Tuesday, 20 December 2016

JALALUDEEN 21

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 2⃣1⃣


  A wani katon gida suka tsaya, mai gadin da sauri ya bud'e motar tare da mika gaisuwa, sunyi parking sannan Habib ya kalli Seemah yace muje ko? Kallansa tai idanunta sunyi raurau kai ya d'aga mata alamar it's okay.
  A hankali ta zuro kafarta ta fito, nan suka jero tare da nufar gidan.

  Bayan sunyi knocking aka zo aka bud'e wata yarinya ce wanda a haife batafi Seemah ba, tana ganin Habib ta saki fara'a tace " Yaya Habib yau kaine a gida?"

   " Tafi shan ni ba ruwana dake ai." Ya fad'a tare da shiga, Seemah na biye dashi.
Matsawa tai d'aya gefen tace " Haba yayana na kaina ai nasan bazaka iya fishi da ni ba."

  Kunnenta ya kama tasa kara tare da cewa yaya Habib da zafi fa? Seemah ce ta kalleshi ta saki fuska tace " kai yaya Habib daga isowa sai a fara da cin zali? Amata hakuri."
    Sakinta yai yace " kinci darajar kanwata mai daraja."
   Kallan Seemah tai tace " badai mai darajar nan wannan sakaliyar kanwar taka ba.....?"

  Hararar da Habib ya maka mata ne yasa tai shiru kallam Seemah yai yace " kyaleta kanwata wannan da kika ganta batajin magana."

   Jisukai ance lale maraba da Habibullah, juyawa sukai inda maganar ke fitowa, wata babbar macece wanda kana ganinta kasan takai misalin shekara 50, sai dai tasha kayanta ta kuma d'aura d'ankwali abinta dagwas, fara'a ce sosai a fuskarta Habib ma fuska ya saki sosai ya ja hannun Seemah suka karasa gunta, zama tai suma suka karasa suka zauna a kusa da ita a kasa, Habib ne ya gaida ita sannan Seemah, ta amsa tare da cewa " Zara na neman hanaka hutawa ko?"

  Kallan wacce aka kira da Zara yai yace ai Ummy wannan yarinyar tana bukatar bulala a gurina.

   Dariya suka saki dukansu, Ummy tace tashi ki kira Abbanku, nan ta mike tana cewa yaya habib zanzo Allah, amma sai yaya Ammar yazo kasar.

Da mamaki Seemah ta kalleta Ammar? Habib ne yace " Gwara ma kizo d'an Allab ba wai saboda Ammar ba kinfi kowa sannan yace bayayi dake."

  Da sauri ta karasa b'angaren Abba fuska a had'e, tana dawowa, Abba na shigowa, Abba shima ya taho yana farinciki, Ummy yaji tace " Habib wannan fa? D'an ban tab'a ganinta ba?"
  Murmushi Habib yai yace " Kanwa tace Seemah." Ummy ta maimaita Seemah? Seemah?
  Abba dake tsaye idanunsa suka tashi daga farin ciki, su ka kad'a sukai jaa, sunan yake maimaitawa a ransa da kuma abinda ya faru a baya, abinda ya ruguzama kaninsa rayuwa ya kuma tada hankali duk zuri'arsu suka zama abin nuni ga duniya, yana tsaye Zara tace "Abba yaka tsaya anan?"

   Juyowa sukai dukansu suka kalleshi Habib ya saki Murmushi ya mik'e tare da tahowa gunsa, Ummy kam tunda taji sunan itama jikinta yai sanyi, shiru tai kawai tana kallan Seemah.

  Habib na zuwa kusa da Abba ya kama hannunsa tare da cewa " Abba na dade banzo gaisuwa ba ko?"

  Kallansa Abba yai idanunnan jawur, zaiyi magana sukaji ance " Hello My Ummy Ur Son is back." Gaba d'aya kowa ya juya ya kalli kofa, saurayine da baifi su Ammar ba sai dai yasha kayan nigogi kana ganinshi kaga saurayin dake ji da kansa, idanunsa nakaikan Habib ya karaso da sauri yace "Hello Bros long time no see"

  Baki Habib ya saki sannan ya kalleshi daga sama har kasa yace " Zaid kanannan a yanda kake, nikam yaushe zaka girma?"

Baki yad'an karkata irin salon ' yan gayo maza d'in nan zaiyi magana idanunaa suka kai kan Seemah da sauri yakarasa kusa da ita ya matsa daf da ita yana kare mata kallo, itama kallansa tai tare da  kokarin matsawa,  mikewa yai yace Wow ummy she is just my type.

  Idanu Seemah ta zaro tare da kallansa, Zaid ya kanne mata ido d'aya dasauri tai kasa da kanta, gun Abba ya koma yace " Abba kumin aure please,  nan da 1 week inasan auran yarinyarcan."

   Cikin tsawa Abba yace " Ashe haryanzu zaid bazakai hankali ba? Daga ganin yarinya kawai kafara min zancen banza? Kasanta ne? Ko kasan tsatson ta?"

  Kowa sai daya tsarata a falon.

  Cikin rashin fahimta da raahin jin dad'i Habib yace " Abba baka tambayeni ba ai, Kanwatace fa, Seemah."

  Abba ya kalleshi cikin bacin rai sai kuma ya juya ya koma ciki da sauri, Habib ya bishi da kallo, Seemah kam tumda take yauce rama ta farko da tsawa ta girgizata, jitai idanunta sun ciciko, Zara ta kalleta tace " Yaya Habib Gimbiyarku na neman yin kuka da alama bata sabajin tsawa ba."

  Da sauri Habib ya taho, Zaid yasa gudu ya rigashi zuwa, kusa da ita yakara zama shima kamar me shirin kuka yace " Babyna kiyi hakuri, haka sirikinki yake sai dai nima na dade banga b'acin ransa haka ba, but karki damu tunda ni inasanki zan kareki daga komai."

   Matsawa Seemah tai baya kad'an tana mai kallan mekakeyi hakan? Ummy ce tace " Zaid ka bari mana." Tafad'a tare da mikewa tace Habib inasan ganinka.

  Nan suka juya, Zara ta girgiza kai tace Seemah ina tausaya mikk kin had'u da cingam d'an manne, itama ta mik'e ta bar falon.

Zaid ya kara matsowa gun Seemah yace " Babyna nasha wahala gurin nemanki,meyasa kika wahalar dani sai yau kika bayyanamin kanki?"

   Seemah ta kalleshi da mamaki tace " ni kuma? A ina ka tab'a ganina?"

  Jitai ya damko hannunta yakai saitin zuciyarsa yace " anan baby na."

  Da sauri ta fizge hannunta tare da nik'ewa tace " Banasan haka."
  Shima mikewa yai yace me kikeso to? Fad'amim in miki cikin gaggawa.

  Harara ta makamai tace " Zaid kake ko? To bari kaji nifa ba ka ra gareni ba, sannan ba tsoro gareni ba, wannan abin da kakemin bakomai bane illa sallon  yaudara ta samari masu ji dakansu, saidai me? Am sorry d'an na riga na gano lagwanka, bakuma na tunanin hakan zaiyi tasiri a guna."

    Kallanta yakeyi kawai tana gama magana ya fad'i zaune rugub ya sa hannu a kirjinsa yace " wow! Kaiiii!!! I really like ur boldness, Baby na."
  Harararsa takara yi sannan taj hanyar waje.



Habib nezaune a falon ummy, ta kalleshi tace " Habib kad'au yarinyar nan kubar gidan nan tun kafin Abbans Zara ya kara fitowa,  dan banaji abin zaizo da sauki, kallanta yai yace " dab Zaid yace yanasanta ko me?"

  Ido ta runtse tace " kaidai kai abinda nacemaka please Habin banasan abinda aka birneshi da kyar a kara hakoshi."

  Kallan mamakin kalamanta yake sai dai ya daure ya mike yace shikenan bari mu wuce.



Zaid bin Seemah yai a tsaye a jikin mota ya ganta, karasawa yai  tareda mika mata wayarsa yace ur number is needed here!

  Juyawa tai tace" bazan iya bada wa ba."

  Zaid yace "Kefa kanwatace, d'an haka dole ne ki samin number dana bukata."

  Murmushin mugunta ta saki sannan ta amshi wayar tasa number tai dialing ringing 2 ta katse tace gashi nasa in naje gida zan gani dan ban fito da wayata ba."

  Murmushi ya saki yace " Amma Ammar yaci amana ta dabai tab'a nunan hotonki ba."

  Kallansa tai tace " ko kuma mutuncin dake tsakaninku bai kai ya kawoba ba, tunda dai ko abokanansa sunsan hotonane akan screen d'insa."

   Matsowa yai kusa da ita yace " Wow I really like ur Style dear. "

  Mota tai saurin bud'ewa ta shiga tare da kulle kofar, Murmushi zaid ya saki sannan ya juya.

  Habib ne ya fito fuskarsa d'auke da tambayoyi kala kala waya ya d'aga ya kira Dad tare da cewa " Dad munzo gidan Abba amma......"

  Jiyai Dad ya katseshi yace " Habib meyasa kukaje? Meyasa baka tambayeni ba? Ina Seemah ba abinda ya faru da itadai ko?"

   Habib da mamaki yace " Dad menene kake kokarin boyemin? Yaza'ai kace meyasa mukazo gun Abba?"


Dad kam duk ya rud'e yace " Habib, Seemah fa? Is she alright? "

   Habib yace eh tare da kashe wayar, meke faruwa?









© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

   *Bang��*
  
       *Bang��*

��‍♀

No comments:

Post a Comment