Sunday, 11 December 2016

JALALUDEEN 5

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ
     ๐Ÿพ *Jร…ฤนร€ฤนร™ฤŽฤšฤšร‘*๐Ÿพ
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ






Na *AYUSHER MOHD*



  *NO*5โƒฃ



_*This page is dedicated to you Beely Badaru*_๐Ÿ˜๐Ÿ˜




    Sun fito rike da hannun juna, kana ganinsu kasan suna cikin tsananin farin ciki, suna tafe ana gaidasu, sai gulma da mutane sukeyi ganin abun banbarakwai,nan suka shiga motar Habib, suna baya driver na jansu.

  Seemah takalleshi tace "yaya amma d'azu ba wannan bane yazo d'aukana?"taimaganar tana nuna drivern da ido, Habib ya kalli mai tukin sannan yace mata" yaje gida ne d'azu  'yarsa ce bataji dad'i ba."
  Ta d'aga kai tare da tuno birkin da ya ja ta k'umu, kallan Habib tai tace " amma yaya wannan waye?"
Habib yace " bansani ba gaskiya."da sauri tace " yaya ban gane ba?"

   Habib yace " Sagir nasa ya tura wani ya d'aukoki."turo baki tai cikin shagwab'a tace " au yaya kanwar taka zata dawo bama kasan waya tafi d'aukota ba?"

    Ta juya kai tare da hard'e hannayenta, dariya yai yace " kanwata ayi hakuri ko sai na kira Dad ya bada hakuri a madadi na."

    Har suka isa gida Habib na lallab'ata suna shiga daga gate tashiga kallen gidan, gida ne karami daidai saidai tsarin gidan yayi kyau sosai, suna parking wata had'ad'iyar mace ta fito da wata kuma sa'ar Seemah,  suna tsaye daga jikin kofa suna murmushi, Seemah ta kallesu ta tabbatar matar yaya Habib ce dan taganta a hotuna, sai dai wace take sa'arta ce bata san ko wace ba.
 
    A hankali suka karasa gun da sauri matar yayan ta karaso tare da rungume Seemah cikin tsananin farinciki tace " Kanwata sannu da zuwa, naji dad'in ganinki sosai."

   Seemah ta saki murmushin dad'in taji dad'in yanda aka nuna mata so, yaran suka taho da gudu su biyu mace da namiji, Seemah ta rungumesu tace "  Ra'is da Ra'isa sai yau naganku."

   Sun dad'e kafin matar habib tace muje ciki kanwata.

   Sun shiga ciki, nan sa'ar seemah taja jakar seemah tai ciki da ita,  kallan matar yayanta tai tace " Aunty Farida amma kanwarki ce ko? Naga kama."
Daga mata kai tai tace " D'aukota nai d'an kiji dad'in hutun anan kinsan in akwai sa'arka kafi jin dad'i" dariya Seemah tai tace " naji dad'i Aunty amma ya sunanta?"

 Jisukai ance " Aisha Mohd Rabi'u" da sauri Seemah ta juya tare da dariya tace " Aisha irin wannan fad'ar suna har ka ka?" Nan sukasa dariya dukansu.

   Tayi sallah sannan aka jera abinci kala kala a dinning,  Sun zauna Seemah tai murmushi tace " Auntyna duk wannan na welcome ne?" Habib yace " I Farida na sanki sosai seemah tanaso kizo, yanzu tunda kika samu zuwa kuwa ai ba dama...........



    Sun gama cin Abinci suka shiga d'aki suna hira, duk da ba sabawa sukai ba amma Aisha na kok'arin janta da hira, itadai ba wani sakewa take ko jin dad'in hirar takeyi ba, tunanin cin fuskar da aka mata yau takeyi,  aiya sanin rayuwarta sai dai ita tacima mutum mutunci badai ita a mata ba, tai shiru tana hango sanda ya kumeta a kujera, wai sorry?

  Jitai Aisha ta tab'ata tace kinajina? Seemah tace " naga magrib ta kusa bari na shiga wanka, amma nikam garin nan sam ba sanyi."

    Aisha ta kalleta da mamaki tace "sanyi kuwa, ke bakyaji?"
Seemah bata amsa mata ba ta shiga toilet, Aisha ta bita da kallo tace " sai a tambayi mutum kuma inya bada amsa sai ta shareshi" tsaki tai tace nifa bansan rainin hankali.

   Seemah na fitowa bayan tayi sallah batare datama Aisha magana ba kawai ta fita daga d'akin.
  Su Ra'is ta jiyo kamar suna wasa, hartaje zata shiga taji Yaya yace " kanwata?" Da sauri ta juyo tare da murmushi tace " yaya? Ashe kana nan?"
 Alama yamata data karaso, dasauri taje inda yake, tare da cewa" yaya nima ina san irin kayansu Aunty Farida."
  Cikin mamaki yace " Atamfa?" Tad'aga kai yace " ba matsala in yaso gobe sai kuje ke da ko Aisha ne."
 Hannunshi ta rik'e cikin shagwab'a tace " ni da kai nakeso yaya." Tafad'a tare da turo baki.

   Ya saki ajiyar zuciya yace " shikenan in yaso gobe ina tasowa daga gun aiki sai muje." Tace eh yayana.
Sun dad'e suna hira kafin Farida ta iso itama ta shiga aka cigaba dayi da ita.

    Seemah ta mik'e zata tafi tace " yaya yaushe kuma zani gurun iyayen su mumy na da dad?"
   Habib yai shiru, can yace "  zan tambayi Dad."
  Seemah ta kalleshi tace Ok
 **************************


    Seemah ta kwanta da niyyar bacci sai dai ta rasa dalilin dayasa ta kasa, tai tunanin hala canjin guri ne d'an tunda aka haifeta a can take.
  Wayar Ammar ce ta shigo, da sauri ta d'aga  yace " kin kasa bacci ko?" Tace " yaya shiyasa nake sanka dayawa, kasan ni sosai."
  Cikin wani yanayi na tausayi yace " to yanzu ya za'ayi?" Tace "oho kasan yanda zakai kawai inyi bacci nidai."

    Dariya yai sosai sannan yace bari na baki story, nan ya shiga bata labari hartai bacci jin shiru yasa ya kashe wayar tare da sakin wani murmushi shima ya kwanta.

    *********************

  Da safe Seemah sai 11 ta tashi, tana tashi tai wanka sannan tasa kaya ta sauko, su Ra'isa har sun tafi makaranta,  sannan Aisha bata d'akin, a falo ta gansu suna hira, ta karasa tare da gaida Farida,  cikin sakin fuska ta nuna mata dinning sannan tad'an harari Aisha, nan Aisha ta juyo tare da k'akaro murmushi tace " Seemah kin tashi? Aunty ta hanani cin abinci wai sai kin taso."

  Cikin ko in kula Seemah tace " Aunty da kin barta ai ni nafisan cin abinci ni kad'ai indai har bada family's d'ina bane." Ba Aisha ba har farida taji haushin wannan maganar sai dai bata nuna ba.

  Seemah kam ko a jikinta ta wuce dinning taci abinci,tana gamawa ta taso ta dawo falon tace " yaya na office ?" Farida tace eh, Aisha ta kalleta ta sannan tace " nima yanzu zan fita skul ina da lectures by 1 zanje da wuri d'an akwai abinda zanyin."
   Seemah tad'an kauda kai ko meta tuna sai kuma ta juyo tace " nikam Aisha kin iya driving? " Aisha takalli farida tace " inadai koya." Seemah tace" mu fita tare inyaso sai ki ajiyeni a office da motar sai ki hau Taxi." Aisha ranta yakara b'aci amma ganin yanda farida tai yasa ta d'aure tace " towa zai dawo dake? " inada driver acan ai abinda Seemah tace kenen, Farida tace " gun Habib zaki? Memakwan ki zauna muyi hira?"
"Am sorry Aunty akwai abinda nakesan yine a can."
Nan ta mik'e.

Aisha ta bita da harara tace kamar in kifa mata mari nakeji wlh.
Farida tace " banasan haka Aisha ki rufan asiri wannan yarinya akanta Habib zai iya sakina."tana kai nan ta mik'e tare da mik'a mata key tace kuma kuyi a hankali kinga baki da licence.
*************************

 Sun fito sun shiga mota,Seemah ta shiga baya, Aisha bakin ciki ya kamata sai dai ya zatai?  sai da sukai d'an nisa Seemah tace " namanta phone d'ina a gida." Aisha tace mukoma ne?
  Seemah tad'an kauda kai tace " mutafi kawai."

  Sun kusa isa office zasu  shiga kwana sam Aisha bata kula da wanda ke kokarin shigowa ba, da karfi ta taka burki, Seemah tad'an gwaru da kujera, cikin b'acin rai tace " Aisha meye hakan? " Cike da tsoro Aisha tace " Seema wani na kusa kad'ewa.........bata karasa maganar ba taji anyi knocking d'in glass d'in motar inda zake, cikin tsoro ta zuge, wanda aka kusa kad'ewa cikin had'e rai yace " muga licence d' inki?" Miyau ta had'iya tace " hmmm namanta da shi  gida,"
  Seemah dake jinsu sai dai tana tunanin wannan muryar, Aisha kam kallansa kawai takeyi, kwarjinshi ya hanata magana sosai, kirjinsa takalla, mai fad'in gaske da gani yana motsa jiki ganin yanda jikinsa yake da fad'i, jitai an katseta ance " in baki iya mota ba meye naki na ja? Ku mutane sai ku d'inga abu ba tunani." Da sauri Aisha tace yahakuri, cikin b'acin rai Seemah ta bud'e bayan motar tafito, idanunta in bai mata k'aryaba mutumin jiya ne, kuma ga mamakinta coat d'in nan ta jiya ce kawai dai an wanketa ne, Jalal ta kalleta sarai ya ganeta amma bai nuna mata ba ya kalli Aisha yace " you hav to be careful." Ya juya zai wuce.
   Da karfi Seemah cikin takaicin yanda ya shareta tace " Kai driver?" Jalal ya juyo cikin b'acin rai sannan ya karaso inda take ya junata da ' yatsa yace " kisan me zaki d'inga fad'a niba drivernki bane kuma bana tunanin zan zama d'aya."

    Seemah tai wani murmushi tace " ko zanyi doubling d'in albashinka?" Tafad'a cikin salon rainin hankali, Jalal haushi ya kamashi batare da ya amsa mata ba ya juya zai wuce, da sauri Seemah ta riko hannunsa tace " Who gave you permission to live? According to whom? "

 Jalal ya kalleta tare da zare hannunshi yace " According to me." Yana kainan ya juya, da sauri Seemah ta sha gabanshi tace " malam magana fa nake, a ka'idata in ina magana dole ne a tsaya in gama  kuma dole ne a ji, d'an haka ka wuce muje ka karasa dani Company d'in yayana." Jalal zaiyi magana yaga text ya shigo mai, shiru yai idanunsa suka kad'a sukai jaa, meya sami kanwar sa? Gashi daga office yake ko kud'i bai fito da shi ba, jiyai Seemah na cewa " Driver dakai nake magana wato kaji zancen doubling d'in kud'i shine ka kasa kagana ko?" Ta kalli Aisha dake tsaye tace bani key ki wuce skul d'in.
  Aisha ta mik'a mata ita kuma ta mik'ama Jalal dake tsaye duk tunaninsa ya kule, kallan key d'in yai yace " meye hakan?" Tace " ka wuce muje ko?"

   Jalal ya kalleta da alama sai ya gyara yarinyarnan, key d'in ya amsa yace " muje ko?"  Murmushi tai tace " aikin kawai a ido kamar kud'i bazai rinjayeshi ba, dama ai hakane d'an adam inyaji kud'i?" Ta saki tsaki, Jalal na jinta yai kwafa tare da shiga mota, itama ta shiga baya.


Jalal ya fizge mota ya juya yai hanyar fita daga gari, Seemah ta kalleshi cikin mamaki tace " ina kuma zamu? Duk da ni ba ' yar garin bace amma nasani kwarai nisan company d'in bai kai haka ba."

   Jalal ko kulata baiyi ba kawai gudu yakeyi tunaninshi d'aya meyasamu kanwarsa da har zainab ta turomai sako???????

Seemah kam ganin sun bar gari kuma gudu yakeyi yasa tsoro ya fara kamata, ta fara masifa, malam meye hakan? Me kake nufi dani? Ina kake k'okarin kaine?

 Jalal bai kulata ba tafiyarsa kawai yake, Seemah ta shiga ihu, ta d'auka ko fyad'e zai mata ko wani abun, tunda ita batasan ana satar mutane ba, duk masifa da ihun datake Jalal bai kulata ba, gashi bata d'auko sayarta ba, a hankali ta shiga bashi hakuri ganin tsoro ya kamata da gaske Jalal yace " Sorry akwai inda zani ne,ba wani abun zan miki ba."
   Cikin hawaye tace ina zanyarda dakai? Bansan gari ba kazo ka fita dani kawai kana gudu dani a titi, kayi hakuri in har haushi kaji nacema driver.

JALAL bai sake magana ba, itama tun tanayi har ta gaji ta takure a gefe har suka isa binin/gwari, Jalal ya karasa gidansu yai parking tare da rufeta a mota, ya wuce ciki, kuka take sosai itakam tasan yau karshen rayuwarta yazo.









BY *ร€YUSHER Mร’HD*

๐ŸŒโ€โ™€

No comments:

Post a Comment