa gun tare da tambayarsu lafiya? Kallamsa sukai suka kalli maccen dake cikin mota tanata bubuga glass, hakuri ya basu yace " batada lafiya ne asibiti zan kaita.
Jin haka yasa suka wuce tare da musu sallama.
Jalal ya shiga mota tare da kallanta, duk ta gama rikicewa, wani tausayinta ne ya kamashi, me ya kaishi yin haka, kasa magana yai kawai ya juya mota suka fara tafiya sunyi nisa sosai kafin Seema ta d'aure tace" har yanzu bamu iso inda kake shirin lalatamin rayuwar ba?" Kallanta yai ta glass ya d'auka tagama tsorata lalai yarinyarnan wato fitsara dai bazata daina ba, bai amsa mata ba hakan yasa ta shigaba, " kada kai tunanin zan tsorata akan wani banzan sharri dakake shirin yimin, sai dai ka makaro dan ni bana shakkar komai, sqi tausayinka danake, d'an in ka bari yayana ko mahaifina ya kamaka?" Tai ajiya zuciya tace "I don't think you will go away easily. "Tafad'a tare da yin kwafa.
Murmushi yai a ranshi yace " she is bold, wato ko tana tsoro bataso ta nuna?."
Seemah kam zuciyart fal take da tsoro, sai dai batason raini.
Sunyi nisa sosai d'an baifi saura 1hr su isa Abuja ba, mota tafara nuna musu danger, Jalal ya kalleta yarasa mai zaice ga ba kud'i a gunshi, ya d'aure yace " ba mai a motar, zaki iya ban aron kud'i?"
Kallanshi tai sannan tasa wata dariya, tace " What did you just said? " ran Jalal ya b'aci yace " ban fito da kud'i ba ga magrib ta kawo kai ko so kike muyi dare a hanya?"
Tsaki taja tace " wannan matsalarka ce kuma, ba dare ba mu kwana ma mana ni ina ruwana."
Haushi ya kamashi, ga motar tama fara kokarin mutuwa, gashi gun daji ne, parking yai a gefe sannan ya juyo ya kalleta sannan ya nunata da yatsa yace " don't you dare do that to me again, d'an ba abinda na tsana irin a min tsaki, bare ke mace macema yarinya."
Dariya tasake yi kad'an tace " in kuma na sake fa? Me zakamin?" Tafad'a tare da matse kafofinta dake d'an rawa.
Ya harareta yace" ko zaki gwada?" Ta murgud'a mai baki tace " oho kuma yau ina tausaya ma dan watan barin aikinka ya kama."
Jalal ya juya yana kallan titi ya zasuyi? Ganin zaman bazai mai amfani ba yasa ya fita tare da fara tsaida motocin da suke wucewa, sai dai abin haushi duk ba wanda ya tsaya kowa wucewa kawai yakeyi.
Seema dake zaune a mota ta makamai harara tace" kalleshi kamar na kwarai, kirjinsa takalla, da sauri tai tsaki tace "irin wad'an nan mutanen nafi tsana a rayuwa ta masu nuna su na Allah ne bayan kuma ba haka bane a ransu."
Jalal ganin abun yaki ci yaki cinyewa gashi magrib har tayi yasa ya dawo mota yai shiru, wayarsa ya d'aga wa zai kira to? Shi duk abokanansa ba wani abota bace ta kud da kud kowa in ya ganshi da yarinyarnan zarginsa zaiyi.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Habib kam da rana ya k'ira Farida d'an jin lafiyarta, itakam cike da mamaki tace " Seemah ai tun wajen 12 ta taho gunka office." cikin tsananin mamaki yace " Farida mai kike nufi da wannan zancen? Wani irin Seemah tazo? Bayan ni ban ganta ba? Kuma wama zai kawota? D'an nasan bata iya driving ba."
Tsoro yakama Farida tace '"tare suka fita da Aisha bari na kirata inji."
Da sauri Habib ya kashw wayar ya kara k'iran wayar Seemah datun dazu bata dauka ba.
Farida tak'ira Aisha itakam nan ta sanar da duk abinda ya faru.
Farida cikin tsoro ta kashe kafin takira Habib yasake k'iranta, yace " ya sukai?" Cikin tsoro ta shiga fad'amai abinda akai.
Yana gama ji ya kashe wayar tare da jawo coat d'inshi take lankaye, yasa ya fita da sauri, nemanta ya shigayi sai dai abin tambayar? Wanene wanda auka tafi taren? Itadai Aisha batasani ba bare kuma su Habib.
Nan aka sanar da Security's na Company d'in aka shiga nemanta, har police station aka sanar mawa, ganin abun yaki cinyewa yasa aka baza cigiya gidan radio da Tv.
Hmmmmmmm
●●●●●●●○●●●●●○●●●●●○
Jalal kam kansa ya dafe, can ya juyo ya kalli Seemah dake rik'e da ciki da alama yunwa takeji, shikanshi yunwa yakeji, fita yai daga motar ya rufeta yai d'an dajin, bishiyar mango yagani rigarsa ya cire ta sama ya hau kad'owa, ba laifi ya samo guda 5 sakosu yai a rigarsa ya koma mota, yana zuwa ya mika mata, ta kalleshi tare da hararsa tace " ce maka akai yunwa nake ji?" Kalanta yai yace " im ba yunwa kikeji ba ki barsu."
Yana gama fad'ar hakan ya bud'e mota ya fita, Seemah ta harareshi tare da jawo mango d'in nan ta shiga sha.
Shikam wayarsa ya d'auka ya k'ira Sagir, Sagir na d'agawa yace " Mutumin ina ka shiga?" Jalal yace " ba wannan ba da matsala fa, yarinyar nan fa na tare da ni."
Cikin rashin fahimta Sagir yace wacce? Jalal yace wace nad'auko jiya.
Cikin tsananin mamaki Sagir yace " What? Jalal meke faruwa? Dama kaine wanda kuka fita tare? Kasan yanda ake nemanta kuwa? Jalal in akasan kaine da......."
Katseshi Jalal yai yace " man mota ya kare inaso ka sanar azo a d'auketa ko kai kazo ka d'auketa, nan ya mai kwatance ya kashe wayar.
Sagir yabi wayar da kallo, bai tsaya wani tunani ba ya zari key. ......
Seemah kam sai datasha guda 4 tad'aga na karshen zata sha sai kuma ta kalli Jalal dake tsaye a waje gashi da alama sanyi yakeji yanda taga yana takurewa,zuge glass d'in motar tai tace " ungo na k'oshi? " kallanta yai sannan ya juya kai gefe kamar bai jita ba, tai tsaki tace " mutum sai rainin hankali,"
Komawa tai ta zauna tace oho cikin wa? Can kuma tace ba dai poison yasamin ba? Da sauri ta kalleshi sai kuma tace " ah ai kayan fruit ne" can kuma tace in yai injecting d'in mango d'in fa da poison? Sai kuma tace "kaiii yaushe har ya fita dashi, Can kuma tace wayyo in kuma ya shirya fa? Da sauri ta bud'e motar taje kusa da shi ta mik'amai mango d'in, ya kalleta tare da juya kai, kallansa tai tace " wato magani kasa min na guba ko?" Kallanta yai kamar ya? Ta kara mik'amai tace " sha in gani." Kansa ya kara juyawa sannan ya mik'a mata rigar coat d'insa takalleshi tare da kallan rigar, sai dayai d'an nisa kad'an yace " nafi karfin nasama mutum guba, sannan kisa rigar d' an na tsane inga mace da irin kayan nan tana tallar kanta."
Ha! ha! ha! What? Talla? Leb'enta ta tad'an ciza sannan ta kalli coat d'in.
Mota suka koma ba wanda yai magana can Seemah tace " wai anan kake tunanin zan kwana?" Jalal baiyi magana ba" tace namanta da jakata ne nima ban fito da kud'i ba, bai kulata ba, ganin haka yasa ta mik'amai coat d'insa tace "nima nafi karfin sa wannan rigar."
Baiyi magana ba ya fita ganin kamar mota na nufosu.
By *Ayusher Mohd*
© *NWA*
No comments:
Post a Comment