๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ *Jร
ฤนรฤนรฤฤฤร*๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Na *AYUSHER MOHD*
NO8โฃ
Likita yazo ya dubata, wahalace kawai da yunwa suka had'un mata nan ya bata magani ya tafi, Habib ya kalli wayarsa dake ka ra yai shiru ya rasa mai zaice d'an tun rana Dad ke k'iransa akan yaji Seemah shiru, yanason lale abashi 'yarsa suyi magana.
Kallanta yai sannan ya kalli wayar, jiyai ance " Dad ne ko?" Habib ya kalli Seemah yace " eh" hannu ta mik'amai ya bata wayar daga kwance ta d'aga wayar tare da cewa " Dad d'ina."
Dad yace " Princess ina kika shiga? Bayan tun rama nake nemanki, sannan ya naji muryarki haka?"
Da sauri tace " Dad bacci fa nakeyi yaya ya tasheni."
" Ayya kiyi hak'uri ban sani ba, tunda naji muryarki yanzu mayi waya da safe."
Dad ya fad'a cike da namaki ganin seemah ba baccin wuri takeyi ba.
Seemah tace "to Dad nyt, love u." Tana kai nan ta kashe wayar tare da sakin ajiyar zuciya.
Habib ya kalleta yace " Bari a kawo miki abinci." Kafin ya mik'e Farida ta shigo d'auke ta tire ta ajiye kusa da Seemah tace " Seemah tashi kid'an ci wani abun."
Habib ya taimaka mata ta zauna, Farida ta zuba mata nan tafara ci, tad'anci dayawa kafin tace ta koshi, Farida ta zuba mata juice ta sha sannan tajingina.
Habib ya kalleta yace " Seemah meta faru wai?ance da wani kuka tafi, waye shi?"
Tai ajiyar zuciya tace
" Yaya irin wannan tambaya?"
Habib ya had'e rai sosai yace " ki fad'amin wanene in ba haka ba indai nai bincike da kaina, banajin zan barshi haka."
Shiru tai can tace " nima ban sanshi ba yaya, kawai dai da Aisha takusan kad'ashi ne na fita bashi hakuri sai yake cemin kamar jiya ya ganni a Company d'in dayake aiki, nikuma ganin a Company d'inka yake aiki yasa nace ya karasa dani shine yai wani gurin dani."
Habin ya mik'e cikin b'acin rai yace " ki kwanta ki huta gobe karfe 10 zansa a d'aukoki ki duba kaf ma'aikatan Company d'in ki nuna min shi."
Gaban Seemah ya fad'i a hankali tace to yaya.
Nan ya juya ya fita ta bishi da kallo, itakam menene nata na kare Jal? Meyasa batasan asan shine?
Mik'ewa tai ta shiga toilet tai alwalata dawo ta tada Sallah, bayan ta idar ne ta mik'e ta hau gado, Aisha ce ta kalleta tace Sannu Seemah, sannan d'azu Special Bros ya k'iraki, da sauri ta d'au waya ganin missed call 40 ta duba duk yayinta 3 sun nemeta da kuma dad sai dai na yaya habib yafi yawa tunda shi kad'ai yasan meke faruwa, layin Ammar ta d'anna, ringing 2 yad'aga ta saki murmushi tare da cewa" Oppa ya? Da alama yau kayi missing d'in kanwarka dayawa."
Murmushi yai yace " Seemah kinsan dai bana jure rashinki ko? Sanda na tafi South Korea wani Conference sau nawa muke waya dake?"
Dariya tai tace " Kai yaya wayar fa damukeyi yawanci ni nafi nemanka."
"Seemah ni dai banasan haka daga yau na k'ayade mana waya sau 8 a rana, ni zan k'ira sau biyar ke ki k'ira sau 3 duk wanda yai missing k'ira ko d'auka zai biya kud'i."
Dariya sosai tayi tace " shikenan yaya deal?" Yace deal.
Sun dad'e suna waya Aisha dake kwance tanata mamaki wannan dabad'an yayanta bane lalai sai ta ce su masoyane.
ใใใใใใใใใใใใ
Seemah ta kwanta bacci tad'ade kafin tai baccin sam ta rasa meke damunta, sai dai 1 thing is cleared sai tai ta hango Jalal sanda yana tsaye a waje ita kuma tana mota, bargo taja ta rufe kanta gaba d'aya sai dai duk da haka ta sake ganinshi yaye bargon tai sannan ta d'an sa ihu kad'an tace " Frustration! !!!!! Yau kuma meke damuna? Can tace nama gane, tsabar tsanar dana mai ne."
Tadad'e bata bacci ba sai can ya sace ta.
โขโขโขโขโขโขโขโขโข
9 ta tashi tai wanka tasa kayanta, yau doguwa ce rigar sai dai ta kanti ce mai bin jiki ta d'auko har zata fito sai kuma ta koma ta cire ta kara duba akwatinta, riga da wando ta d'auko na pakistan da yaya junaid ya siyo mata dayaje india tasa tare da yafa mayafin, tayi kyau sosai.
Ta sauko kasa ta taradda Aunty Farida kad'ai nan tai breakfast ko tambayar Aisha batai ba, kafin ta gama har driver yazo, Nan sukai sallama da Farida ta fita.
Suna isa company d'in ta sauko a hankali, Habib tagani a tsaye mamaki ya kamata a hankali ta karasa, sai dai abinda yabata mamaki tun daga cikin bakin kofar company d'in mutane suka jeru, ajiyar zuciya gai takarasa gun habib, yace " muje ki duba ga kananan ma'aikata anan manyan kuma na inda muke meeting." kallan yaya tai a hankali tace to.
Sun fara dubawa tana tafe yana binta a baya, sai kallan mutane takeyi, kowa tagani tace bashi bane, sai da suka zo kusan karshe, idanunsu ya had'u da Jalal, kallan juna sukai ta kuramai ido mamakinta babu alamar tsoro a idanunsa, jitai Habib yace " Shine?" Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, mamakine ya kama Jalal da sagir, me take nufi? Jitai Jalal yace ki kara dubawa dai.
Yawo ta had'iya sannan ta kalleshi ta wuce na gaba dashi, har taje karshe tace ba kowa, nan sukai hanyar inda manya suke, ba shakka sunji haushin wannan rainin hankalin, wai an tarasu saboda wata 'yar yarinya, Seemah ta duba nan ma tace ba kowa, Habib yai shiru can ya kalli Sagir yace kaita office ni zamuyi meeting.
Suna fitowa suka had'u da Jalal, ya matso kusa dasu kad'an yace " Follow me. "
Tad'an harareshi tace dalili? Yace " karki b'atan rai ki biyoni ko?"
Nan ta kalli sagir tace ina zuwa.
Elevator ya bud'e ya shiga itama ta shiga, sun yi shiru har suka isa last foor suna zuwa ya karasa sama itama ta bishi, saman ba komai a gun sai flowers da kujeru, suna shiga gun Jalal ya kalleta da karfi yace " What are you doing? "
Seemah ta kalleshi da mamaki tace " haka zaka cemin?"
Jalal ya matso daf da ita tad'anyi baya ya bita sai da sukaje jikin bango yasa hannu d'aya a jikin bangon, tsoro ya fara kamata, Jalal cikin b'acin rai yace " Do you find me pitiful? Don't tell me kinaso in miki godiya akan abinda kike tunanin kinmin."
Cike da mamaki da takaici tasa hannu ta ture hannunshi zuciya tazo mata wuya, ta d'unkule hannunta ta kaima duka a kirji cikin takaici da hawaye tace " haka kake? Me yasa bazaka duba alkairin mutum ba? Sai ka d'inga kok'arin juya alkairi zuwa sharri."
Ta had'iye wani abun sannan ta cigaba, "you don't want me to pity you? Ko kuwa kana tunanin kafi karfin hakan?" Tai shiru tarasa me zatace juyawa tai kawai tai ta wuce.
Jalal ya bita da kallo yarasa me yasa yakejin zuciyarshi ba dad'i, zama yai a gun tare da dafe kai.....
Seemah kam da gudu ta karasa elevator tana shiga ta tsugunna a ciki tasa kuka mai ban tausayi, can wata zuciyar tace me kikema kuka? Mik'ewa tai da sauri ganin har sun zo, office d'in Habib ta wuce, Sagir ganin fuskarta yasan Jalal ya b'ata mata rai.
Seemah na shiga ta rufe kofar tare da jingina da kofar idanta na zubar da hawaye............
Na *Ayusher Mohd*
ยฉ *NWA*
No comments:
Post a Comment